WAYE YA ASSASA ZAGIN ALLAH DA MANZONSA A NIGERIA?
An dade ana shiga hakkin al'ummar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam a Najeriya, sannan a take hakkin masoyan Allah da ManzonSa na gaskiya da sunan sufanci to ya zuwa yanzu tura ta gama kaiwa Bango, ina amfani rayuwu idan har za a tab'a mutuncin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam a garin Kano da sunan Maulidi, wanda tun usuli ce mana akai Maulidin Manzon Allah ake yi, me ya kutso da assasa Maulidin Shehu idan ana batun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam?
Dama tuntuni Malamanmu sun sha gaya mana, kuma mun karanta, mun gani, wannan shi ne hakikanin manufarsu, ita ce su rushe addini su yiwa Allah da ManzonSa kishiya. Mutanenan ba muslinci suka nufa ba, banda fasikanci da iskanci ba abin da suke yi, Sallah bata damesu ba, su nemi Maza su nemi mata su ci haram su yi dukkan wani nau'I na iskanci yadda ransu yake so, sannan a fake da cewa "mune masoya Sayyaduna Rasulullahi" mun sanI, kuma muna da labarin abin da wasu manya manyan Shehunai suke yi a cikin garin Kano da sunan dari'kun Sufaye, Allah ya tsinewa duk wanda ya kishiyi Allah ko ManzonSa, Allah ya turmuza hancin masu ZaginSa Sallallahu Alaihi Wa Sallam da Sahabbansa da ahalin gidan sa.
A cikin liattafin: Jawahi’ur Rasa’il na Sheikh Ibrahim Inyas shafi na [16] Kaulaha yake cewa: "ku sani cewa Allah ya koro duniya a wannan zamani har ta nufi halaka, ba kuma wanda zai kubuta daga wannan halaka sai wanda Allah ya azurta da son shehu Ahmadu Tijjani", shehu Tijjani yana cewa: "hakika 'yan Tijjaniyyah suna da wata martaba wacce takai matuka wajen daukaka, martabar da haramun ne a fadeta, ko a yayata ta, da zan gaya muku wannan martaba da mabiya gaskiya da ma’abota ilimi malamai na Allah sun yi ijma’i a kan a kashe ni, ballantana kuma gama garin mutane" wannan magana tana nan a cikin wannan littafi nasu.
To yanzu dan Allah wannan wace martaba ce idan ba SHIRKA ba, da rashin ganin girman Allah da ManzonSa Sallallahu Alaihi Wa Sallam, wannan shi ne abin da Babban Dagutu ya koya musu, wato Ibn Arabi Al Sufi. In sha Allah nan gaba zan kawo tarihin sa. To irin wadannan maganganu fa sune suka assasa zagin Allah da ManzonSa a Najeriya.
Kuma ina mamaki da mutanan da zasu baiwa kansu sunan masoya Sayaduna Rasulullahi a kano, yau a ce sati daya kenan da faruwar wannan abu amma wai har yanzu mutuminnan yana nan araye, ai yakamata a ce tuni anyi layya da shi kamar yadda aka yi layya da Malaminsa Hallaj, wanda shima Hallaj in sha Allah zan kawo tarihin sa, amma muna nan muna jira mu ji wane irin hukunci kotu zata yanke a kan wannan zindikin.
Bayan haka kuma, ba zamu taba yadda da duk wani yunkuri na baiwa wannan mutumin kariya ba, wai ace mana "DAN ISKAN GARI NE" kamar yadda abin takaici jiya wani Malami a BBC yake kokarin wanke mutumin da nuna wai dan iska ne ba da yawun kowacce darika yayi wannan farucin ba. Wannan fa shi ne irin abin nan da Turawa suke yi dan baiwa mai laifi kariya, idan ya aikata laifin da zai fuskanci hukunci mai tsanani sai su ce "ai dan iska ne ba a hayyacinsa yake ba" shi kenan sai kaji batun ya bi ruwa.
Masu wannan Aqidah to ku sani wallahi asirinku ya gama tonuwa domin fassarar littafin Ubudiyyah na IbnTaimiyyah ya kusa fitowa cikin harshen Hausa wanda babban Malamin mu Dr. Muhd Sani Umar R/lemo ya rubuta, bawani sharriniku wanda kuka rubuta a cikin littattafanku wanda ba a yi bayanisa ba, kowa zai karanta ya gani, al'aurarku ta fito fili.
Yasir Ramadan Gwale
20-05-2015
Aslm,gsky wannan posting din da kayi bai dace ba,saboda wannan cin mutuncin wani kayi ba wa'azi kayi ba, sannan kuma shiriya ya kamata ka nema masu a gurin Allah [s.w.t], bawai kana tozarta su ba..
ReplyDelete"gaskiya ce"