IMAM MUHAMMAD ASH-SHAFI'E
Imam Ash-shafi’e
asalin sunansa shi ne: Muhammad Bin Idris Bin Abbas Bin Usman Bin
Shafi’e; Abu Abdullah, Ash-shafi’e, Al-qurashi, Al-makki, nasabarsa tana
tukewa zuwa ga Lu’ayyu Bin Galib, wato kakannin Manzon Allah(Sallallahu
Alaihi Wa Sallam ).
An haifi Imam Ash-shafi’e a shekarata
(150A.H) a garin Makkah, mahaifinsa ya rasu tun yana yaro karami, don
haka ya taso ka...rkashin kulawar mahaifiyarsa ne. Imam Shaffi'e
ya fara neman ilimi tun yana yaro, ya fara da karatun harshen larabci
da kuma wake-waken larabawa har ya tumbatsa a cikin wannan fanni, sannan
ya fuskanci karatun fiqihu har ya zamanto jagora a zamaninsa.
Imam Ash-shafi’e ya karanta littafin Muwadda a wajen Imam Malik, ya kuma
yi wallafe-wallafe na littattafai da dama, daga cikin mafi shaharar
littattafansa akwai: Ar-Risala, da Al-Um, da Al-Musnad, da kuma
As-Sunan.
Imam Ash-shafi’e yana cewa: neman ilimi ya fi sallar
nifila, duk wanda ya koyi qur’ani matsayinsa zai daukaka, duk wanda ya
karanta hadisi hujjarsa zata yi karfi, duk wanda bai kame kansa ba daga
sabon Allah to iliminsa bai masa amfani ba. Imam Ash-shafi’e ya rasu a
shekarata (204A.H).
Yasir Ramadan Gwale
04-05-2015
Allah yakin sa da rahma
ReplyDelete