Saturday, January 23, 2016

KANO: Gwamna Ganduje Yana Ta Gyada


KANO: GWAMNA GANDUJE YANA TA GYA'DA
Irin nad'e nad'en da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yake yi abin yayi yawa. A daidai lokacin da tattalin arzikin Kasa ya shiga wani irin mawuyacin halin ha'ula'i, arzikin man da k'asarnan ta Dogara gare shi kullum komawa baya yake yi. Farashin manfetur ya karye ya zube kasa warwas, kasuwanci ya durkushe, harkokin masanata'antu kullum suna komawa baya a guje. Kuma alumma na kara yawaita. Amma Gwamna ba ruwansa, sai bayar da muk'amai yake yi barkatai kamar kayan gadon gidansu, kullum ana karawa Laftawa Gwamnati hanyoyin zurarewar kud'i ba gaira babu dalili.
Ya kamata Gwamna ya maida hankali wajen ayyukan da ya gada wajen gwamnatocin da suka shud'e wajen yaga ya kammala su, ba kara dorawa Gwamnati nauyi ba. A makotanmu, Kaduna, Gwamna Nassir el-Rufai har ya zuwa yanzu nad'e nad'en SA da yayi basu kai goma ba. Amma mu Kano sabida watakila kirarinmu na cewa ko da me kazo mun fika, sai barna da ta'adi Gwamna yake yi da dukiyar al'ummah da sunan mukamin SA. Ya kamata Gwamna ya san ina gabas take, ya tsaya ya fuskanci kalubalen da yake kansa na tattalin arziki dan ciyar da Kano gaba, ba irin wannan nad'e nad'e marasa kan gado ba.
Ina amfanin Gwamnati ta tursasa mutane biyan haraji, daga karshe kuma ta rabawa SA's a matsayin Albashi da Alawus? Bama yiwa duk wanda Gwamnati ta baiwa muk'ami Hassada kan abinda aka bashi, hasalima muna fatan ayi mulki lafiya. Amma ba daidai bane, lokacin da ya bayyana karara cewar Gwamnatin kasarnan na fama da matsalar kud'i, amma Gwamna ba ruwansa, sai kirkiro hanyoyin kashe kudi yake da ba zasu amfanawa al'umma komai ba, domin da wadannan mukamai da babu su za ai Gwamnati ba tare da wata matsala ba, kamar yadda muke gani a Kaduna.
A dan haka, ya kamata Gwamna ya samu nutsuwa ya maida hankali wajen ganin yabi sahihan hanyoyin da zai ciyar da Kano gaba, ba rabon mukamai barkatai ba. Abin kunyar ma da yawan wadan da ake nadawa ko sunan mukamin da aka basu basa iya rubutawa daidai. Ace Gwamna ya dinga diban tantagaryar jahilai ana basu mukamai ba gaira ba dalili. Wannan wace irin Gwamnati ce haka? Ya kamata Gwamna ya sani yanzu karni na Ashirin da d'aya muke, aikin mutum goma mutum daya tak zai iya yi kuma a samu Nasara. Wannan lokaci ne da duniya ke samun koma baya ta fuskar tattalin arziki. Kullum Gwamnatocin da suka san me suke suna tsuke bakin aljihun Gwamnati ne ba wargaje shi ga mutane haka kurum ba.
Yasir Ramadan Gwale 
22-01-2016

No comments:

Post a Comment