Saturday, May 16, 2015

TUNATARWA: Tsakanin Masu Zana Hoton Manzon Allah SAW DA Masu Zaginsa



TUNATARWA: TSAKANIN MASU ZANA HOTON MANZON ALLAH SAW DA MASU ZAGINSA KARARA 

A facebook din nan naga ana yada hoton wani mutum Bature, ana tsine masa tare da la'antarsa da kwashe masa Albarka. Ance mutumin yayi alkawarin yin Zane Zane na hotunan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, abin mamaki da tashin hankali da takaici. Shi ne, Musulmi a cikin garin Kano, ya fito bainar Jama'a ya kama sunan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam karara yace WALLAHI SAI SUN TAKA AKE MUHAMMAD! Wal Iyazubillah. Allahumma ajirni fi musibati......! Amma kalli yadda akai gum akan wadannan mushrikai zindikai makiyan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam na hakika.

Ya jama ya kamata mu fadaka, mu sani cewa wadannan mutanafa abin nasu ya wuce duk yadda muke zato, munufarsu shine ruguje addini, domin addinin ba shine a gabansu ba, ba sa ganin girman Manzon Allah (SAW) kai Allah ma ba ganin girmansa suke yi ba, mu kuma musulmi bamu da wanda ya kai Manzon Allah, idan wasu kafirai sunyi zane ko sun fadi wata mummunar magana game da Manzon Allah hankalin duniya zai tashi ayi kone-kone a kasashe da dama saboda kare martabar Annabi (SAW) wadanda Allah dama ya gaya mana a cikin Kur'ani cewa zamu dinga jin irin wadannan maganganu daga wajensu, sai mu yi hakuri, to ya za a yi yau kuma a ce wai wasu wadanda ake cewa wai suna da alaka da muslinci su zasu dinga cin zarafin Manzon Allah a cikin garin kano kuma shuwagabanninmu na addini suna gani, kawai saidai a bar malamai da magana. Allah ya Ubangiji ka tsinewa duk wanda ya assasa wannan mauludin na Ibrahim inyas wadan aka ci zarafin Annabi (SAW) a cikinsa. 

Lallai muna kira da babbar murya ga Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin Babban Limamin Kandahar Sheikh Abubakar Rijiyar Lemo da babban kwamandan hisbah na Kano Mal.Aminu Ibrahim Daurawa da Gwamnatin Kano, akan lallai su yi bincike akan wadan da suka shirya wannan cin mutunci ga fiyayyan Halitta, a kamasu ayi musu hukunci dan hakan ya zama darasi ga duk wani dan iska dake shirin irin wannan magana anan gaba.

Sannan wannan mawakan da suke fkewa da yabon Shehu suna yin I zai lancing ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, lallai ne hukuma ta hana wannan. Yana daga cikin wajibin hukuma, karewa al'umma addini da mutunci da hankali da dukiyoyinsu. 

Kuma In sha Allah zamu mai da hankali a kan bayanin shugabannin bata na duniya wadanda suka dora wadannan mutane a kan wannan mummunar akida ta raina Allah da Manzonsa Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Yasir Ramadan Gwale 
16-05-2015

No comments:

Post a Comment