Saturday, May 2, 2015

Takaitacce Tarihin Imam Malik Bin Anas


IMAM MALIK BIN ANAS (IMAMU DARUL HIJRAH)

Imam Malik asalin sunansa shi ne: Malik Bin Anas Bin Malik Bin Abi Amir, Abu Abdullah, Al-asbuhi, Al-madani, Imam Darul hijra, Hujjatul Islam, an haifi Imam Malik a shekara ta (93A.H) a Madina.

Imamu Malik ya fara neman ilimi tun yana yaro karami, Allah ya yi masa kafin basira da fahimta cikin sauki, Imam Malik ya bunkasa tun yana karami, ya kai matsayin mai yin fatawa,  ya fara yin fatawa tun yana dan shekara ishirin. 

Abu Huraira Radiyallahu Anhu, ya rawaito hadisi daga Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam, yana  cewa, Annabi  ya ce: Zamani ya kusa  zuwa da mutane zasu niki gari wajen tafiya neman ilimi, amma ba za su samu Malami ba kamar malamin Madina.

Sufyan bin Uyaina ya ce: ina garin wannan Malami da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya yi ishara da shi, shi ne Imamu Malik Ibn Anas, imam Malik bai rubuta wani littafi ba face fita ce littafin nan da ya shahara da shi wato Muwadda. Imamu Malik ya rasu a shekara ta (179A.H).

Yasir Ramadan Gwale 
02-05-2015

4 comments: