SABUWAR GWAMNATIN KANO ZATA FARA DA KAMA KARYA
Labarin da yake fitowa daga Kano na nuna cewar an kame tare da garkame wani matashi Sanusi Bature Dawakintofa sabida ya bayyana ra'ayinsa a an abinda sabuwar Gwamnati ta yi. Wannan bawan Allah fa dan asalin karamar hukumar Dawakintofa ne, karamar hukumar da sabon Gwamnan Kano Ganduje ya fito, amma aka kama shi sabida ya fadi ra'ayinsa na cewar anyi almubazzaranci a kwashi mutane 70 zuwa Umrah da Ganduje yayi bayan da aka ce shi ya ci zabe.
Wannan alamu ne da suke nuna cikakkiyar kama karya da sabuwar Gwamnatin Kano mai zuwa zata yi. Akan me za'a kama Sanusi Bature Dawakintofa dan kawai ya fadi abinda ya sani ko ya gani? Shin wannan yana nuna mana cewar Gwamnatin Kano mai zuwa ba zata iya jure hamayya ba kenan ko me?
Bayan haka muna kallon yadda ake korar 'yan Hisba kawai dan basu zabi Jam'iyar Gwamna ba. Wannan kama karya ce, kuma babu inda zata je, ai 2019 ba tada Nisa. Da Kwankwaso yace idan Ganduje bai yi abinda ya kamata ba zasu canja shi, na dauka siyasa ce ashe ya san kwanan zancen.
Idan kuwa haka ne, Ganduje ya yaudari mutane, domin muna yi masa kallon mai kamala da dattako sama da Kwankwaso, ashe lokaci zai yi nan kusa da mutanen Kano zasu ce Gwanda Kwankwaso sau dubu da Ganduje? Ayi dai mu gani.
Yasir Ramadan Gwale
11-05-2015
No comments:
Post a Comment