Sunday, May 31, 2015

YAKIN YEMEN: Abinda Sa'udiyya ta Ke Yi . . .


YAKIN YEMEN: ABINDA SA'UDIYYA TA KE YI . . .

A ranar 26 ga watan Maris na wannan Shekarar ne kasar Musulunci ta Sa'udiyya ta bayar da sanarwar kammala dukkan wasu shirye shirye domin fara kai hare hare ta sama ga yankunan da 'yan tawayen Yaman masu samun cikakkiyar gudunmawa daga Iran suka mamaye. 

Ba tare da wata wata ba kasashen yankin Gulf gaba dayansu suka nuna cikakken goyon bayan su ga wannan Yaki; Haka suma kasashen da ba na Gulf ba da suka hada da Jordan da Egypt da Sudan suka nuna cikakken goyon bayan su ga wannan Yaki, da ake ganin shi ne aikin sabon Sarki Salman Bin Abdulaziz Allah ya kara masa lafiya na farko da ya shiga.

Da yawan mutane na da masaniyar abinda ke faruwa a Yemen, dan haka zamu maida hankali ne akan wannan Yaki kacokam da kuma dalilin faruwarsa. Wato abinda yake faruwa a Gabas ta tsakiya shi ne, yunkurin da shedaniyar kasar Iran take yi na mamayar yankin gaba dayansa, tare da yi masa daurin butar Malam. 

Har kullum, abinda kasar Iran take kwana kuma take tashi da shi shine batun yadda zata rusa Ka'aba a Makkah, su shiga Madina su sace gawar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, su maida ita biranensu da suke kira da masu tsarki, sannan su tone k'aburburan Sayyaduna Abubakar da Umar sannan su je Baqee'a su tone kabarin Nana Aisha su yi musu wulakanci. A Takaice wannan shi ne Babban hadafin shedaniyar kasar Iran. 

Kada ka taba yin mamaki da jin wannan zance, wannan ita ce hakikanin manufar kasar Iran, burinsu a rushe Musulunci, ya zama a duniya daga kafurci sai Shianci, wanda kashin bayan su shi ne aikata fasadi da Alfasha a ban kasa. A sabida haka ne, suka hada baki ta fuska biyu, na farko shi ne da kasashen gurguzu da ba ruwansu da Allah ba ruwansu da addini irinsu China da Russia sannan a gefe guda kuma suna da boyayyar alaka mai karfi da Amurka da kasashen Turai na Yamma. 

Tun bayan kammala Berlin Conference manyan kasashen duniya suka kasa duniya gida gida suka fahimci babu wani abu ko yanki da yake zamar musu barazana kamar yaduwar addinin Musulunci a kasashen Sunni, musamman a Gabas ta tsakiya da Arewacin Afurka, wanda a definition din su, idan sun ce kasashen sunni suna nufin kasashen da ba na Shiah ba, ko da kuwa 'yan Bid'ah ne.

Zan cigaba In sha Allah. 

Yasir Ramadan Gwale
31-05-2015

Saturday, May 30, 2015

Goodluck Jonathan Ya Cancanci Jinjina Da Yabo


GOODLUCK JONATHAN YA CANCANCI JINJINA DA YABO A WANNAN ZABE

Ba shakka maganar ba zata yiwa wasu dadi ba, amma gaskiya ce dole mu fade ta. A hakikanin gaskiya dole a yabawa tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan​ a wannan zabe da ya gabata. Wasu na ganin ai babu wani abun yabawa dan Jonathan ya amince da shan kaye,  wanda wannan Sam ba gaskiya bane, a magana ta gaskiya. 

Me yasa nace haka? Mu kalli kasar Syria, kuma mu kalli abinda ke faru a kasar yanzu, sannan mu kalli yanayin da muke ciki. Mutanan kasar Suriya suka ce, sun gaji da mulkin Shekaru fiye da Ashirin na mulkin zurriyar Assad, dan haka suke san ayi sabon zabe dan samun sabon Shugaban kasa. Amma Bashar  Assad a yace Allah ya kashe duk mutanan Syria shi ba zai sauka ba.

Haka ne ya faru, Assad Yaki sauka ya tabbatar da kansa a Mulki a lokacin da jinin al'ummar Siriyawa yake kwarara a birane Alepo da Dar'a da Homs da Damaskus. Ya rushe kasar gaba daya, ya kashe dubban mutane, a yayin da Miliyoyin suka fice suka bar kasar, da yawan Siriyawa sun zama almajirai a kasashen duniya da dama, Assad ya raba mutane da garuruwan su abin alfaharinsu, da yawan wasu sun bar siriya har abada. 

Yau ko da kasar Suriya ta samu zaman lafiya, shekaru nawa za'a dauka kafin a gina inda Assad ya rurrusa?  Ba komai yasa Bashar Assad aikata wannan mugun ta'addancin ba illa kawai yunkurin tabbatar da kansa a mulki ko ana so ko ba'a so. Yanzu fa batun da ake kasar Suriya ta zama Kango, an rushe ko ina, babu wani abu da yake aiki, ba makarantu, babu asibiti, babu kamfamoni, babu sufuri, komai ya koma zero! Duk sabida tabbatar Bashar Assad akan mulki.

Yanzu tsakani da Allah, da Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi taurin kai irin na Bashar Assad a me muke zaton zai faru a Najeriya? Yaki ne gagarumi wanda za'a samu ba tare da mun shirya ba. Kasashen duniya musamman Turai da Amurka zasu marawa Jonathan baya, musamman idan ya makalawa mutanan Arewa Boko Haram. Yai ta kashe mutane domin tabbatar da kansa a mulki, kuma kasashen duniya na bashi goyon baya.

Duk wanda yake kallon abinda ke faruwa da musulmin Rohingya a kasar Burma ko Myanmar zai tabbatar da cewa kasashen Turai da Amurka munafukai ne, domin duk wani shugaba da zai gallazawa Musulmi suna iya d'aga masa kafa a kauda kai daga gareshi kamar yadda har yanzu babu wanda ya zargi hukumomin Myanmar da aikata laifi ga Musulmin Rohingya, illa Majalisar dinkin duniya dake maganar agaji kawai.

Yanzu idan Najeriya ko Arewa ta fada cikin Yaki gashi ba wani tanadi ake da shi na kariya ba me zai faru? Haka nan mutanan Arewa zasu fantsama kasashen Nijar da Kamar da Chadi da Sudan da sauransu domin neman mafaka. 

Amma a sabida kaucewa fadawa irin wannan hali irin na Mutanan Suriya tare da sallama wa zab'in al'umma, da kuma kaucewa fadawa Yaki.  Duk kuwa da cewar kasashe da dama sunyi Nazarin cewar a wannan lokacin Najeriya zata shiga mummunan Yakin da Allah ne kadai yak san karshensa. Allah cikin ikon sa ya tsallakar da mu fadawa Yaki.

Abin da wasu har yanzu basu fahimta ba shi ne, dan an ce Goodluck Jonathan yayi abin a yaba masa, ai ba shi ke nuna an tsarkaka shi daga laifukan da ya aikata ba. Ba shakka Jonathan nada nasa laifukan masu yawa kamar kowanne tsohon Shugaban kasa a Najeriya, amma wannan ba zai zama dalilin da zai sanya mu kasa yi masa adalci ba.

Na taba fadin cewar, Jonathan mutum ne mai matukar Hakuri da kuma kauda kai. A gefe guda kuma yana da sakaci ainun da abubuwa na wajibi a gareshi, harkar tsaro da cin hanci da muguwar sata da kazamar cuwa cuwa duk sun dabaibaye harkar man fetur a Gwamnatinsa, amma bai yi wani abun ku zo mu gani ba na dakile hakan. 

Amma duk da haka yayi abin a yaba masa kuma a jinjina masa wajen nuna dattako da karbar kaddara tun kafin a ayyana sakamakon zabe. Wannan manazarta da dama suka dinga cewar ya tsallakar da Najeriya daga fadawa Yaki da zubar jini. Shi kansa sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari​ ya yabawa Jonathan ta wannan fannin, ya kuma sha alwashin tsare martabar Jonathan a matsayinsa na tsohon Shugaban kasa.

Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya a kasarmu.

Yasir Ramadan Gwale 
30-05-2015

Friday, May 29, 2015

BUHARI: By an Shan Rantsuwa Kuma Sai Me?


BAYAN SHAN RATSUWA UMAR SAI ME?

Yau Juma'a Babbar Rana a Musulunci, aka rantsar da sabon zababben Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari​ a matsayin Shugaban kasa Karo na biyu kuma shugaba na goma sha shida. Kamar yadda manazarta ke ta fadi, kalubalen da ke gaban sabon Shugaban kasa yana da yawa ainun, sannan al'umma sun zura ido, sun kasa kunne wajen ganin anyi aiki sha yanzu magani yanzu.

Jam'iyar APC da Shugaban kasa sunyi alkawura a lokacin yakin neman zabe. Anyi alkawura musamman akan abinda ya shafi Tsaro da Tattalin arzikin da Ilimi da sha'anin tafiyar da Gwamnati da sauransu. A bisa wadannan alkawaruka da ma wasu al'umma da dama suka zabi sabon Shugaban kasa da jwm'iyawrsa a watan da ya gabata.

Fatanmu da addu'ah da zamu yi wa wannan Gwamnati shi ne, Allah ya basu ikon sauke wannan nauyi, babu shakka Allah ya basu dama ta yin duk  wasu ayyuka da zasu kyautata rayuwar 'yan Najeriya birni da karkara. Muna kuma da yakinin cewar Shugaba Muhammadu Buhari​ zai iya fiye da yadda ake tsammani. Ya Allah ka sahale masa wannan gagarumin aiki. Allah ka sa alkawuran da ya dauka su zama hujja a gareshi ba hujja akansa ba.

Suma sabbin Gwamnonin da aka rantsar a yau, muna yi masu fatan alheri da kuma tuna musu girman kalubalen da ke kansu. Allah ya basu ikon yiwa al'umma hidima, tare da tsare mutunci da martaba da addinin wadan da suke jagoranta. 

Allah ka sa wannan sauyi ya zama alheri ga Najeriya da duk 'yan Najeriya a ko ina suke a duniya. Allah yasa ayi shugabanci bisa gaskiya da adalci. 

Yasir Ramadan Gwale 
29-05-2015

Wednesday, May 27, 2015

Ba zamu Manta Da Zagin Da Akaiwa Manzon Allah SAW A Kano Ba



BA ZAMU MANTA DA ZAGIN DA AKAIWA MANZON ALLAH A KANO BA

Yau a kano, da wani Malamin Izala ne yace "Sai Ya tattaka Wuyan Inyass" da yanzu Kano tana nan kamar za ai tashin alkiyama, su Sheikh Google su yita kurari da barazanar karya, suna kiran Bala'i zai sauka a Kano tunda aka zagi waliyyiyai.

Amma yanzu an taba Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, shiru kake ji, wasu ma sabida tsabar bakin jahilci da rashin sanin meye martaba da Darajar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, mune ma masu laifi a wajensu, sabida muna daga maganar, a cewarsu, wai sai dai mu yiwa wanda sukai zagin adduar shiriya. Wallahi karya ne! Hatta 'Ya 'yanmu da jikokinmu sai mun basu labarin cewar 'yan Tijaniya sun zagi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam a unguwar Makwarari a Kano.

Muna kuma kara tunasar da hukumomi cewar, wallahi wannan maganar ba zamu yi shiru ba, matukar bamu ga an yankewa wadannan zindikai hukunci ba, In sha Allah kotu ta sake su tace basu sabawa dokar kasa ba. Anan ne zasu san cewar ba gata sukai musu ba, Wallahi Darajar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam tafi komai a wannan rayuwa. Rayuwarmu fansa ce gareka Ya Rasulullah!

YASIR RAMADAN GWALE
27-05-2015

Akan Inyass Kaulaha Aka Zagi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam?!


AKAN INYASS KAULAHA AKA ZAGIN MANZON ALLAH SAW?

Wallahi duk wanda yake zaton za'a taba martabar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam mu yi shiru ya yaudari kansa. Wallahi Tallahi Manzon Allah yafi ubana yafi ubanka yafi duk wani shehi na da da na yanzu. Wallahi wadannan mutanan karya suke ba kaunar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam  suke ba, tsakaninmu da Allah yadda suke kambama Maulidin Inyass Kaulaha da yadda suke kashe kudi haka suke kambama Maulidin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam? Wannan babban dalili ne da zai tabbatar wa mai shakka cewar ko Maulidin da suke da sunan Manzon Allah karya suke sun fake ne dan su tabbatar da kafa Maulidin Inyass Kaulaha.

Wallahi karya suke, ba kaunar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam suke yi ba. Duk wanda yace wai wannan abinda su Abdul Inyass suka fada wai ba da yawunsu akai ba,  karya suke munafukai ne, sun san wannan abin da Allah ya tona musu asiri ta bakin su Abdul Inyass,  shi ne faira shi ne hakika kuma shi ne abinda Tijaniya ta kansa, basa kaunar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam basa ganin girman Allah.

Shin yau aka fara irin wannan kafuricin a Kano ko kuma a cikin Tijaniya? Shekara da Shekaru suna yin wannan shirka da kafurci suna shiga cikin Musulmi suna sajewa,  sai yanzu ne Allah ya fara tona musu asiri. Duk wanda ya rike wani mutum ba Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam wallahi ya tab'e ya halaka.

Duk wannan abin da ke faruwa a Tijaniya Ibrahim Inyass Kaulaha shi ne ya assasa shi. Wallahi Inyass tataccan dan Damfara ne, mushrikai,  zindiki, ya cuci al'Umar Musulmi a Najeriya, yayi musu fashin Imani ya raba su da Allah ya raba su da ManzonSa Sallallahu Alaihi Wa Sallam.  Babu wani mutum da zai ce Inyass Kaulaha mutumin kirki ne, ta ina ya zama mutumin kirki? Shin abinda ke cikin Faila da hakika ba a cikin Tijaniya suke ba? 

Wallahi akan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ba zamu daina la'antar wadannan mushrikai ba, wanda duk zai ji haushi yaji, wanda zai b'ata Rai ya b'ata. Abinda na sani ne kuma nayi Imani da shi cewar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam yafi ubana yafi ubanka, yafi shehinka yafi uban shehinka. Ba zamu gushe ba muna ce muku Allah ya isa bamu yafe ba.

Yasir Ramadan Gwale

Dagutancin Inyass Kaulaha kashi Na Biyu



DAGUTANCIN INYASS KAULAHA KASHI NA BIYU 

A cikin kashi na farko da ya gabata, mun kawo wasu maganganu da Sheikh Ibrahim Inyass Kaulaha yayi a cikin littafinsa As-sirrul akbar wan Nurul Abhar, maganganun da suke nuna shirka da kangarewa Allah Subhanahu Wata'ala, amma babu wadan su daga masu kare darikun sufaye ko mabiya Inyass din da suka karyata maganganun da hujja ko wani dalili mai karfi. 

Duk abin da mabiyan Inyass din suke bai wuce soki buritsu irin na wanda hujja ta kare masa ba. Har yanzu sun kasa cewa Littattafan ba nasa bane, sannan kuma sun kasa karyata maganar cewa ba a cikin littafin take ba. To wadan da basu san meye Darikar ba ne fa su Seikh Google ke yaudara a ce musu wai an gina Tijaniya akan Zikiri da Hailala da Salatul Fatihi. 

Wanda idan ka nutsa cikin Darikar babu abinda ke cikin ta sai shirka da fajirci da zina da matan mutane da aikata Luwadi da matasa. Ko Abdul jabber Nasiru Kabara a cikin martanin da yayi musu, ya kalubalanci irin wannan iskanci da suke wai shi cire gashi munkiri. 

Haka kuma, Ibrahim Inyas a cikin littafinsa: Ar-Rihlatul Kanakiriyyah yana cewa wai: shi Allah ya kebance shi da ilimi, da kuma tasrifi wajen jujjuya duniya, idan ya ce: kasance, sai abu ya kasance, ba tare da bata lokaci ba, saidai duk da haka saboda ladabi ga halarar Ubangiji sai ya rike shi abin dogara, shi kuma Allah sai ya rike shi badadayi. 

Karara fa Inyass na baiwa kansa matsayin Ubangiji ne, domin a duk bayanansa zaka ji maganganunsa sun nuna shi ya zarta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, wanda ake fakewa da rudar masu karanci sani cewar babu komai a cikin Darikar sai kaunar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam.  Alhali kuwa wannan gingimemeiyar karya ce.

Allah ka nuna mana gaskiya mu fahimci gaskiya ce ka bamu ikon binta, ka nuna mana karya mu fahimci karya ce k bamu ikon kauce mata.

'Yan uwa mu hadu a kashi na gaba.

YASIR RAMADAN GWALE​
27-05-2015

Tuesday, May 26, 2015

Gareka Malam Fatuhu Mustapha


GAREKA FATUHU MUSTAPHA

Wato irin kiyayyar da abokina Dan Bidiah Fatuhu Mustapha suke yiwa Sunnah ta kai matuk'a. Yanzu kuma, sun gaji da yin soki burutsu akan su Ibn Taymiyya da Muhammad Bin AbdulWahhab, sunga ba ci, sun koma ganin laifin, Saudi Arabia wai dan me, Mamlakar zata baiwa 'yan Najeriya guraben karo karatu su karanci addini?! A cewar Fatuhu Dan Bid'ah, me yasa basa bayar da damar karanta sashin lafiya da injiniya da sauran fannonin rayuwa ga 'yan Najeriya.

Alhamdulillah, muna yiwa Allah godiya da wannan falala da yayi mana. Babu abinda zamu ce ga Al-Saud sai godiya da adduar fatan alheri, domin yanzu haka adadin mutanan da suka zama daktoci a katafariyar Jami'ar Islamic University of Madinah sun kai 25 'yan Najeriya. Wannan jami'ah, ta zama sila wajen ceto miliyoyin al'ummar Najeriya daga B'ata da Bid'ah da shirka da kangarewa Allah.

Abinda su Fatuhu ba su sani ba shi ne, mun fi bukatar sanin addini da yadda zamu bautawa Allah ba tare da mun hada Allah da wani abin halitta ba wajen Ibada (Shirka). Alhamdulillah, Ilimin Tauhidi da su Fatuhu basa son al'umma su sani, kullum yaduwa yake kamar wutar daji. Al'umma kara samun wayewa suke game da addinin, ko wane lungu da sako kahe zaka ga ana karantar da Sunnah, gidajen Radiyoyi da kafafe irinsu Facebook ba abinda kake ji sai maganar Sunnah.

Shi ya sa kullum hankalin su Fatuhu a tashe yake irin yadda suke ganin, kullum kasuwar Bid'ah kara mutuwa take, jama'a sai watsi suke yi da D'arikun Sufaye suna kama Hanyar Sunnah mikakkiya da zata sada su da Allah da ManzonSa ba tare da sunyi shirka ba. Wannan abin da alama ya dugunzuma su Fatuhu, sun rasa abin yi. Shi yasa kullum daga su ce, Ibn Taymiyya kaza da kaza, sai su ce Wahabiyya, Izala da sauransu.

Amma, Albishirin su Fatuhu, ina fatan zasu ce Dabino Ajwa. Muna matukar jin dadi ku ce mana Wahabiya sama da ko wane suna da zaku Jingina mana. Abin da kawai muke so ku gane, shi ne, mu ba wai Daular Sa'udiyya muke bi ba dan yiwa Allah bauta. Muna bin addinin Allah ne, kamar yadda ya aiko ManzonSa Sallallahu Alai Wa Sallam da shi. Muna da yakinin alkhairan da Daular Sa'udiyya ta wanzar yafi sharrinsu, munyi Imani su ne daular da suka fi kowacce Daula a duniyar yau Bin Tafarkin Sunnah. Bamu taba ganinsu a matsayin wasu ma'asumai ba, muna tare da su a inda suka yi daidai, muna kuma barranta daga garesu a inda suka kaucewa Addini. 

Daga karshe, ina amfani da wannan kafa, domin yin kira ga abokina Fatuhu da ya watsar da duk wasu Bidi'o'i da yake yi da sunan addini ko bin darikun Sufaye, ka zo mu bi Sunnar Baban Qassim Sallallahu Alaihi Wa Sallam, hanya d'od'ar da zata sadaka da Allah Madaukakin Sarki lami lafiya ranar gobe alkiyama.

YASIR RAMADAN GWALE
26-05-2015

Taya Murna Ga Sabon Daktan Sunnah


TAYA MURNA GA SABON DAKTAN SUNNAH

Alhamdulillah, ina amfani da wannan dama nayi Allah godiya da ya kara sanyawa wannan tafiya Sunnah albarka. A jiya Lahadi dan uwa Malam Jamilu Yusufu Zarewa ya samu matsayin Dakta a katafariyar Jami'ar Musulunci ta Madina. Ba shakka muna alfahari da wannan cigaba musamman a fa gen Fiqihu da al'umma ke kishirwarsa. 

Ina maka fatan alheri dan uwa Dr. Jamilu Zarewa, Allah ya yi maka jagoranci yayi riko da hannunka ya yalwata kirjinka. Ina taya ka murna kai da iyalanka na samun wannan daukaka. Allah ya cigaba da amfanar da al'umma da rayuwarka. Alf Alf Mabrouk.

Yasir Ramadan Gwale
26-05-2015

Monday, May 25, 2015

Taya Murna Ga Sabon Daktan Sunnah


TAYA MURNA GA SABON DAKTAN SUNNAH

Alhamdulillah, ina amfani da wannan dama nayi Allah godiya da ya kara sanyawa wannan tafiya Sunnah albarka. A jiya Lahadi dan uwa Malam Jamilu Yusufu Zarewa ya samu matsayin Dakta a katafariyar Jami'ar Musulunci ta Madina. Ba shakka muna alfahari da wannan cigaba musamman a fa gen Fiqihu da al'umma ke kishirwarsa. 

Ina maka fatan alheri dan uwa Dr. Jamilu Zarewa, Allah ya yi maka jagoranci yayi riko da hannunka ya yalwata kirjinka. Ina taya ka murna kai da iyalanka na samun wannan daukaka. Allah ya cigaba da amfanar da al'umma da rayuwarka. Alf Alf Mabrouk.

Yasir Ramadan Gwale
26-05-2015

Sunday, May 24, 2015

Da Me Zamu Tuna Gwamnoni Masu Barin Gado?


DA ME ZAMU TUNA GWAMNONI MASU BARIN GADO?

Tun daga kammala babban zabe na kasa, muka kasa kunne danjin yadda zata kaya a wasu jihohin game da sha'anin mikawa da karbar mulki daga tsaffin Gwamnoni zuwa sabbi. Naji dadi sosai da jin cewar Gwamnan Katsina Barr. Ibrahim Shema fadin cewar zai bar kudi wajen Naira Biliyan 4 a asusun Gwamnati, sannan ana lisfta shi a zaman gwamna daya tilo da zai bar mulki ba tare da ya barwa jiharsa bashin ko kwandala ba, hakika wannan abin a yaba masa ne, idan akai la'akari da abinda ke faruwa a sauran jihohi.

Ba shakka abinda na gani ya faru a jihar Jigawa ya bani mamaki, irin yadda naga mutane da dama suna zubda hawaye da nuna alhini a makon da ya gabata don rabuwa da Gwamna Sule Lamido. Ba shakka Gwamna Sule Lamido​ yayi abin a yaba masa a wannan shekaru takwas da ya kwashe. Sule lamido ya samu Jigawa tamkar koramar da ta kafe ta tsotse, amma ya inganta ta, ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa da gina jihar, har ta kai Jigawa na amsa sunanta na sabuwar duniya. Naji ana cewa tun da aka yanke Jigawa daga Kano, bata samu Gwamnan da ya hidimta mata ba, kamar Malam Sule Lamido, Allah ya saka masa da alheri, kurakuransa kuma Allah ya yafe masa.

Sannàn naji tausayin 'yan uwa na jama'ar jihar Bauchi da ba albashi wajen kwana sittin da biyar, bayan kuma a bay wasu na bin  bashin na baya. Na kyautatawa Malam Isa Yuguda zato cewa mutum ne mai jin kai da tausayin al'umma, musamman ma'aikata, amma kwatsam, sai abubuwa suke sauyawa, duk da cewa shima Gwamna Yuguda yana da irin nasa alkhairan da ya yiwa jihar Bauchi.

Kwastsam sai muka ji a jihar Bauchin cikin satinnan ana bandar hannun jarin kamfanin intercelular da ya jima a sume, na dukkan kananan hukumomi 20 dake jihar, wanda ake kiyasta yakai wajen Naira Miliyan  300, amma ana ta gaggawar neman layar zana dasu kafin 29 ga mayu, Haba dattijo Malam Isa Yuguda ko don fulaku na fulatanci a tausayawa al'ummar Bauchi mana. ma'aikata na ta bulayi, 'yan kasuwa ba ciniki, jama'a kamar a rude, rana zafi inuwa kuna, kowa yana wayyo Allah. Malam Isa Yuguda a tausayawa al'umma a rabu lafiya.

A jiharmu mai albarka kuwa, ance ana yiwa juna  kallon kallo, tsakanin Gwamna mai tafiya da mai shigowa. A tsawon Shekarun Kwankwaso hudu yana rike da ragamar Gwamnatin Jihar kano, yayi abubuwan alheri da za'a jima ana tunawa da shi, an yi gadar sama waddata tayi kyau kuma tana bada sha'awa, an gina azujuwa, an samar da sabuwar jami'ah ta Arewa Maso Yamma.

Haka kuma, wasu rahotanni musamman wanda Premium Times​ ta ruwaito na cewar Gwamna zai bar bashin da ya kai kimanin Naira Biliyan 200, ga kuma bashin tituna masu tsawon kilo mita biyar da akai alkawari a kananan hukumomi 44 tun farkon gwamnati ba'a yi ba a mafiya yawancin kananan hukumomi.

Gwamnan jihar Neja kuma shugaban Gwamnonin Arewa mai barin gado shima ance ya cika ciki da bashi duk da kuri da yayi a baya. Bayanai sun nuna cewar Gwamna Aliyu bai yi wani aikin kuzo mu gani ba, a matsayinsa na Shugaban Gwamnonin Arewa, ayyukansa basu taka kara sun karya ba, idan aka hada shi da takwarorinsa irinsu Sule Lamidoda Shehu Shema da Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso​. komi za'a haifa? mun dai zuba ido sai mun gani.

A yobe kuwa, jama'a da dama na tafadin kasawar Gwamna Bra-bra, domin bayanai sun nuna baiyi wani aikin kirki ba, duk kuwa da cewar a gwamnonin da zasu shiga zagaye na biyu yafi kowa samun isasshen lokaci a baya, domin tunkafin shekaru biyu da wannan zubin mai karewa yake rike da akalar jihar Yobe. Ba ko shakka, jihar tayi fama da hare-haren 'yan ta'adda, amma dai an samu sararin da ya kamata ace anyiwa al'umma ayyukan ku zo mu gani a lokacin da aka samu.

Yasir Ramadan Gwale
23-05-2015

Masu Bautar Inyass Kaulaha


MASU BAUTAR INYASS KAULAHA


Zaka ji mamaki yadda mutane da suke kiran kansu musulmi, amma suna Ikirarin shirka da bakin su, ta hanyar bayyana cewa su Inyass Kaulaha ne ya halicce su, kuma shi suke bautwa. Wato irin wadannan zaka tausaya musu ne, domin bayan kasancewarsu Mushrikai, sannan Tantagaryar Jahilai ne na buga misali. Yanzu tsakani da Allah, ta yaya mutum mai hankali zai ce yana Bautawa Inyass Kaulaha ko yace Inyass Kaulaha ne ya halicce shi, bayan kuwa Inyass Kaulaha bai iya hana kansa mutuwa ba! Dan Allah ina hankali anan?

Idan anbi ta barawo Abi ta mabiyin Barawon. Muna kyautata zaton da yawan wasu mutane musamman Matasa da Mata suna yin Tijaniya ne dan an nuna musu kaunar Manzon Allah a ciki, sun shiga da wannan manufar, kamar yadda Sheikh Google yake cewa babu komai a cikin Tijaniya sai Salati da Zikiri da Hailala sannan ba'a shan taba sigari. Da dama sukan dauka haka Tijaniyar take, kuma akan haka suka shiga, amma a zahirin gaskiya an boyewa wasu abubuwa da yawa. Sai mutum ya dahu tukuna ake bayyana masa hakikaninta. 

Duk mutum mai san gaskiya da tsoron Allah, da kuma ya san meye hakikanin Tijaniya, kuma yasa waye Inyass Kaulaha, to bai isa yace irin wadannan miyagun kalmomi na Shirka basa cikin littattafan Tijaniya ba. Abin haushi da takaici kaga wasu na Ikirarin Sunnah amma suna ta kokarin wanke Tijaniya daga wadannan maganganu na shirka dan suna son burgewa, ko kuma dan ita ake yi a gidansu ba zasu iya kalubalantarta ba. 

Da ace Hujja mutane suke nema suyi addini, da kowa yabi Sunnah, amma ina shiriya a hannun Allah take. Wanda duk Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi, wanda Allah ya shiryar shi ne hakikanin shiryayye. Namu shi ne isar da sakon abinda muka yi tsuwurwuri daga Malamanmu na daga maganganun magabata. 

In sha Allah daga gobe zamu fara gabatar da bayanai akan Tijaniya da Inyass Kaulaha, daga cikin littattafan Tijaniya. Ya Allah ka nuna mana gaskiya mu fahimceta kuma ka bamu ikon binta, ka nuna mana karya mu fahimceta kuma ka bamu ikon kauce mata. Allah ka tabbatar da dugaduganmu akan bin Sunnar ManzonKa Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Yasir Ramadan Gwale
24-05-2015

Wednesday, May 20, 2015

Malam Yayi Baki Biyu Akan Wannan Qadiyya Ta Zagin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam


MALAM YAYI BAKI BIYU KAN WANNAN QADIYYA TA ZAGIN MANZON ALLAH SAW

Jiya Talata 19 ga watan Mayu, a cikin shiri Rana na BBC Hausa​ anyi hira da Babban Kwamandan Hisbah na Kano Mal.Aminu Ibrahim Daurawa​ inda ya nuna cewar wannan mutum da ya zagi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ba dan Tijjaniyyah bane, Malam yace "Dan Iskan Gari" ne kawai, abinda ya bayu ga wasu zuwa ga "kamar" yunkurin bada kariya ga mai laifi. 

Sannan kuma, a Shafin Babban Kwamandan hisba din na Facebook Malam ya danganta wannan lamari kai tsaya da Darikar Tijjaniyya,  har ma yayi kira da mabiyanta su kaurace mata,  wannan ya nuna akwai cin karo da juna tsakanin bayanan guda biyu, bayan a jiya Malam ya ce babu ruwan Tijjaniyyah a wannan magana.

Ko dai ya kasance Malam ba shi ne yake tafiyar da shafinsa na Facebook ba, dan haka ake samun cin karo na bayanansa,  ko kuma maganar da yayi a BBC kuskure yayi, wanda tuni duniya ta riga ta ji. Dan haka, tilas Malam yayi kokarin daidaita bayanansa akan wannan Qadiyya kasancewarsa Babban Kwamandan Hisba na Kano, kuma daya daga cikin Malamai a Kano.

A hannu daya kuma, muna goyon Bayan Matakin da hukumar Hisba ta dauka, wanda zamu taya su da adduah. Sannan kuma, muna kira a garesu  da lallai su tsaya kai da fata wajen ganin ba a shatale wannan Shari'ah ta hanyar mai da wannan mutum Dan Iskan Gari ba, ko a nuna subul da baka yayi koma ace ba a cikin hayyacinsa yayi maganar ba, wanda hakan na iya bashi damar Kubuta daga fuskantar hukunci.

Haka kuma, muna sane da cewar kwanakin baya a cikin Darikar Tijjaniyya aka samu wani mawaki da yayi kalamai na Shirka, ya sanyawa Allah kishiya wanda ta janyo har sai da Khalifa Isyaku Rabi'u ya barrantar da kansu da kalamwn wannan mawaki, aka ce mana an mika shi hannun hukuma dan yi masa Shari'ah, labarin da har ya zuwa yanzu bamu san inda aka kwana ba. To amma wallahi wannan ba zamu bari ba, zamu bibiya har sai an masa hukunci. Idan kuma hukuma ta kasa yi masa hukunci to su sani ba gata sukai masa ba, akwai Masoya Manzon Allah SAW na gaskiya a Kano suna nan suna kallon motsinsa. 

Yasir Ramadan Gwale 
20-05-2015 

Asalin Wadan Da Suka Assasa Zagin Manzon Allah A Najeriya?


WAYE YA ASSASA ZAGIN ALLAH DA MANZONSA A NIGERIA?

An dade ana shiga hakkin al'ummar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam a Najeriya, sannan a take hakkin masoyan Allah da ManzonSa na gaskiya da sunan sufanci to ya zuwa yanzu tura ta gama kaiwa Bango, ina amfani rayuwu idan har za a tab'a mutuncin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam a garin Kano da sunan Maulidi, wanda tun usuli ce mana akai Maulidin Manzon Allah ake yi, me ya kutso da assasa Maulidin Shehu idan ana batun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam? 

Dama tuntuni Malamanmu sun sha gaya mana, kuma mun karanta, mun gani, wannan shi ne hakikanin manufarsu, ita ce su rushe addini su yiwa Allah da ManzonSa kishiya. Mutanenan ba muslinci suka nufa ba, banda fasikanci da iskanci ba abin da suke yi, Sallah bata damesu ba, su nemi Maza su nemi mata su ci haram su yi dukkan wani nau'I na iskanci yadda ransu yake so, sannan a fake da cewa "mune masoya Sayyaduna Rasulullahi"  mun sanI,  kuma muna da labarin abin da wasu manya manyan Shehunai suke yi a cikin garin Kano da sunan dari'kun Sufaye, Allah ya tsinewa duk wanda ya kishiyi Allah ko ManzonSa, Allah ya turmuza hancin masu ZaginSa Sallallahu Alaihi Wa Sallam da Sahabbansa da ahalin gidan sa.

A cikin liattafin: Jawahi’ur Rasa’il na Sheikh Ibrahim Inyas shafi na [16] Kaulaha yake cewa: "ku sani cewa Allah ya koro duniya a wannan zamani har ta nufi halaka, ba kuma wanda zai kubuta daga wannan halaka sai wanda Allah ya azurta da son shehu Ahmadu Tijjani", shehu Tijjani yana cewa: "hakika 'yan Tijjaniyyah  suna da wata martaba wacce takai matuka wajen daukaka, martabar da haramun ne a fadeta, ko a yayata ta, da zan gaya muku wannan martaba da mabiya gaskiya da ma’abota ilimi malamai na Allah sun yi ijma’i a kan a kashe ni, ballantana kuma gama garin mutane" wannan magana tana nan a cikin wannan littafi nasu.

To yanzu dan Allah wannan wace martaba ce idan ba SHIRKA  ba, da rashin ganin girman Allah da ManzonSa Sallallahu Alaihi Wa Sallam,  wannan shi ne abin da Babban Dagutu ya koya musu, wato Ibn Arabi Al Sufi. In sha Allah nan gaba zan kawo tarihin sa. To irin wadannan maganganu fa sune suka assasa zagin Allah da ManzonSa a Najeriya.

Kuma ina mamaki da mutanan da zasu baiwa kansu sunan masoya Sayaduna Rasulullahi a kano, yau a ce sati daya kenan da faruwar wannan abu amma wai har yanzu mutuminnan yana nan araye, ai yakamata a ce tuni anyi layya da shi kamar yadda aka yi layya da Malaminsa Hallaj, wanda shima Hallaj in sha Allah zan kawo tarihin sa,  amma muna nan muna jira mu ji wane irin hukunci kotu zata yanke a kan wannan zindikin.

Bayan haka kuma, ba zamu taba yadda da duk wani yunkuri na baiwa wannan mutumin kariya ba, wai ace mana "DAN ISKAN GARI NE" kamar yadda abin takaici jiya wani Malami a BBC yake kokarin wanke mutumin da  nuna wai dan iska ne ba da yawun kowacce darika yayi wannan farucin ba. Wannan fa shi ne irin abin nan da Turawa suke yi dan baiwa mai laifi kariya,  idan ya aikata laifin da zai fuskanci hukunci mai tsanani sai su ce "ai dan iska ne ba a hayyacinsa yake ba" shi kenan sai kaji batun ya bi ruwa.

Masu wannan Aqidah  to ku sani wallahi asirinku ya gama tonuwa domin fassarar littafin Ubudiyyah na IbnTaimiyyah ya kusa fitowa cikin harshen Hausa wanda babban Malamin mu Dr. Muhd Sani Umar R/lemo​ ya rubuta, bawani sharriniku wanda kuka rubuta a cikin littattafanku wanda ba a yi bayanisa ba, kowa zai karanta ya gani, al'aurarku ta fito fili.

Yasir Ramadan Gwale 
20-05-2015

Monday, May 18, 2015

Barranta Daga Wannan Mutumin Da Ya Zagi Manzon Allah SAW Kadai Ba Zai Wadatar Ba


BARRANTA DAGA WANNAN MUTUMIN DA YA ZAGI MANZON ALLAH SAW KADAI BA ZAI WADATAR BA 

Idan har wani wanda ba Musulmi ba zai zagi Manzon Allah ko ya zana hotonsa, hankalin al'ummah ya tashi, a farwa wadan da basu san hawa ba basu san sauka ba, da sunan nuna bayar da kariya ga Manzon Allah SAW. Wannan shi ne lokaci mafi dacewa da al'ummar Musulmi a Najeriya ya kamata su misali akan Musulmin da ya zagi Manzon Allah SAW, domin isar da sako ga wadan da ba Musulmi ba da suke tunanin taba mutuntakar Manzon Allah SAW, mu nuna misali akan wannan Zindiki ta hanyar aiwatar da hukuncin da Shariah ta tanada. Wallahi martaba da kimar Manzon Allah tafi duniya da abinda ke cikinta. Zartarwa da wannan Mushrikin hukunci shi ne, zai nuna misali ga cikakkiyar soyayyar da muke ga Manzon Allah SAW.

Wajibin hukumomi ne a Kano su dauki mataki akan wannan mutumin da wadan da suka shirya Maulidin da akai wannan cin mutuncin. Dan uwa Malam Hamisu Nasidi Baban Auwaab, Allah ya saka maka da alheri bisa wannan mataki da ka dauka, hakan ne kuma ya kamaci dukkaninmu, wajen nuna tsantsar soyayya ga Fiyayyen halitta. Sahabbansa, Sallallahu Alaihi Wasallam, sun bayar da dukkan abinda suka mallaka da rayuwarsu saboda shi, sukai mana tsuwurwurin wannan addini har ya kawo garemu.

Dan haka wajibi ne mu tsaya kai da fata wajen ganin an hukunta duk wani mara kunya da yake zaton zai iya taba martabar Manzon Allah SAW ya kwana lafiya. Amma abin mamaki, wasu ko san daga maganar basa son ayi.

Anan a Kano fa wani dan siyasa yace da Malamai da 'yan wasan kwaikwayo duk daya suke wajen koyar da tarbiyya, Malamai suka raja'a akansa akai ta hudubobi akan wannan mutum, sabida an taba mutuntakarsu. To yau gashi, an wayi gari an taba Martabar Manzon Allah SAW, amma wasu na shayin magana akai, sai malamai kalilan suka maida martani akan wannan zindikin.

Wannan batu ba wai kawai a fito ace an barranata daga abinda wannan dan iska ya fada ba shi kenan magana ta lafa, tilas a kaishi gaban alkali ayi masa hukuncin da Shariah ta tanada ga duk wanda ya taba mutuncin Manzon Allah SAW. Allah ka yi dadin tsira a gareshi, Salallallahu Alaihi Wasallam.

Yasir Ramadan Gwale
17-05-2015

Sunday, May 17, 2015

Allah Ka La'anci Wanda Ya Taba Martabar ManzonKa SAW


MARTABAR MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM 

Ya Allah muna rokonka da sunayan ka tsarkaka madaukaka,  Ya Allah kaine kace ku roke ni zan amsa muku! Ya Allah ina me kaskantar da kai a gareka, Ya Allah Kada ka kama mu da laifin da wawayen cikinmu suka aikata musamman na zagi da aibata ManzonKa Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Ya Allah kayi dadin tsira a gareshi da Sahabbansa da Alayensa, Alu Aqeel, Alu Abbas, Alu Jaafar da Alu Alee. Ya Allah an cutar da mu da aibata ManzonKa Sallallahu Alaihi Wa Sallam, Ya Allah ka nuna mana misalin kudurarka akan wadannan batattu. Ya Allah ka gwada musu darajar Annabinka tafi duniya da abinda ke cikinta. Ya Allah ka watsa aniyarsu, Ya Allah Kada ka basu dacewa da sabati a cikin dukkan lamuransu na rayuwa. Ya Allah ka faranta mana Rai da saukar musu da masifar da tashin hankali akan abinda suka aikata na zagin AnnabinKa,  fiyayyan Halitta Baban Fatima kakan Hassan Da Hussain Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Bi Abi Anta Wa Ummi Ya Rasulullah! 

Yasir Ramadan Gwale 
17-05-2015

Saturday, May 16, 2015

Gaisawar Buhari Da Mace Ya Jan yo Cecekuce


YANZU DAN BUHARI YA GAISA DA MACE SAI ABINDA YA ZAMA LABARI? 

Gaskiya ni banga wani abin yamadidi da GMB ba akan wannan Musabiha din ba. Domin ai ba wannan ne karon farko da aka taba ganinsa ya gaisa da mace ba. Amma me yasa sai a wannan ne mutane zasu yi ta yada hoton?

Gaisawa da mace laifi ne a Musulunci to amma, idan har GMB yayi hakan to laifin tsakaninsa ne da mahaliccinsa. Bai kamata mutane su shagaltu da bayyana laifin wani ba, alhali su sun take nasu. Babu wanda zai shiga tsakanin Allah da bawansa.

Ya kamata al'umma su shagaltu da tattauna abubuwa masu muhimmanci da zasu janyowa rayuwarsu da ta 'ya 'yansu cigaba, ba tattauna akan wani abu da mutum ba zai iya dakatar da shi ba.

Buhari ya aikata laifi, shin me yasa mutane ba zasu sameshi sui masa Nasiha ba. Kamar yadda da dama suka kalubalanci Sheikh Gumi akan me yasa ba zai yiwa GMB nasiha shi da shi ba.

Har ga Allah abin na bani mamaki yadda naga mutane sun baiwa wannan musabiha muhimmanci wajen tattaunawa bayan ga abubuwa muhimmai, da ya kamata ayi muhawarori domin samun mafita daga halin da ake ciki.

Kuna kallo aka zagi Manzon Allah aka keta alfarmar Musuluncin da muke tut iya da shi a cikin garin kano mutane basu dauki wannan a bakin komai ba sai gaisawar GMB da mace?

Alfarmar Manzon Allah fa aka taba! Aka Zage shi, amma jama'a basu kalli wannan a matsayin abinda zasu bada lokacin su ba sai batun laifin da wani ya aikata tsakanin sa da mahaliccinsa? BI ABI A TA WA UMAR YA RASULULLAH. 

Yasir Ramadan Gwale 
16-05-2015

TUNATARWA: Tsakanin Masu Zana Hoton Manzon Allah SAW DA Masu Zaginsa



TUNATARWA: TSAKANIN MASU ZANA HOTON MANZON ALLAH SAW DA MASU ZAGINSA KARARA 

A facebook din nan naga ana yada hoton wani mutum Bature, ana tsine masa tare da la'antarsa da kwashe masa Albarka. Ance mutumin yayi alkawarin yin Zane Zane na hotunan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, abin mamaki da tashin hankali da takaici. Shi ne, Musulmi a cikin garin Kano, ya fito bainar Jama'a ya kama sunan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam karara yace WALLAHI SAI SUN TAKA AKE MUHAMMAD! Wal Iyazubillah. Allahumma ajirni fi musibati......! Amma kalli yadda akai gum akan wadannan mushrikai zindikai makiyan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam na hakika.

Ya jama ya kamata mu fadaka, mu sani cewa wadannan mutanafa abin nasu ya wuce duk yadda muke zato, munufarsu shine ruguje addini, domin addinin ba shine a gabansu ba, ba sa ganin girman Manzon Allah (SAW) kai Allah ma ba ganin girmansa suke yi ba, mu kuma musulmi bamu da wanda ya kai Manzon Allah, idan wasu kafirai sunyi zane ko sun fadi wata mummunar magana game da Manzon Allah hankalin duniya zai tashi ayi kone-kone a kasashe da dama saboda kare martabar Annabi (SAW) wadanda Allah dama ya gaya mana a cikin Kur'ani cewa zamu dinga jin irin wadannan maganganu daga wajensu, sai mu yi hakuri, to ya za a yi yau kuma a ce wai wasu wadanda ake cewa wai suna da alaka da muslinci su zasu dinga cin zarafin Manzon Allah a cikin garin kano kuma shuwagabanninmu na addini suna gani, kawai saidai a bar malamai da magana. Allah ya Ubangiji ka tsinewa duk wanda ya assasa wannan mauludin na Ibrahim inyas wadan aka ci zarafin Annabi (SAW) a cikinsa. 

Lallai muna kira da babbar murya ga Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin Babban Limamin Kandahar Sheikh Abubakar Rijiyar Lemo da babban kwamandan hisbah na Kano Mal.Aminu Ibrahim Daurawa da Gwamnatin Kano, akan lallai su yi bincike akan wadan da suka shirya wannan cin mutunci ga fiyayyan Halitta, a kamasu ayi musu hukunci dan hakan ya zama darasi ga duk wani dan iska dake shirin irin wannan magana anan gaba.

Sannan wannan mawakan da suke fkewa da yabon Shehu suna yin I zai lancing ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, lallai ne hukuma ta hana wannan. Yana daga cikin wajibin hukuma, karewa al'umma addini da mutunci da hankali da dukiyoyinsu. 

Kuma In sha Allah zamu mai da hankali a kan bayanin shugabannin bata na duniya wadanda suka dora wadannan mutane a kan wannan mummunar akida ta raina Allah da Manzonsa Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Yasir Ramadan Gwale 
16-05-2015

Wednesday, May 13, 2015

Shugabannin Afurka Basa Daukar Izna Aga Takwarorinsu


SHUGWBWNNIN AFURKA BASU DAUKA INA DAGA TAKWARORINSU 

Tsohon Shugaban Nijar Tandja Mahamdou yayi kokarin karya tsarin Mulki yayi wa'adi na uku, amma hakarsu bata cimma ruwa ba, duk kuwa da yadda ya dinga cika baki da alfahari da fariya. Amma sojojin suka kawo karshen wannan fata da cika baki nasa.

Haka ya faru a Kwadebuwa inda Laurent Gbagbo shima ya kasa samun darasi, yayi gaban kansa domin tabbatar da kansa a matsayin Shugaban da jama'a suka gaji da shi, karshe shima yaji kunya da babu wani shugaba da aka taba wulakantawa kamarsa. 

Irin haka ce ta sake faruwa a Burkina Fasso inda Blaise Campore shima yayi kokarin, yin kunne uwar shegu da bijirewa  tsarin mulki domin tabbatar da kansa a kan mulki, shima karshe aka kunya ta shi, sojojin suka kawo karshen wannan fata nasa.

Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo shima yayi kokarin karya kundin tsarin Mulki domin bin wannan sawu na shugabanni  masu kunne kashi, amma a karshe ya hadu da tirjiyar 'yan siyasa tun ba'aje ko ina ba.

Yanzu kuma sai ga Shugaban Burundi wanda abin takaici yana da tarihin kwantanta gaskiya da yin mulki na adalci, amma karshe ya bata rawara da tsalle ba tare da ya dauki wani darasi daga magabatan shugabanni Afurka ba.

Duk da irin wannan tirjiya da ake nunawa shugabanni a Africa amma har yanzu akwai masu fatan dawwamar da kansu akan karagar mulki. Shugabanni irinsu Umar Hassan Albashir (Sudan) da Paul Biya  (Cameroon) da Robert Mugabe  (Zimbabwe) da sauransu har yanzu basa ganin abinda ke faru balle su dauki darasi daga takwarorinsu. 

Me yasa Shugabanni a Afrika ke san dawwamar da kansu a mulki duk kuwa da suna Ikirarin Demokaradiyya? 

Yasir Ramadan Gwale 
13-05-2015 

Monday, May 11, 2015

Gwamnatin Kano Zata Fara Da Kama Karya


SABUWAR GWAMNATIN KANO ZATA FARA DA KAMA KARYA

Labarin da yake fitowa daga Kano na nuna cewar an kame tare da garkame wani matashi Sanusi Bature Dawakintofa sabida ya bayyana ra'ayinsa a an abinda sabuwar Gwamnati ta yi. Wannan bawan Allah fa dan asalin karamar hukumar Dawakintofa ne, karamar hukumar da sabon Gwamnan Kano Ganduje ya fito, amma aka kama shi sabida ya fadi ra'ayinsa na cewar anyi almubazzaranci a kwashi mutane 70 zuwa Umrah da Ganduje yayi bayan da aka ce shi ya ci zabe.

Wannan alamu ne da suke nuna cikakkiyar kama karya da sabuwar Gwamnatin Kano mai zuwa zata yi. Akan me za'a kama Sanusi Bature Dawakintofa dan kawai ya fadi abinda ya sani ko ya gani? Shin wannan yana nuna mana cewar Gwamnatin Kano mai zuwa ba zata iya jure hamayya ba kenan ko me?

Bayan haka muna kallon yadda ake korar 'yan Hisba kawai dan basu zabi Jam'iyar Gwamna ba. Wannan kama karya ce, kuma babu inda zata je, ai 2019 ba tada Nisa. Da Kwankwaso yace idan Ganduje bai yi abinda ya kamata ba zasu canja shi, na dauka siyasa ce ashe ya san kwanan zancen. 

Idan kuwa haka ne, Ganduje ya yaudari mutane, domin muna yi masa kallon mai kamala da dattako sama da Kwankwaso, ashe lokaci zai yi nan kusa da mutanen Kano zasu ce Gwanda Kwankwaso sau dubu da Ganduje? Ayi dai mu gani. 

Yasir Ramadan Gwale 
11-05-2015

Sunday, May 10, 2015

Jan Layi


JAN LAYIN 

Ban sani ba ko wannan magana ta tabbata cewar Shugaban kasa mai jiran gado Muhammadu Buhari​ yace zai ja layi, daga lokacin da ya karbi iko. Amma a bisa ga abinda yake faruwa yana nuna cewar Najeriya ta kama hanyar tsiyacewa  (Bankrupt), dan haka fatanmu ga sabon Shugaban kasa shi ne, Jan layin da za'a yi ya kasance ne daga 1999 zuwa baya, amma duk abinda yayo sama har zuwa 2015, lallai a binkitowa al'umma dukiyoyinsu da aka jide aka azurta kai ba bisa ka'Ida ba. Lallai zai yi matukar kyau idan sabon Shugaban kasa ya kakkafa hukumomin binciken almundahana da almubazzaranci da akai da dukiyar al'umma tun daga 1999 har zuwa 29 ga may in 2015.

Wanda duk suka kwashi kudin kasa  ba bisa ka'Ida ba su dawo da su, sannan ai musu hukunci daidai da abinda dokar kasa ta tanadar.  Nayi Imani duk wanda aka binkita kuma aka sameshi da rubda ciki da dukiyar al'umma kuma aka kwace aka hukunta shi, to wallahi taimakon sa akai, domin idan ya tsallake anan duniya akwai wani bincike a Lahira, kowa zai zo da gwargwadan abinda ya dauka ba na hakkin sa ba.

Fatanmu shi ne a gina kasa da kudin kasa, dan Najeriya shima yayi alfahari da kasar sa.  A inganta harkokin Ilimi da noma da kiwo, da sufuri, da wuta lantarki,  da harkokin lafiya, da tsaron kasa. A cusa kishin kasa a zukatan al'umma, a sanya mutane kiyaye bin doka da ka'Ida.  Dan kasuwa yayi kasuwancinsa cikin gaskiya da tsoron Allah, wanda yayi algus ko yayi ha'inci ko yayi yaudara ko zamba ko cin amana a hukunta shi bisa tanadi doka.

Ma'aikata su kiyaye amana da aka danka musu, a farfado ko inganta hukumomin kula da d'a'ar ma'aikata. Kowanne ma'akaci a ko ina yake yaji cewar wajibin sa ne ya hidimtawa kasa, ya kare Martabar kasar sa.  A tarbiyyantar da ma'aikata akan tausayi da jin kai da kula da mutuntakar al'umma.

Al'umma kowa yaji cewa kasar sa na alfahari da shi, shima yana alfahari da kasar sa. Sau da dama, nakan ga wasu kasashen na mutunta tutar kasarsu akan tutar jam'iya,  amma mu a wajenmu tutar jam'iya tafi ta kasa muhimmanci, akan cire tutar jam'iya sai kaga ana ta kai ruwa rana da mutane, amma sunyi ko in kula da tutar Najeriya.

Allah ya sa mu shiga wannan sabon zubin Shugabanci a sa'a. 'Yan Najeriya su kasance mutanan kirki a idon kasashen duniya ba da anga dan Najeriya a fara tunanin rashin gaskiya ko cewa ga wani mazambaci ba. Sunan Najeriya da 'yan Najeriya yayi matukar baci a kasashe da dama, inda har takai matsayin da 'yan Najeriya sun gwammace suyi amfani da fasfunan  wasu kasashen da basu kai Najeriya ba, domin gudun tozartawa ko wulakantawa. 

Hakki ne da ya rata ya a wuya duk dan Najeriya kokarin dawo da Martabar sunan Najeriya, kamar yadda Marigayi tsohon Shugaban kasa Umaru YarAdua ya so aiwatar wa,  Allah bai bashi dama mai yawa ba. Allah ka taimaki kasarmu ka bamu Nasara da karuwar arziki da cigaba mai dorawa. 

Yasir Ramadan Gwale 
10-05-2015 

Saturday, May 9, 2015

Kotu Ta Yanke wa Hosny Mubarack Hukunci


SHARI'A SAI MISRAWA

Kotu yau a Masar ta samu Tsohon hambararren Shugaban Masar Hosny  Mubarack da 'ya 'ya sa biyu Alaa da Gamal da almubazzaranci da kudi kimanin  Dollar Miliyan 18, ta kuma yanke musu hukuncin daurin shekaru uku, ta kuma ce hukuncin zai faro ne tun daga 2011 lokacin da Mubarak ya bar Mulki, dan haka tuni ya gama wa'adinsa na wannan hukunci. A sakamakon haka Kotu ta sallami Mubarack ya koma gida shi da 'ya 'yansa a wannan Shari'ah. Yanzu dai zamu ga yadda Mubarack zai tashi daga kan gado yayi tafiya da kafar sa. 

A hannu guda kuma tsohon zababben  Shugaba MuhammadMursi da aka hambare na can a gidan sarka WAI ana zargin sa da kisan masu zanga zanga guda uku. Ai maka juyin Mulki bisa zalinci sannan a kama ka a daure, a kakaba maka laifin da baka aikata ba. Tab!

 Amma abinda suka manta shi ne, a Lahira ma akwai  wata Shari'ah. Allah ya fada duk wadan da aka zalunta sai ya saka masa, da yawa ba zasu taba fahimtar zancen Allah gaskiya bane, sai ranar da Allah ya kira da kansa Ranar tonan asiri. Ranar da Lauyoyi da Alkalan Bogi su kansu ta kansu suke yi. Allah ya kyauta karshen mu. 

Yasir Ramadan Gwale 
09-05-2015 

Wednesday, May 6, 2015

Talaitaccen Tarihin Imam Ahmad Bin Hambal


IMAM AHMAD BIN HAMBAL (IMAMU AHLUSSUNNAH)

Imam Ahmad asalin sunansa Shi ne: Ahmad bin Muhammad Bin Hanbal Bin Hilal Bin Asad, Ash-shaibani, Al-marwazi, Abu Abdullah. An haifi Imam Ahmad a shekara ta (164A.H), a Birnin Baghdad na Iraqi, ya kasance daya daga cikin manya-manyan malaman duniya, malami ne wanda ya hada ilimi da tsoran Allah da kuma aiki da abin da ya sani na gaskiya.

Wani Malami Ibrahim alharbi a zamanin yake cewa, ban taba ganin mutumin da Allah ya tara masa il...imin mutanan farko da na karshe ba kamar Imam Ahmad, ana yi masa lakabi da imam Ahlussunnah saboda jajircewarsa da tsananin riko da Sunnah lokacin fitinar: cewa kur'ani makhluq ne, wanda imam Ahmad ya tsaya a kan cewa kur’ani zancen Allah ne kuma ba makhluq ba ne.

Imam kutaiba yana cewa: mafi alkhairin mutane a zamaninmu shine: Ibn Mubarak sannan wannan saurayin, wato Imam Ahmad bin Hanbal, idan ka ga mutum yana son imam Ahmad to ka tabbatar cewa wannan mutumin Ahlussunnah ne. Imam Ahmad ya rasu a shekara ta (241A.H).


Yasir Ramadan Gwale 
06-05-2015

Takaitaccen Tarihin Imam Shafi'ee



IMAM MUHAMMAD ASH-SHAFI'E

Imam Ash-shafi’e asalin sunansa shi ne: Muhammad Bin Idris Bin Abbas Bin Usman Bin Shafi’e; Abu Abdullah, Ash-shafi’e, Al-qurashi, Al-makki, nasabarsa tana tukewa zuwa ga Lu’ayyu Bin Galib, wato kakannin Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wa Sallam ). 

An haifi Imam Ash-shafi’e a shekarata (150A.H) a garin Makkah, mahaifinsa ya rasu tun yana yaro karami, don haka ya taso ka...rkashin kulawar mahaifiyarsa ne. Imam Shaffi'e ya fara neman ilimi tun yana yaro, ya fara da karatun harshen larabci da kuma wake-waken larabawa har ya tumbatsa a cikin wannan fanni, sannan ya fuskanci karatun fiqihu har ya zamanto jagora a zamaninsa.

Imam Ash-shafi’e ya karanta littafin Muwadda a wajen Imam Malik, ya kuma yi wallafe-wallafe na littattafai da dama, daga cikin mafi shaharar littattafansa akwai: Ar-Risala, da Al-Um, da Al-Musnad, da kuma As-Sunan. 

Imam Ash-shafi’e yana cewa: neman ilimi ya fi sallar nifila, duk wanda ya koyi qur’ani matsayinsa zai daukaka, duk wanda ya karanta hadisi hujjarsa zata yi karfi, duk wanda bai kame kansa ba daga sabon Allah to iliminsa bai masa amfani ba. Imam Ash-shafi’e ya rasu a shekarata (204A.H).

Yasir Ramadan Gwale 
04-05-2015

Saturday, May 2, 2015

Takaitacce Tarihin Imam Malik Bin Anas


IMAM MALIK BIN ANAS (IMAMU DARUL HIJRAH)

Imam Malik asalin sunansa shi ne: Malik Bin Anas Bin Malik Bin Abi Amir, Abu Abdullah, Al-asbuhi, Al-madani, Imam Darul hijra, Hujjatul Islam, an haifi Imam Malik a shekara ta (93A.H) a Madina.

Imamu Malik ya fara neman ilimi tun yana yaro karami, Allah ya yi masa kafin basira da fahimta cikin sauki, Imam Malik ya bunkasa tun yana karami, ya kai matsayin mai yin fatawa,  ya fara yin fatawa tun yana dan shekara ishirin. 

Abu Huraira Radiyallahu Anhu, ya rawaito hadisi daga Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam, yana  cewa, Annabi  ya ce: Zamani ya kusa  zuwa da mutane zasu niki gari wajen tafiya neman ilimi, amma ba za su samu Malami ba kamar malamin Madina.

Sufyan bin Uyaina ya ce: ina garin wannan Malami da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya yi ishara da shi, shi ne Imamu Malik Ibn Anas, imam Malik bai rubuta wani littafi ba face fita ce littafin nan da ya shahara da shi wato Muwadda. Imamu Malik ya rasu a shekara ta (179A.H).

Yasir Ramadan Gwale 
02-05-2015

Friday, May 1, 2015

Takaitaccen Tarihin Imam Abu Hanifa Rahimahullah


IMAM ABU HANIFA

Imam Abu Hanifa asalin sunan sa shi ne: An-Nu’uman bin Thabit, At-Taimi, Al-Kufi, an haife shi a shekara ta (80A.H) a birnin kufa na kasar Iraqi ya hadu da wasu daga cikin sahabbai kamar Anas bin Malik, amma ana cewa ba shi da riwaya ko daya daga sahabi. 

Imam Abu Hanifa daya ne daga cikin manya-manyan Malaman Muslinci, wanda sukaiwa addini Allan hidama, kuma al'muma ta amfana da tarin ilimi sa,  Allah ya ba shi tarin ilimi da yawan ibada, ana cewa yana saukar kur’ani duk dare. 

Abu Hanifa yana cewa: wata rana na yi mafarki wanda ya razana ni, na yi mafarki kamar gani ina tono kabarin Annabi (SAW) sai na tafi Basra na sa wani mutum ya tambayar min Ibn Sirin ma’anar wannan mafarki, sai Ibn Sirin ya ce: wannan mutumin zai dinga tono hadisan Annabi (SAW). 

Yahya bin Ma’in yana cewa: Imam Abu Hanifa thiqa ne, ba ya rawaito hadisi sai wanda ya haddace, ba ya rawaito hadisin da be haddace ba. Imam Abu Hanifa ya rasu a shekarata (150A.H). 

Yasir Ramadan Gwale 
01-05-2015