Sunday, December 4, 2011

Me ya sa matasan Arewa ke gudun kana nan sana’o’i?


Rashin aikin yi a tsakanin matasa na daga cikin matsalar da take addabar kasashen duniya a yanzu. da yawan kasashen suna ta neman hanyoyi da za a kawo karshe ko kuma rage adadin marasa aikin yi, rashin aikin yi babbar barazana ce ga zama lafiyar kowace kasa, haka kuma barazanace ga tsaron lafiya da dukiya. Kusan kididdiga ta nuna mafiya yawan wadan da ke cikin wannan mummunan yanayi na rashin aikin yi matasane wadan shekarunsu suka kama daga 18 zuwa 30 a mafiya yawan kasashen duniya.

Najeriya kasace da Allah ya huwace mata al’barkatun jama’a wadan da galibinsu matasane maza da mata. Kusan kididdiga ta baya-bayan nan ta nuna cewa akwai kusan mutane miliyan 167 a Najeriya wanda wannan adadi ke karuwa cikin sauri a cewar masana, acikin wannan lissafi kusan sama da kashi 65% matasane ‘yan bana bakwai masu jinni ajika. Kuma mafiya yawan al’ummar Najeriya suna yankin Arewa ne.

Babbar matsalar Najeriya yanzu bata wuce rashin aikin yi tsakanin matasa ba kamar sauran takwararorinta kasashen duniya. Dalilan da suka samar da rashin aikin yi tsakanin matasa a Najeriya abayyane suke. Rashin ingantacciyar wutar lantarki kusan itace babbar matsalar da ta haifar da rashin masana’antu wanda hakan ya haifar da rashin aikin yi, domin da wutar lantarki ne galibin kamfanoni ke aiki wanda suke taka muhimmiyar rawa wajen rage adadin marasa aikin yi akusan galibin kasashen duniya. Yau a Najeriyya babu masana’antu a yankin Arewa da zasu iya rage adadin matasanmu kama daga wadan da suka kamala jami’a da kuma wadan da suka fito daga kwalejoji dama wadan da basu sami damar zuwa makaranta ba.

Kididdiga ta nuna cewa gwamnatin PDP karkashin shugabancin tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo ta kashe kudi sama da dalar amurka Biliyan 16 kimamin Naira tiriliyan 1.3 akan wutar lantarki acikin shekaru 8, amma babu ita babu dalilinta kuma kudin shiru kamar an shuka dusa. Abin tambaya anan shi ne shin ina wutar ta ke? Kuma idan ba’ayi aikin ba kamar yadda muka gani ina kudin suke? Akwanakin baya ‘yan majalisa sunyi dambarwa akan wannan batu amma yanzu shiru kake ji,abun da yake nuna anci bulus kenan.

Idan muka dauki misali da kasar Brazil ta kashe kudi kimanin dalar Amurka biliyan 5 wajen samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 120,000 acikin shekara 3 kacal, haka itama kasar Afurka ta kudu sun kashe kudi kimanin dalar amurka biliyan 1 wajen samar da megawatt 5,000 acikin shekara daya kacal. Idan ka dawo nan gida Najeriya zaka ga cewa kudin da aka fitar ya ninka na Afurka ta kudu ninkim baninkim amma megawatt nawa aka samar mana? Lokacin da marigayi tsohon shugaban kasa Mallam Umaru YarAdua yazo ya kudiri aniyar ganin bayan matsalar wutar lantarki a Najeriya wanda ya durfafi aikin fafur wajen ganin ya cimma kudurinsa na samar da megawatt 10,000, Allah bai cika masa burinsa ba ya kwanta dama. Wannan shugaban da ya gajeshi cewa yay i zai dora daga inda ‘yar Adua ya tsaya inda ya nada kansa munistan makamashi da wutar lantarki amma babu wasu alamu da suke nuna da gaske ake akan wannan batu.

Idan kuma muka komo yankin Arewa a yanzu haka wutar lantarki da muke samu daga babban kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa bai wuce megawatt 3,000 ba gaba daya yankin Arewa mai jihohi 19, wanda wannan kaso kusan shi ake baiwa jihar Legas ita kadai. Abin tambaya me gwamnatocinmu da ‘yan majalisun mu suke? Ina sarakuna da ‘yan boko ina tsofaffin sojojinmu ina sababbinsu ke ina kungiyar dattawan Arewa? Ina duk masu fada aji da muke dasu me sukayi akan cewa yankin Arewa ya samu wutar lantarki tabbatacciya.

Idan kuma muka koma batun aikin yi tunda yake Manya manyan masana’antun da muke dasu a kano da kaduna sun kwanta dama sakamakon sakacin magabatanmu akan wutar lantaarki me ya rage mana? Abin da muka gada iyaye da kakanni wato sana’o’in hannau, amma duk munyi watsi da su. Ina noma da kiwo duk mun watsar dasu sai tsurarun talakawa marasa galihu suke wannan yanzu.

Yankin Arewa mu muka fi kowane yanki albarkar jama’a a Najeriya amma mune muke da adadi mafi yawa na marasa aikin yi; wani abu da na gani ya bani mamaki shi ne inda naga Inyamuri na sana’ar pawa wato ya sayi saniya ya kai abbatuwa a yanka a rabawa Hausawa naman sukuma su sayar idan yamma tayi su hada masa kudinsa, kaga wannan shine cikakken koma baya awajen mutanan Arewa me ya hada inyamuri da sana’ar pawa? Kuma kaje kasuwar Hatsi ta Dawanau dake kano kasha mamaki inda zaka ga inyamurai na cin karensu da babbaka, inyamuri zai sayi wake da masara da gyero ya kai sito ya ajiye idan yayi tsada ya fito dashi ya sayar.

Mafi yawan matasa yanzu a Arewa basa son yin sana’ar hannu. Kowa ya nade hannun riga yana jiran ya samu na banza babu sididi babu sadada. Muna da dimbin matasa da suka kamala jami’a basu da aikin yi, amma kuma su baza suyi sana’a ba indai ta hannu ce kowa ya dogara da cewa sai aiki mai maiko ko kuma aikin da zakayi kudi nan da nan, don haka kullum sana’o’inmu kara komawa baya suke yi. Mafi yawan sana’o’inmu basu da bukatar kama hayar shago ko kanti basu da bukatar kudi da yawa amma zaka samu tashoshi na matasa agefen tituna acikin biranenmu na Arewa suna zaman banza.

Zance na gaskiya iyaye sun taimaka wajen kara yawan masu zaman banza a Arewa. Domin kuwa zaka ga yaro baya samun wani kwarin gwiwar cewa yay i sana’a tun yana karami, haka kuma anshagwaba yara talaka da mai kudi kowa ya shagwaba dansa kaga saurayi dan shekara 18 zuwa 20 harma 25 ana bashi kudin kashewa mu duk agurinmu yaro ne; wanda inda aka cigaba duk dan shekara 15 ya tashi daga sahun yaro ya koma saurayi. Misali a kasar Jamus duk dan shekara 18 dole ya fita daga gidan iyayansa ya nemi na kansa don fuskantar rayuwarsa. Idan banyi karya ba zaka iske matashi dan shekara 30 a Arewa yana zaune agida baya aikin fari bayan a baki kuma ana ciyar dashi da tufatar dashi kai harma da bashi kudin kashewa amma babu wani kwarin gwiwa da ake bashi nacewa yaje ya koyi sana’a.

Ka shiga ka suwanninmu kaga yanda matasanmu suka zama ‘yan kamasho. Mutum zai wanke riga ya fita kasuwa banda haram babu abin da ya tafi nema da sunan wai ya tafi kasuwa amma bashida rumfa ko kanti bashida jari kona kwabo, kawai yana ci ajikin talakawa ‘yan uwansa da daurin gindin wasu daga cikin ‘yan kasuwa. Bayan idan za’ayi Magana ta gaskiya shi kansa kasuwancin da muke takama da shi anyi rugu-rugu da shi ‘yan kasuwa nawa ka sani wadan da suka karye kodai sakamakon bashi ko fashi ko damfara ko zurmiya ko sanbanza da zulama? Suna da yawan gaske basa samun wani tallafi na kirki daga al’umma ko daga gwamnatoci. Yanzu kusan duk kasuwanninmu Sinawa da indiyawa sun mayesu idanma kaga muna kasuwanci to ba namu bane su mukemawa. Me ya janyo mana fadawa wannan hali?

Haka kuma gwamnatocinmu basuyi mana wani tsari na koyar tare da fadawa yara muhimmancin sana’a ba a makarantu tundaga sakandare har zuwa jami’a. ya kamata ace acikin jadawalin karatunmu akwai koyar da sana’o’I yaro tun yana makaranta akoya masa wani abu da zai iya yi ana gaba, haka suma jami’o’I ya kamata ace akwai wani tsari na karfafawa dalibai gwiwa idan sun kammala jami’a su dogara da kansu ba lallai sai mutum ya yi aikin gwamnati kona kamfanonin sadarwa ko wani muhimmin aiki zai zama wani ba.

Na karanta a wani shafi na Makarantar kimiyya da fasa wanda Abubakar salihu baban sadiq yake kula dashi. Inda ya kawo wata kasida da marigayi steve jobs wanda shi ne shugaban kamfanin Apple inc Kafin rasuwarsa dai ana kirga shi daga cikin mutanen da suka yi tasiri mafi girma a duniya wajen habbaka harkar sadarwa da kere-kere, musamman kan wayar salula, da kwamfuta, da na’urorin sadarwa nau’uka daban-daban, da allon shigar da bayanai na kwamfuta (Keyboard), da lasifika da dai sauransu. A yadda shi wannan mutum ya bada tarihinsa ya ce shi bai samu damar yi ko kammala jami’a ba, ya maida kai waje sana’ar hannu ne a karshe ga yadda Allah ya mai dashi. Na kawo wannan ne a matsayin misali kawai.

Ya kamata yanzu duk da wasu gwamnatoci suna kokarin koyawa matasa sana’o’i tare da basu jari, ya kamata wannan shiri ya shiga cikin jadawalin koyar da karatu tundaga matakin sakandare har jami’a kamar yadda yake a shekarun baya.

Yanzu idan ka dauki harkar kiwon kaji da kiwon kifi kawai wata babbar sana’ace da zata rike mutane da yawa, misali ka kalli yawan jama’ar kano da kaduna da sokoto zaka iya kididdigar kwai nawa ake ci a wadan nan garuruwa ko kuwa kifi nawa ake ci? Amma wani abin ban Haushi da takaici shi ne kaso sama da 50% na kwan da muke ci bama iya samar da shi a Arewa sai anshigo mana da shi daga kudu duk da albarkar da Allah ya bamu ta ruwa da kasa mai yabanya.

Mu kanmu yanzu a Arewa sai kaga cewa kamar wani mulkin mallaka ake yi mana domin irin gonakan da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya sa aka sayarwa da manoma ‘yan kenya da zambabwe a jihohin Taraba da Kwara ake amfani da matasanmu su noma kuma akwashe a fita dasu daga baya a sarrafa wani abu a kawo mana a farashi mai dan karen tsada bayan mu muka sha wahalar. Allah ya kyauta.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment