DAGUTANCIN INYASS KAULAHA KASHI NA BIYU
A cikin kashi na farko da ya gabata, mun kawo wasu maganganu da Sheikh Ibrahim Inyass Kaulaha yayi a cikin littafinsa As-sirrul akbar wan Nurul Abhar, maganganun da suke nuna shirka da kangarewa Allah Subhanahu Wata'ala, amma babu wadan su daga masu kare darikun sufaye ko mabiya Inyass din da suka karyata maganganun da hujja ko wani dalili mai karfi.
Duk abin da mabiyan Inyass din suke bai wuce soki buritsu irin na wanda hujja ta kare masa ba. Har yanzu sun kasa cewa Littattafan ba nasa bane, sannan kuma sun kasa karyata maganar cewa ba a cikin littafin take ba. To wadan da basu san meye Darikar ba ne fa su Seikh Google ke yaudara a ce musu wai an gina Tijaniya akan Zikiri da Hailala da Salatul Fatihi.
Wanda idan ka nutsa cikin Darikar babu abinda ke cikin ta sai shirka da fajirci da zina da matan mutane da aikata Luwadi da matasa. Ko Abdul jabber Nasiru Kabara a cikin martanin da yayi musu, ya kalubalanci irin wannan iskanci da suke wai shi cire gashi munkiri.
Haka kuma, Ibrahim Inyas a cikin littafinsa: Ar-Rihlatul Kanakiriyyah yana cewa wai: shi Allah ya kebance shi da ilimi, da kuma tasrifi wajen jujjuya duniya, idan ya ce: kasance, sai abu ya kasance, ba tare da bata lokaci ba, saidai duk da haka saboda ladabi ga halarar Ubangiji sai ya rike shi abin dogara, shi kuma Allah sai ya rike shi badadayi.
Karara fa Inyass na baiwa kansa matsayin Ubangiji ne, domin a duk bayanansa zaka ji maganganunsa sun nuna shi ya zarta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, wanda ake fakewa da rudar masu karanci sani cewar babu komai a cikin Darikar sai kaunar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Alhali kuwa wannan gingimemeiyar karya ce.
Allah ka nuna mana gaskiya mu fahimci gaskiya ce ka bamu ikon binta, ka nuna mana karya mu fahimci karya ce k bamu ikon kauce mata.
'Yan uwa mu hadu a kashi na gaba.
YASIR RAMADAN GWALE
27-05-2015
Allah yakara ILMI malam yasir gwale.
ReplyDeleteGASKIYA DOKIN KARFE.
da ga muhammad sanusi usman