Thursday, October 15, 2015

Malaman Sunnah Sun Ki Jin Magana ta . . .


MALAMAN SUNNAH SUN KI JIN MAGANA TA . . .

Na karanta bayanin wani dan yaga riga a facebook, yana kalubalantar Malaman Sunnah, akan, dan me, ya jima yana kiransu da su shiga harkokin siyasa, amma sunki, a cewar sa,  ya sha gaya musu, ba sau daya ba, kuma ba sau biyu ba, amma sunki jin kiran sa.  Ya kuma kalubalance su a akan dan me basu taimakawa Shugaban kasa ba a lokacin da yake yakin neman zabe. 

A cewar sa,  ya auna ya gano, sam Malaman basu fadakar da mabiyansu ba a akan su zabi Buhari, yace yayi ta kira amma Malaman sukai shakulatun bangaro da batun sa. Ya cigaba da cewar yana da masaniyar cewa fa 'yan Siyasa suna baiwa Malaman kudi da motoci, kuma yace da idonsa ya hango wasu a Umra, Goodluck Jonathan Mai Nasara,  ya kai su dan suyi wa Najeriya addu'ah. 

A cikin soki burutsun nasa, yace, ku Malamai ku sani fa, dan kafi mutum ilimin addini ba shine yake nuna ka fishi kwakwalwa ba. Sannan ya yabawa Adamu Adamu a kokarin sa na ganin kasar sa ta fita daga halin cin hanci da karbar rashawa da samun mafita a harkar tattalin arziki, ya yabawa Adamu Adamu akan wannan kokari nasa, a daidai lokacin da ya kwarewa Malamansa da yake jingina kansa garesu cewar basu ji irin kiraye kirayen da ya dinga yi musu na su ja hankalin mabiyansu su zabi Buhari ba.

Wannan dan hauragiya yayi ta rambatsu yana aibata Malaman Sunnah da yake jingina kansa garesu, duk kuwa da ta bayyana a fili wasu daga cikinsu da yake muzantawa sun tsunduma kansu cikin siyasa tsundum kuma jam'iyyar da yake wa fatan taci zabe, kuma taci din. Wannan dan harbatamati yayi ta soki burutsu da hayaniya da nuna rashin kunya ga Malaman Sunnah. Kalaman sa na rashin ladabi, ba boyayyu bane musamman ga Babban Malamin Tafsiri na Kaduna Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da aibata shi da nuna cewa shi yafi Malamin Sanin addini da sanin Sunnah.

Irin wadannan yan jagaliya basa bukatar Nasiha ko Jan hankali,  a biyo masa ta inda ya shigo zai Fi gane wannan yaren. 

Wannan somin tabi ne.

Yasir Ramadan Gwale 
15-10-201

1 comment:

  1. AkramakalLah, tsakani da Allah kayi zafi da yawa, musamman ganin cewa gyara ya nufa duk da ya yi rashun ladabi a maganganunsa wanda na karanta. Sannan wani abu kuma ni kaina ina da raayin rashin kokarin mu na tabukawa sosai a siyasa duk da akwai bukatar taka tsantsan kada a zubar da mutuncin addini musamman a al'umma irin tamu.

    ReplyDelete