Wednesday, May 13, 2015

Shugabannin Afurka Basa Daukar Izna Aga Takwarorinsu


SHUGWBWNNIN AFURKA BASU DAUKA INA DAGA TAKWARORINSU 

Tsohon Shugaban Nijar Tandja Mahamdou yayi kokarin karya tsarin Mulki yayi wa'adi na uku, amma hakarsu bata cimma ruwa ba, duk kuwa da yadda ya dinga cika baki da alfahari da fariya. Amma sojojin suka kawo karshen wannan fata da cika baki nasa.

Haka ya faru a Kwadebuwa inda Laurent Gbagbo shima ya kasa samun darasi, yayi gaban kansa domin tabbatar da kansa a matsayin Shugaban da jama'a suka gaji da shi, karshe shima yaji kunya da babu wani shugaba da aka taba wulakantawa kamarsa. 

Irin haka ce ta sake faruwa a Burkina Fasso inda Blaise Campore shima yayi kokarin, yin kunne uwar shegu da bijirewa  tsarin mulki domin tabbatar da kansa a kan mulki, shima karshe aka kunya ta shi, sojojin suka kawo karshen wannan fata nasa.

Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo shima yayi kokarin karya kundin tsarin Mulki domin bin wannan sawu na shugabanni  masu kunne kashi, amma a karshe ya hadu da tirjiyar 'yan siyasa tun ba'aje ko ina ba.

Yanzu kuma sai ga Shugaban Burundi wanda abin takaici yana da tarihin kwantanta gaskiya da yin mulki na adalci, amma karshe ya bata rawara da tsalle ba tare da ya dauki wani darasi daga magabatan shugabanni Afurka ba.

Duk da irin wannan tirjiya da ake nunawa shugabanni a Africa amma har yanzu akwai masu fatan dawwamar da kansu akan karagar mulki. Shugabanni irinsu Umar Hassan Albashir (Sudan) da Paul Biya  (Cameroon) da Robert Mugabe  (Zimbabwe) da sauransu har yanzu basa ganin abinda ke faru balle su dauki darasi daga takwarorinsu. 

Me yasa Shugabanni a Afrika ke san dawwamar da kansu a mulki duk kuwa da suna Ikirarin Demokaradiyya? 

Yasir Ramadan Gwale 
13-05-2015 

No comments:

Post a Comment