Kabarin Shugaban
Kasa!
A lokacin da marigayi shugaban kasa malam Umaru Musa ‘YarAdua yake
da rai, yana yawan kai ziyara makabartar wali dan marina a jihar katsina. Yana zuwa
wannan makwantai domin ziyara ga kushewar mahaifinsa da kuma dan uwansa;
marigayi ‘YarAdua ya taba tambayar mai gadin makabartar cewa, “kana da da
tabbacin idan na mutu zan samu waje a wannan makabartar, musamman kusa da
mahaifina da kuma dan uwana? Sai mai gadin ya mayar da tambaya zuwa ga marigayi
‘YarAdua, ranka ya dade me kake nufi? Sai ‘YarAdua ya ce masa na lura da sabbin
mutanen da ake biznewa suna yawa, sannan mai gadin makabartar ya amsa masa da
cewar Insha ALLAH bazaka rasa waje ba a wannan makabarta. ALLAH cikin ikonsa
mai aukuwa ta auku ga ‘YarAdua, kuma burin da yayi na samu makwanci a cikin
wannan makabarta ALLAH ya cika masa, muna addu’ar ALLAh ya jikansa da rahama.
Dukkaninmu
munyi imani da cewa akwai rata mai yawa tsakanin fadar shugaban kasa da kuma
gidan talaka. Wannan kusan zaka iya cewa rata ce da tsakanin yana da yawan
gaske, domin fadar shugaban kasa wajene da aka tsarashi na musamman, ba dan
komai ba, sai domin amfanin rayuwar duniya da jin dadi da morewa. Amma kuma
babu wanda yake shakkar cewa da kabarin shugaban kasa da kabarin almajirin da ya
mutu a hanya da bashi da ko damar shiga gidan haya daya suke, yadda aka sanya
shugaban kasa a cikin rami, aka nade gawarsa da farin kyalle haka za’ayiwa
wannan talaka, wannan ya nuna dangantakarmu daya ce da masu mulki.
Alhamdulillah! kamar yadda addinin musulunci ya tanada idan musulmi ya rasu
gaggawa akeyi a binneshi ba sai an bata wani lokaci ba. Wannan ya tunamin da
wani baiti da MARAYA Jos yake cewa:
“Kai mai akwai ka gane, In baka ɗan
misali, Ranar komuwa ga Allah
Yadi biyar fari ɗai, A ciki za a nannaɗe ka, Rami guda a kan tona
Ka tuna ba a tona goma, Don wai kana da hali, Ciki za a turbuɗa ka
Haka nan wanda bai da kome, Ran komuwa ga Allah, Yadi biyar fari ɗai
Ciki za a nannaɗe shi, Rami guda a kan tona, Ka tuna ba a tona goma
Don wai fa bai da kome, To malam idan ka duba, Tanan haka dangantakar ku daidai”.
Yadi biyar fari ɗai, A ciki za a nannaɗe ka, Rami guda a kan tona
Ka tuna ba a tona goma, Don wai kana da hali, Ciki za a turbuɗa ka
Haka nan wanda bai da kome, Ran komuwa ga Allah, Yadi biyar fari ɗai
Ciki za a nannaɗe shi, Rami guda a kan tona, Ka tuna ba a tona goma
Don wai fa bai da kome, To malam idan ka duba, Tanan haka dangantakar ku daidai”.
Marigayi
tsohon Shugaban kasa mallam Umaru ‘YarAdua, ya sha fama da jinya kafin ALLAH ya
karbi rayuwarsa. A cikin hadisin da
Bukhari ya fitar da shi manzon ALLAH sallalahu Alaihi wasallam yana cewa ALLAH
yana kankare zunuban bawan da aka jarrabeshi da cuta kafin rasuwarsa, Shuagab
YarAdua yayi sa’a, domin ya shiga cikin sahun mutanan da za’a kankaremusu
zunubansu sakamakon tsananin rashin lafiya da aka jarrabeshi da ita. Allah mai
girma da dauka ya fada a cikin littafinsa mai tsarki Al-kur’ani a cikin sura ta
3 aya ta 185 cewa ‘Lallaine tabbas kowace RAI zata dandani mutuwa’ shugaban
kasa dai ya riga ya dandana tasa.
Fadar shugaban kasa nanne wajen da yafi ko ina
samun tsaro da kariya a duk fadin Najeriya, amma wannan tsaro bai iya hana mala’ikan
mutuwa shiga wannan fadar ba wajan dauko ran shugaban kasa ya fito salin’alin.
Allah Akbar! Haka nan, mala’ikan mutuwa ya shiga wannan fada ya dauko ran
magabacin YarAdua, marigayi Gen Sani Abacha, ba tare da ya fuskanci wata barazana
ko tirjiya daga dukkan jami’an tsaron da ke wannan fadar ba, ALLAH kenan mai
yadda ya so, duk kauna da soyayya da kariya da ake baiwa masu mulki ashe bata
da wani amfani tunda bazata iya hana mala’ikan mutuwa shiga duk inda yaga dama
ba, lallai ne kowace RAI bazata mutu ba sai ta cika ajalinta.
Dan
haka, duk wanda ya fahimci manufar wannan rayuwa kuma ya kalli karshenmu gabaki
daya, sai ya samu natsuwa a cikin zuciyarsa, ya san cewar ALLAH baya barci yana
nan yana kallon kowa. Kuma, kowa zai tafi da ayyukan da ya aikata ne, idan Alheri
ka aikata wallahi babu abinda zaka gani sai alheri, hakama idan sharri ka
aikata babu abinda zaka gani sai shi, ALLAH shi da kansa ya haramta zalinci
akansa, ballanatana danAdam. Munyi imani da cewa dukkan wani tsanani akwai
rahama a karshensa, fatanmu shine ALLAH ka sanya karshenmu yayi kyau, halin da
muke ciki ALLAH ka sayaya mana, ALLAH ka sa can tafi nan.
Yasir
Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment