IMAM AHMAD BIN HAMBAL (IMAMU AHLUSSUNNAH)
Imam Ahmad asalin
sunansa Shi ne: Ahmad bin Muhammad Bin Hanbal Bin Hilal Bin Asad,
Ash-shaibani, Al-marwazi, Abu Abdullah. An haifi Imam Ahmad a shekara ta
(164A.H), a Birnin Baghdad na Iraqi, ya kasance daya daga cikin
manya-manyan malaman duniya, malami ne wanda ya hada ilimi da tsoran
Allah da kuma aiki da abin da ya sani na gaskiya.
Wani Malami
Ibrahim alharbi a zamanin yake cewa, ban taba ganin mutumin da Allah ya
tara masa il...imin mutanan farko da na karshe ba kamar Imam
Ahmad, ana yi masa lakabi da imam Ahlussunnah saboda jajircewarsa da
tsananin riko da Sunnah lokacin fitinar: cewa kur'ani makhluq ne, wanda
imam Ahmad ya tsaya a kan cewa kur’ani zancen Allah ne kuma ba makhluq
ba ne.
Imam kutaiba yana
cewa: mafi alkhairin mutane a zamaninmu shine: Ibn Mubarak sannan wannan
saurayin, wato Imam Ahmad bin Hanbal, idan ka ga mutum yana son imam
Ahmad to ka tabbatar cewa wannan mutumin Ahlussunnah ne. Imam Ahmad ya
rasu a shekara ta (241A.H).
Yasir Ramadan Gwale
06-05-2015
No comments:
Post a Comment