YAKIN YEMEN: ABINDA SA'UDIYYA TA KE YI . . .
A ranar 26 ga
watan Maris na wannan Shekarar ne kasar Musulunci ta Sa'udiyya ta bayar
da sanarwar kammala dukkan wasu shirye shirye domin fara kai hare hare
ta sama ga yankunan da 'yan tawayen Yaman masu samun cikakkiyar
gudunmawa daga Iran suka mamaye.
Ba tare da wata wata ba
kasashen yankin Gulf gaba dayansu suka nuna cikakken goyon bayan su ga
wannan Yaki; Haka suma kasashen da ba na Gulf ba da suka hada da Jordan
da Egypt da Sudan suka nuna cikakken
goyon bayan su ga wannan Yaki, da ake ganin shi ne aikin sabon Sarki
Salman Bin Abdulaziz Allah ya kara masa lafiya na farko da ya shiga.
Da yawan mutane na da masaniyar abinda ke faruwa a Yemen, dan haka
zamu maida hankali ne akan wannan Yaki kacokam da kuma dalilin
faruwarsa. Wato abinda yake faruwa a Gabas ta tsakiya shi ne, yunkurin
da shedaniyar kasar Iran take yi na mamayar yankin gaba dayansa, tare
da yi masa daurin butar Malam.
Har kullum, abinda kasar Iran take kwana kuma take tashi da shi shine batun yadda zata rusa Ka'aba a Makkah, su shiga Madina su sace gawar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, su maida ita biranensu da suke kira da masu tsarki, sannan su tone k'aburburan Sayyaduna Abubakar da Umar sannan su je Baqee'a su tone kabarin Nana Aisha su yi musu wulakanci. A Takaice wannan shi ne Babban hadafin shedaniyar kasar Iran.
Kada ka taba yin mamaki da jin wannan zance, wannan ita ce hakikanin manufar kasar Iran, burinsu a rushe Musulunci, ya zama a duniya daga kafurci sai Shianci, wanda kashin bayan su shi ne aikata fasadi da Alfasha a ban kasa. A sabida haka ne, suka hada baki ta fuska biyu, na farko shi ne da kasashen gurguzu da ba ruwansu da Allah ba ruwansu da addini irinsu China da Russia sannan a gefe guda kuma suna da boyayyar alaka mai karfi da Amurka da kasashen Turai na Yamma.
Tun bayan kammala Berlin Conference manyan kasashen duniya suka kasa duniya gida gida suka fahimci babu wani abu ko yanki da yake zamar musu barazana kamar yaduwar addinin Musulunci a kasashen Sunni, musamman a Gabas ta tsakiya da Arewacin Afurka, wanda a definition din su, idan sun ce kasashen sunni suna nufin kasashen da ba na Shiah ba, ko da kuwa 'yan Bid'ah ne.
Zan cigaba In sha Allah.
Yasir Ramadan Gwale
31-05-2015

No comments:
Post a Comment