Sunday, October 7, 2012

ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (4)



ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (4)

Kasashen yammacin turai karkashin jagorancin Amerika basu damu da duk wani jini da zai zuba ba indai bukata zata biya, matukar jinin ba na Amerikawa bane ko na turawa ja-ja-yen fata ba. Babbar manufar ‘yan jari hujja ita ce shigar da kwadayi da hadama da babakere akan kimar haja tun kafin lokacin amfaninta ya zo, dan haka tsarin jari hujja ya ginu ne akan cin gwagwgwabar riba a harkar kasuwanci, ‘yan jari hujja zasu iya baiwa ko wace haja irin kimar da bata da ita, kuma jama’a su raja’a akanta abinda Karl Max ya korawo da sunan ‘Tsatsube’ bisa wannan ka’idar ‘yan jari hujja zasu iya maida kimar Ruwa ta fi ta Zinariya ko Tagulla.

Idan muka koma yankin tafkin caspean zamu ga cewar bayanai sun tabbatar da cewar akwai gangar danyan mai a kwance a wannan tafki da ta kai kusan ganga sama da biliyan 49, wannan antabbatar da samuwarta, sannan kuma ana hasashen samun karin wasu ganguna da suka tasamma biliyan 500 zuwa sama. Dan gane kuma da bayanin Iskar gaz da ke wannan yanki, har yazuwa yanzu babu wasu al-kaluma da suka tabbatar da adadinta amma sai dai babu wanda yake shakkar cewar yankin yana tattare da iskar gaz mai dankaren yawan tsiya, sai dai daga lokaci zuwa lokaci kasashen da suke kewaye da wannan yanki sukan fitar da alkaluman da suke ganowa na dimbin makamashin da yake yankin, kasashen sun hada da Rasha da Iran da Azarbaijan da Turkministan da kuma Kazakstan.

A shekarar 2011 ma’aikatar mai ta Iran ta bayyana gano makamashin iskar gas dake bangarenta da ya kai cubec mitre tiriliyan daya a gabar ruwanta. A cikin watan oktoban shekarar 2011 kamfanin mai na TOTAL ya bayyana gano iskar gaz a gabar ruwan kasar Azarbaijan da ta kai cubec mitre biliyan 350, sannan kuma a cikin filin Talotan na kasar Turkumistan an bayyana gano makamashin Iskar gaz da ya kai Tiriliyan 21.1 a ma’aunin cubec mita, kasashe guda biyu kawai Kazakstan da Turkministan suna da dimbin makamashin iskar gaz a gabar ruwansu da ya kai kimar dalar Amurka Tiriliyan 12.

A zamanin rusashshiyar tarayyar sobiya ita da Iran ne kadai suke raba arzikin wannan yanki na caspean dai-dai-wa-dai-da bisa yarjejeniyar da suka kulla tun cikin shekarar 1921 domin sauran kasashen da suke kewaye da wannan yanki na caspean duk suna karkashin tarayyar Sobiya ne a matsayiin jamhuriyoyi. Rushewar da tarayyar sobiya ta yi a 1991 shine abinda ya karfafawa manyan kamfanonin ‘yan jari hujjar Amerika guiwa inda suka fara nuna kulafucinsu a fili akan arzikin da yake wannan yanki. Kamar yadda muka fada a baya cewa sanannen abu ne cewa akwai aure irin na katolika tsakanin gungun kamfanonin ‘yan jari hujjar Amerika da kuma duk wani shugaban Amerika da aka zaba da kuma dukkan manyan jami’an gwamnati masu fada aji.

Babbar matsalar da ba’a warwareta ba shine ta yaya za’a debo arzikin da yake dankare a wannan tafki na caspean zuwa inda ake da tsananin bukatarsa. Dan haka wadannan gungu na Corporate Capitalism na Amerika suka tabbatarwa da kansu cewar mafitar wannan arziki da yake wannan yanki shine a gina hanyar al-hariri wato Silk Road wadda za’a debo wannan arziki zuwa inda ake so, sai dai yin hakan ba abu bane mai sauki domin akwai matukar wahala da hadari tattare da yin hakan, amma kuma romon da yake cikinsa shine yake rinjayarsu.

Ta hanyoyi guda uku ne kadai za’a iya fito da wannan arziki na makamashi zuwa Amerika. Wato kasar Chana tayi iyaka da tafkin caspean ta gabas, sannan kasar Rasha da Iran da Turkiyya sunyi iyaka da shi ta yamma, sai kuma Afghanistan da Pakistan suka yi iyaka da shi ta kudu. Tsarin farko da kamfanin UNOCOL (Wanda Iyalan Bush da Bin laden suke da hannu jari acikinsa) ya fito da shi akan yadda za’a shimfida bututun da zai dauko makamashin kasar Turkuministan, shine za’a shimfida bututun dai zai ratsa ta kasar Afghanistan ya bi ta birnin karachi na Pakistan daga nan kuma ya tuke zuwa ga tekun indiya wato Indian Ocean. Wannan shine kalubale na farko da wannan kamfanin ya zai fuskanta, duba da cewar kasar Afghanistan tana fama da yakin basasa tun bayan ficewar Rasha tsakanin ‘yan Taliban da kuma gamayyar kungiyoyin Norhern Alliance karkashin jagorancin Sha Ahmed mas’ud.

Dan haka wannan kamfani ya yi amfani da wannan damar wajen kutsa kansa cikin yakin basasar Afghanistan dan share hanya ga bututunsa da zai ratsa Afghanistan ba tare da ya fuskanci wata tirjiya ba. Dan haka, a bisa shawarar da jakadan Amerika a Pakistan Robert Oakley ya baiwa wannan kamfani dan haka, kamfanin ya kulla kawance da kungiyar Taliban wadda a wannan lokaci ikon da suke da shi bai wuce birnin Kandahar ba kawai, bisa cikakken hadinkai daga gwamnatin Bill Clinton ta wannan lokaci da kuma taimakon kungiyar leken asiri ta Amurka CIA aka kulla wannan alaqa tsakanin kamfanin da Taliban ta wancan lokacin. A wannan lokacin Osama  Bin Laden yana Afghanistan, dan haka ina mai cike da shakkun sahihanci ko gaskiyar Osama Bin laden cewa ba Amurka ne suka yi amfani da shi domin cimma wannan nufi na su ba, idan mai karatu bai mantaba a baya mun fada cewa shi wannan kamfani Iyalan Bush da Bin Laden suna da hannun jari a cikinsa.

Hikimar kulla wannan kawance tsakanin ‘yan mafiya na makamshi daga Amurka da kungiyar Taliban ta ‘yan takife ya bayyana kamar wata daran goma sha biyar a lokacin da Ted Roll ya rubuta wata kasida a cikin San Francisco Chronicle ta ranar 2 ga watan Nuwamban 2001, wato wata guda kenan bayan harin 11 ga watan satumba a tagwayan cibiyar kasuwancin Amurka, ina fatan mai karatun da yake bina ya alakanta wannan bayanai da suka gabata da kuma harin 11 ga watan satumba, ya gani akwai alaka ko babu! Ga abinda Ted Roll yake cewa “idan ka sami danyan man fetur din da ba’a fara taba shiba, sannan kuma kana da bukatar dibarsa, sai ka kulla yarjejeniya da gwamnatoci masu karfi wadanda suke da kusanci da kamfanonin mai na Amerika. Dan haka tsari mafi dacewa shine a shimfida bututun da zai ratsa Afghanistan ya bi ta karachi har ya bulle bakin gabar ruwan Arebiya, sai dai mutanan Afghanistan sun kasa kafa gwamnati saboda yakin basasar da yake a tsakaninsu. A saboda haka abinda ya kamata ayi shine abinda CIA ta ringa yi na kafa gwamnati mai kawo zaman lafiya ‘a fadarsu’ Gwamnati wacce zata kawo karshen yakin basasa sannan ta bada kariya ga bututan da kamfanin UNOCAL zai shimfida da zai ratsa ta Afghanistan”.

Wani marubuci Stave Coll ya fada a cikin wani littafi da ya rubuta mai suna Ghost War cewa kamfanin mai na Unocal ya taimakawa da kungiyar Taliban da kudaden da makaman da ta yi amfani da su wajen kame birnin kabul daga hannun ‘yan Northern Alliance a cikin shekarar 1996. Shi kuwa Ted Ross ya fada cewa kungiyar taliban ta samu bayanan sirri akan Northen Alliance a hannun CIA tare da kugiyar leken asirin Pakistan. Allah ne kadai yasan adadin mutanan da suka hallaka daga Kandahar zuwa kabul domin baiwa Taliban ikon kafa gwamnati a Afghanistan, a mastayin share fage ga kamfanin Unicol domin safarar arizkin Iskar gaz daga yankin gabas mai nisa zuwa Amerika da sauran kasuwannin duniya.

Bayan da taliban ta samu shekaru biyu da samun gindin zama a Kabul, gwamnatin Amurka ta wancan lokacin ta gayyaci ministocin Afghanistan har Warshington domin tattaunawa. Anyi wata ganawa ta musamman da karamin ministan harkokin wajen Amerika mai kula da kudancin Asiya Karl Inderforth da wadannan ministoci daga Afghanistan, daga cikinsu akwai ministan ma’adanai da masana’antu Ahmed Jan da ministan Al’adu Amr Muttaqi da kuma ministan tsara dabarun ayyukan taliban Deen Muhammad, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da sanarwar wannan ganawar a matsayin wani muhimmin ci-gaba.

Kamar yadda masu iya magana suke cewa yaki dan zamba ne, babban makamin da Amurka ke amfani da shi a karon farko a duk harkar yaki shine kafafan watsa labarai inda take cin mutane da buguzum. Tambaya anan ita ce shin suwaye hakikanin wadanda suka shirya harin 11 ga watan Satumba? Suwa ke da alhakin kai harin? Me ye ya sa Amerika ta shiga Afghanistan da karfin tuwo tun bayan wannan hari?

Mu hadu a muqala ta gaba domin jin wasu bayanai masu sarkakiya dangane da wannan batu.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale






No comments:

Post a Comment