Wednesday, October 21, 2015

Dr. Goodluck Jonathan: Sabon Malamin Siyasar Kasar Tanzania


Dr. GOODLUCK JONATHAN: SABON MALAMIN SIYASAR KASAR TANZANIA 

Wani hanin ga Allah baiwa ne,  inji 'yan magana. Idan ya karbe ta can sai ya baka ta nan. Yanzu dai ance Mista  Goodluck Jonathan shi ne zai jagoranci wata kakkarfar tawagar kwararru domin sanya ido akan yadda za'a gudanar da zaben Shugaban kasa a Tanzania. Tuni rahotanni suka nuna irin kyakkyawar tarba da maraba lale da akaiwa Mista Jonathan a Arusha, ba da jimawa ba kuma aka ce Jonathan ya shiga aiki ka ' in da na ' in wajen yin kira ga 'yan siyasa da masu takara a Tanzania da su sanya kishin kasarsu akan ra'ayinsu. 

Ba shakka har yanzu ina samun nutsuwa da gamsuwa cewar tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ba yadda da yawa suka dauke shi haka yake ba. Ina ganin mutum ne mai saukin kai da saukin Mu'amala. Ya iya jure yadda da kaddara mai matukar wahala a sahun mutane irinsa. Yayi abinda Shugabanni da yawa a Afrika har da Nigeria basu yi ba, dan haka ne, duniya ta jinjina masa, kuma, aka yaba masa, bisa wannan namijin kokari da yayi na karbar kaddarar faduwa zabe. Har hakan ta kaishi ga samun wannan mukami. Haka zalika, har yanzu sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai dena yabawa wannan namijin kokari na Mista Jonathan ba.

Goodluck Jonathan ya nuna misali a Afrika wajen nuna kishin kasarsa da nuna cewar maslahar 'yan Nigeria tafi maslaharsa. Ko da kuwa za a gwale shi ace yaga babu sarki sai Allah shi yasa ya karbi kaddara, hakika yayi abin da ya saya masa mutuncin da kudi ba zasu iya Saye ba. Muna fatan Kullum 'yan Najeriya su kasance abin misali a Afrika wajen nuna kyawawan halaye da mutunta ra'ayin mafiya rinjaye. Ina fatan Allah ya masa jagoranci a wannan aiki yasa 'yan takara a Tanzania suyi koyi da shi (Goodluck Jonathan) wajen karbar dukkan sakamakon da yazo na gaskiya daga hukuma. Allah ya taimaki Najeriya. 

Yasir Ramadan Gwale 
21-10-2015

No comments:

Post a Comment