MALAM YAYI BAKI BIYU KAN WANNAN QADIYYA TA ZAGIN MANZON ALLAH SAW
Jiya Talata 19 ga watan Mayu, a cikin shiri Rana na BBC Hausa anyi hira da Babban Kwamandan Hisbah na Kano Mal.Aminu Ibrahim Daurawa inda ya nuna cewar wannan mutum da ya zagi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ba dan Tijjaniyyah bane, Malam yace "Dan Iskan Gari" ne kawai, abinda ya bayu ga wasu zuwa ga "kamar" yunkurin bada kariya ga mai laifi.
Sannan kuma, a Shafin Babban Kwamandan hisba din na Facebook Malam ya danganta wannan lamari kai tsaya da Darikar Tijjaniyya, har ma yayi kira da mabiyanta su kaurace mata, wannan ya nuna akwai cin karo da juna tsakanin bayanan guda biyu, bayan a jiya Malam ya ce babu ruwan Tijjaniyyah a wannan magana.
Ko dai ya kasance Malam ba shi ne yake tafiyar da shafinsa na Facebook ba, dan haka ake samun cin karo na bayanansa, ko kuma maganar da yayi a BBC kuskure yayi, wanda tuni duniya ta riga ta ji. Dan haka, tilas Malam yayi kokarin daidaita bayanansa akan wannan Qadiyya kasancewarsa Babban Kwamandan Hisba na Kano, kuma daya daga cikin Malamai a Kano.
A hannu daya kuma, muna goyon Bayan Matakin da hukumar Hisba ta dauka, wanda zamu taya su da adduah. Sannan kuma, muna kira a garesu da lallai su tsaya kai da fata wajen ganin ba a shatale wannan Shari'ah ta hanyar mai da wannan mutum Dan Iskan Gari ba, ko a nuna subul da baka yayi koma ace ba a cikin hayyacinsa yayi maganar ba, wanda hakan na iya bashi damar Kubuta daga fuskantar hukunci.
Haka kuma, muna sane da cewar kwanakin baya a cikin Darikar Tijjaniyya aka samu wani mawaki da yayi kalamai na Shirka, ya sanyawa Allah kishiya wanda ta janyo har sai da Khalifa Isyaku Rabi'u ya barrantar da kansu da kalamwn wannan mawaki, aka ce mana an mika shi hannun hukuma dan yi masa Shari'ah, labarin da har ya zuwa yanzu bamu san inda aka kwana ba. To amma wallahi wannan ba zamu bari ba, zamu bibiya har sai an masa hukunci. Idan kuma hukuma ta kasa yi masa hukunci to su sani ba gata sukai masa ba, akwai Masoya Manzon Allah SAW na gaskiya a Kano suna nan suna kallon motsinsa.
Yasir Ramadan Gwale
20-05-2015
No comments:
Post a Comment