Saturday, December 31, 2011

Mallam Ahamadu Maigandu shi ne Gwarzona na shekarar 2011!

Assalamu Alaikum warah matullahi ta'ala wa barakatuhu.

Ya 'yan uwa ina gaisheku gai suwa irin ta addinin musulunci. kuma ina fatan alheri gareku baki daya. sanin kowannenmu ne cewa shekarar Musulunci tuni ta riga ta gabata, sannan kuma yau ne muke ban kwanan da wannan shekara ta miladiyya ta 2011. Kamar yadda muka sani gab da karewar wannan shekara wani muhimmin al'amari ya faru wanda dukkan 'yan uwa suka yi farin ciki da murna da faruwarsa, wato hadin kai da aka samu tsakanin bangarorin izala guda biyu Jos/kaduna.

Shakka babu wannan al'amari muhimmin abu ne. wannan hadin kai dai ya faru ne sakamakon rasuwar dan uwa kuma daya daga cikin jigo na kungiyar Izala reshen jihar kaduna. Jama'a da dama sun nuna alhinin wannan bawan Allah irin yadda aka ringa fadar kyawawan kalamai a gare shi ya nuna irin yadda ya zauna da jama'a lafiya. jama'a daga sassa da dama sunta tudada zuwa jiharsa ta Bauchi domin yin ta'aziya ga iyalansa da 'yan uwansa da abokan arziki. Da kuma nuna alhinin rashinsa.

Lokacin da Sheikh Sani Yahaya Jingir shugaban bangere na Jos ya nemi wannan hadin kai lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyar Maigandu. shakka babu akwai jama'a da dama da suka kai ruwa rana domin samar da wannan hadin kai amma Allah bai sa hakarsu ta cimma ruwa ba, ina jin jina ga babban malaminmu sheikh Dr. Ahmad Gumi ganin irin shi ma yadda ya yi ta kokari a baya wajen ganin wannan hadin kai ya samu. Allah baisa wannan muhimmin al'amari zai samu ta bangarensa ba.

Shakka babu, wannan rasuwa ta wannan bawan Allah ba karamin alkhairi ta haifarwa dimbin musulmi ba. kowa dai yasan da cewa dole hankali ya tashi zuciya ta raurawa idanu su zubar da kwalla a ya yin da akayi rashi musamman na mutumin da yake hidima wa jama'a. Amma Allah cikin ikonsa ya sanya rasuwar wannan bawan Allah itace silar bude wani sabon babi na hadin kan al'ummar Musulmi a wannan kasa tamu. Tabbas iyalan Malam Maigandu da makusantansa sunji takaicin rabuwa da shi a lokacin da Allah ya rubuta rayuwarsa zata koma zuwa gareshii. kamar yadda Allah ya fada a cikin alkur'ani kowane mai RAI zai dandani mutuwa, mai gandu dai ya riga ya dandani tasa kamar yadda kowannemu zai dandana kamar yadda Allah ya yi alkawari. Amma kuma ta gefe guda kuma masu hankali sai suyi murna ganin cewa ta sanadiyarsa ne Allah ya samar da wannan babban muhimmin al'amari na hadin kan Musulmi Ahlussunnah a wannan kasa tamu.

Muna fatar wannan hadin kai da akasamu ya dore har iya tsawon rayuwarmu. kuma kamar yadda aka cimma matsaya kan Alkur'ani da sunnah shakka babu wannan shi ne zai hada kan al'ummar Musulmi baki daya, Allah ya cigaba da hada kanmu wajen yi masa da'a da biyayya da hani ga mummuna da kuma umarni da kyakkyawa.

Daga karshe ina addu'ar Allah ya jikan Mallam Ahamadu Maigandu ya gafarta masa yasa al'janna ce makomarsa. kuma 'yan uwansa da iyalansa Allah ya basu ladan hakuri ya cika a mizaninsu. kuma shima babban malaminmu kuma sabon shugaban wannan hadaddiyar kungiya Sheikh Sani Yahaya Jingir Allah ya saka masa da alheri kuma Allah ya yi masa jagoranci bisa wannan Nauyi da aka dora masa. Allah ya sadamu da alherinsa baki daya.

Mallam Maigandu wallahi kaine gwanina na wannan shekarar, Allah ya albarkaci zurriyarka ya kyautata bayanka.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@yahoo.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com


No comments:

Post a Comment