JAN LAYIN
Ban sani ba ko wannan magana ta tabbata cewar Shugaban kasa mai jiran gado Muhammadu Buhari yace zai ja layi, daga lokacin da ya karbi iko. Amma a bisa ga abinda yake faruwa yana nuna cewar Najeriya ta kama hanyar tsiyacewa (Bankrupt), dan haka fatanmu ga sabon Shugaban kasa shi ne, Jan layin da za'a yi ya kasance ne daga 1999 zuwa baya, amma duk abinda yayo sama har zuwa 2015, lallai a binkitowa al'umma dukiyoyinsu da aka jide aka azurta kai ba bisa ka'Ida ba. Lallai zai yi matukar kyau idan sabon Shugaban kasa ya kakkafa hukumomin binciken almundahana da almubazzaranci da akai da dukiyar al'umma tun daga 1999 har zuwa 29 ga may in 2015.
Wanda duk suka kwashi kudin kasa ba bisa ka'Ida ba su dawo da su, sannan ai musu hukunci daidai da abinda dokar kasa ta tanadar. Nayi Imani duk wanda aka binkita kuma aka sameshi da rubda ciki da dukiyar al'umma kuma aka kwace aka hukunta shi, to wallahi taimakon sa akai, domin idan ya tsallake anan duniya akwai wani bincike a Lahira, kowa zai zo da gwargwadan abinda ya dauka ba na hakkin sa ba.
Fatanmu shi ne a gina kasa da kudin kasa, dan Najeriya shima yayi alfahari da kasar sa. A inganta harkokin Ilimi da noma da kiwo, da sufuri, da wuta lantarki, da harkokin lafiya, da tsaron kasa. A cusa kishin kasa a zukatan al'umma, a sanya mutane kiyaye bin doka da ka'Ida. Dan kasuwa yayi kasuwancinsa cikin gaskiya da tsoron Allah, wanda yayi algus ko yayi ha'inci ko yayi yaudara ko zamba ko cin amana a hukunta shi bisa tanadi doka.
Ma'aikata su kiyaye amana da aka danka musu, a farfado ko inganta hukumomin kula da d'a'ar ma'aikata. Kowanne ma'akaci a ko ina yake yaji cewar wajibin sa ne ya hidimtawa kasa, ya kare Martabar kasar sa. A tarbiyyantar da ma'aikata akan tausayi da jin kai da kula da mutuntakar al'umma.
Al'umma kowa yaji cewa kasar sa na alfahari da shi, shima yana alfahari da kasar sa. Sau da dama, nakan ga wasu kasashen na mutunta tutar kasarsu akan tutar jam'iya, amma mu a wajenmu tutar jam'iya tafi ta kasa muhimmanci, akan cire tutar jam'iya sai kaga ana ta kai ruwa rana da mutane, amma sunyi ko in kula da tutar Najeriya.
Allah ya sa mu shiga wannan sabon zubin Shugabanci a sa'a. 'Yan Najeriya su kasance mutanan kirki a idon kasashen duniya ba da anga dan Najeriya a fara tunanin rashin gaskiya ko cewa ga wani mazambaci ba. Sunan Najeriya da 'yan Najeriya yayi matukar baci a kasashe da dama, inda har takai matsayin da 'yan Najeriya sun gwammace suyi amfani da fasfunan wasu kasashen da basu kai Najeriya ba, domin gudun tozartawa ko wulakantawa.
Hakki ne da ya rata ya a wuya duk dan Najeriya kokarin dawo da Martabar sunan Najeriya, kamar yadda Marigayi tsohon Shugaban kasa Umaru YarAdua ya so aiwatar wa, Allah bai bashi dama mai yawa ba. Allah ka taimaki kasarmu ka bamu Nasara da karuwar arziki da cigaba mai dorawa.
Yasir Ramadan Gwale
10-05-2015
No comments:
Post a Comment