Sunday, May 24, 2015

Da Me Zamu Tuna Gwamnoni Masu Barin Gado?


DA ME ZAMU TUNA GWAMNONI MASU BARIN GADO?

Tun daga kammala babban zabe na kasa, muka kasa kunne danjin yadda zata kaya a wasu jihohin game da sha'anin mikawa da karbar mulki daga tsaffin Gwamnoni zuwa sabbi. Naji dadi sosai da jin cewar Gwamnan Katsina Barr. Ibrahim Shema fadin cewar zai bar kudi wajen Naira Biliyan 4 a asusun Gwamnati, sannan ana lisfta shi a zaman gwamna daya tilo da zai bar mulki ba tare da ya barwa jiharsa bashin ko kwandala ba, hakika wannan abin a yaba masa ne, idan akai la'akari da abinda ke faruwa a sauran jihohi.

Ba shakka abinda na gani ya faru a jihar Jigawa ya bani mamaki, irin yadda naga mutane da dama suna zubda hawaye da nuna alhini a makon da ya gabata don rabuwa da Gwamna Sule Lamido. Ba shakka Gwamna Sule Lamido​ yayi abin a yaba masa a wannan shekaru takwas da ya kwashe. Sule lamido ya samu Jigawa tamkar koramar da ta kafe ta tsotse, amma ya inganta ta, ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa da gina jihar, har ta kai Jigawa na amsa sunanta na sabuwar duniya. Naji ana cewa tun da aka yanke Jigawa daga Kano, bata samu Gwamnan da ya hidimta mata ba, kamar Malam Sule Lamido, Allah ya saka masa da alheri, kurakuransa kuma Allah ya yafe masa.

SannĂ n naji tausayin 'yan uwa na jama'ar jihar Bauchi da ba albashi wajen kwana sittin da biyar, bayan kuma a bay wasu na bin  bashin na baya. Na kyautatawa Malam Isa Yuguda zato cewa mutum ne mai jin kai da tausayin al'umma, musamman ma'aikata, amma kwatsam, sai abubuwa suke sauyawa, duk da cewa shima Gwamna Yuguda yana da irin nasa alkhairan da ya yiwa jihar Bauchi.

Kwastsam sai muka ji a jihar Bauchin cikin satinnan ana bandar hannun jarin kamfanin intercelular da ya jima a sume, na dukkan kananan hukumomi 20 dake jihar, wanda ake kiyasta yakai wajen Naira Miliyan  300, amma ana ta gaggawar neman layar zana dasu kafin 29 ga mayu, Haba dattijo Malam Isa Yuguda ko don fulaku na fulatanci a tausayawa al'ummar Bauchi mana. ma'aikata na ta bulayi, 'yan kasuwa ba ciniki, jama'a kamar a rude, rana zafi inuwa kuna, kowa yana wayyo Allah. Malam Isa Yuguda a tausayawa al'umma a rabu lafiya.

A jiharmu mai albarka kuwa, ance ana yiwa juna  kallon kallo, tsakanin Gwamna mai tafiya da mai shigowa. A tsawon Shekarun Kwankwaso hudu yana rike da ragamar Gwamnatin Jihar kano, yayi abubuwan alheri da za'a jima ana tunawa da shi, an yi gadar sama waddata tayi kyau kuma tana bada sha'awa, an gina azujuwa, an samar da sabuwar jami'ah ta Arewa Maso Yamma.

Haka kuma, wasu rahotanni musamman wanda Premium Times​ ta ruwaito na cewar Gwamna zai bar bashin da ya kai kimanin Naira Biliyan 200, ga kuma bashin tituna masu tsawon kilo mita biyar da akai alkawari a kananan hukumomi 44 tun farkon gwamnati ba'a yi ba a mafiya yawancin kananan hukumomi.

Gwamnan jihar Neja kuma shugaban Gwamnonin Arewa mai barin gado shima ance ya cika ciki da bashi duk da kuri da yayi a baya. Bayanai sun nuna cewar Gwamna Aliyu bai yi wani aikin kuzo mu gani ba, a matsayinsa na Shugaban Gwamnonin Arewa, ayyukansa basu taka kara sun karya ba, idan aka hada shi da takwarorinsa irinsu Sule Lamidoda Shehu Shema da Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso​. komi za'a haifa? mun dai zuba ido sai mun gani.

A yobe kuwa, jama'a da dama na tafadin kasawar Gwamna Bra-bra, domin bayanai sun nuna baiyi wani aikin kirki ba, duk kuwa da cewar a gwamnonin da zasu shiga zagaye na biyu yafi kowa samun isasshen lokaci a baya, domin tunkafin shekaru biyu da wannan zubin mai karewa yake rike da akalar jihar Yobe. Ba ko shakka, jihar tayi fama da hare-haren 'yan ta'adda, amma dai an samu sararin da ya kamata ace anyiwa al'umma ayyukan ku zo mu gani a lokacin da aka samu.

Yasir Ramadan Gwale
23-05-2015

No comments:

Post a Comment