Sunday, May 24, 2015

Masu Bautar Inyass Kaulaha


MASU BAUTAR INYASS KAULAHA


Zaka ji mamaki yadda mutane da suke kiran kansu musulmi, amma suna Ikirarin shirka da bakin su, ta hanyar bayyana cewa su Inyass Kaulaha ne ya halicce su, kuma shi suke bautwa. Wato irin wadannan zaka tausaya musu ne, domin bayan kasancewarsu Mushrikai, sannan Tantagaryar Jahilai ne na buga misali. Yanzu tsakani da Allah, ta yaya mutum mai hankali zai ce yana Bautawa Inyass Kaulaha ko yace Inyass Kaulaha ne ya halicce shi, bayan kuwa Inyass Kaulaha bai iya hana kansa mutuwa ba! Dan Allah ina hankali anan?

Idan anbi ta barawo Abi ta mabiyin Barawon. Muna kyautata zaton da yawan wasu mutane musamman Matasa da Mata suna yin Tijaniya ne dan an nuna musu kaunar Manzon Allah a ciki, sun shiga da wannan manufar, kamar yadda Sheikh Google yake cewa babu komai a cikin Tijaniya sai Salati da Zikiri da Hailala sannan ba'a shan taba sigari. Da dama sukan dauka haka Tijaniyar take, kuma akan haka suka shiga, amma a zahirin gaskiya an boyewa wasu abubuwa da yawa. Sai mutum ya dahu tukuna ake bayyana masa hakikaninta. 

Duk mutum mai san gaskiya da tsoron Allah, da kuma ya san meye hakikanin Tijaniya, kuma yasa waye Inyass Kaulaha, to bai isa yace irin wadannan miyagun kalmomi na Shirka basa cikin littattafan Tijaniya ba. Abin haushi da takaici kaga wasu na Ikirarin Sunnah amma suna ta kokarin wanke Tijaniya daga wadannan maganganu na shirka dan suna son burgewa, ko kuma dan ita ake yi a gidansu ba zasu iya kalubalantarta ba. 

Da ace Hujja mutane suke nema suyi addini, da kowa yabi Sunnah, amma ina shiriya a hannun Allah take. Wanda duk Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi, wanda Allah ya shiryar shi ne hakikanin shiryayye. Namu shi ne isar da sakon abinda muka yi tsuwurwuri daga Malamanmu na daga maganganun magabata. 

In sha Allah daga gobe zamu fara gabatar da bayanai akan Tijaniya da Inyass Kaulaha, daga cikin littattafan Tijaniya. Ya Allah ka nuna mana gaskiya mu fahimceta kuma ka bamu ikon binta, ka nuna mana karya mu fahimceta kuma ka bamu ikon kauce mata. Allah ka tabbatar da dugaduganmu akan bin Sunnar ManzonKa Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Yasir Ramadan Gwale
24-05-2015

No comments:

Post a Comment