ZABEN AMERIKA:
Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (2)
Siyasar
Amerika tana da fusaka biyu, wato akwai wadda ake yi ta zahiri wadda Amerikawa
suka sani kuma suke bibiyarta, wato siyasar Amerika ta cikin gida wadda ta
shafi Amerikawa. Da yawan Amerikawa gidadawa ne, ta yadda basu san galibi yadda
al’amura ke gudana tsakanin Amerika da sauran kasashen duniya ba. Kamar yadda a
kasar Meseddoniya a kullum tarbiyyar da ake yiwa ‘yan kasar shine daga Allah
sai mesedoniya, haka itama Amerika, kullum tarbiyyar da ake baiwa Amerikawa
shine daga Allah sai Amerika, dan haka ne aka jahiltar da mafiya yawansu akan
abinda ya shafi hakikanin alakar Amerika da sauran kasashen duniya, sannan aka dauke
musu hankali ta hanyar shagaltar da su da abubuwa na more rayuwa da jin dadi.
Wannan ta
sanya kullum Amerikawa basu da wani tunani sai abinda ya shafi aikin yi, jima’i
wanda ya hada da morewa da jin dadi da shakatawa da kuma hutun karshen wata ko
na karshen shekara. Wannan kusan sune suka damu da yawa daga Amerikawa na
zahiri da muke gani, dan haka nema, duk wasu abubuwa na banza da wofi da bata
lokaci sai kaga Amerikawa sun basu muhimmanci, kamar kallon karrama taurarin
fina-finai na Hollywood, kallon namun daji, linkayawa a bakin kogi (beach) da
sauran sharholiya, haka kuma, su Amerikawa wannan shine ya damesu. Dan haka
sukeyiwa sauran kasashe musamman na musulmi wani irin kallo a matsayin na
Abokan gabar Amerika, saboda abinda ake watsa musu a kafafa watsa labarai
kenan.
Kamar
yadda dubban mutane suka kalla a ranar larabar nan da ta gabata 3 ga watan
oktoba, anyi muhawara ta fako tsakanin Obama da Romney. Wadda a wannan muhawara
aka tabo abinda ya shafi siyasar Amerika ta cikin gida. Mista Jim Lehrere na
kafar watsa labarai ta PBS Newshour shine ya jagoranci wannan muhawara da ta
hada Obama da Romney a karon farko a bainar jama’a, wadda abinda aka tabo a
wannan muhawara kusan abubuwa ne da duk wanda yake bibiyar siyasar Amerika ta
zahiri ya sansu, wato batun nan mai cike da kalubale na Tsarin kiwon lafiya na
Obama (health care), da batun makomar tattalin arzikin kasar Amerika anan gaba
(The future of the Economy), da kasafin kudin gwamantin tarayyar Amerika (The
federal Budget), da kuma batun bashin da ya dabaibaye Amerika, wanda Amerika
ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan bashi a duniya (The National Debt) domin
yanzu batun da ake suna da bashin da ya kai Dala Tiriliyan goma sha shida ($16t)
wanda idan ka kwatatanta da na Najeriya da Gej ya ciwo ($45b) bai wuce kudin
shan-shayi ba akan na Amerika.
Haka
kuma, batun da Amerikawa suka fi damu da shi shine abinda ake kira da turanci
DEFICIT wato abinda Amerikawa suke kashewa yana dara abinda suke samu na
albashi, da kuma batun samar da aikin yi yake taka muhimmiyar rawa, yanzu
rashin aikin yi a Ameriaka yakai kashi takawas (Unemployment rate 8%), wanda
kusan shine agaba wajen abinda ya damu Amerikawa. Sannan da wani batu da aka
jima ana yin takaddama da shi tsakanin Obama da Romney shine na batun haraji
akan hamshakan mutane da kuma talakawa (Tax cut). Kusan wadannan a takaice sune
suka mamaye wannan muhawara da akayi a jihar DENVER, sannan za’a cigaba da
wannan muharawa tsakanin ‘yan takarar biyu ranar 16 ga watan Oktoba a jihar New
York wadda zata dora akan abubuwan da aka faro tattaunawa akansu ne, sannan
kuma da muhawara ta karshe wadda za’a yi a ranar 22 ga watan nan na oktoba za’a
karkare wannan muhawara a jihar Florida wadda zata maida hankali akan siyasar
Amerika ta daya bangaren mai cike da sarkakiya wato siyasar Amerika da kasashen
duniya da suke cewa Foriegn Plocy.
Tun bayan
faduwar tsohuwar hadaddiyar tarayyar sobiya (USSR) a shekarar 1991, kasar
Amerika ta samu damar shuka irin abinda ta ga dama da kuma shigewa gaba wajen
yin yadda taga dama da kasashen duniya wanda ake kira UNILATERALISM, a wannan
lokacin Amerika ta yi ta shimfida hanyar da zata mamaye duniya musamman a goman
karshe na karni na 20 wato daga 1991 zuwa 1999. Ta shirya tsaf tare da kammala
shirinta akan mamaye dimbin albarkatun manfetur da ALLAH ya huwacewa yankin
GABAS TA TSAKIYA, domin bayanai sun tabbatar da cewar da akwai gangar danyan
man fetur fiye da ganga Biliyan 350 a kwance a kasar IRAQI wanda ya dara man da
kasar SAUDIYYA take da shi a yankin gabas ta tsakiya, domin bayanai sun
tabbatar da cewar Saudiyya tana da gangar danyan mai da ta kai ganga Biliyan
267. Wannan batu na mamaye albarkatun danyan man da ke yankin gabas ta tsakiya
shine ya sanya Gwamnatin Amerika karkashin George Wolter Bush ta shiga Iraqi da
karfin tuwo a shekarar 2003, inda suka yaudari duniya da cewar marigayi Saddam Hussain
ya mallaki makaman kare dangi. Duk kuwa da cewar hukumar dake kula da makamashin
Nukiliya ta duniya IAEA karkashin Mohammed el-Baradai ta tura tawaga mai karfi
karkashin Hans Blicks wanda suka je sukayi iya kar bincike basu ga komai ba.
Wannan
yunkuri da Amerika take yi na mamaye dumbin arzikin gurbataccen mai da yake
kwance a yankin gabas ta tsakiya shine ya sanya da yawa daga cikin kasashen
gabas ta tsakiya suke cikin halin yaki kusan tun cikin karni na 20 har kawo
yanzu. Kada ka bini bashin rantsuwa domin dukkan wadannan fadace-fadace da
akeyi a yankin gabas ta tsakiya shirayyene daga kasar Amerika domin mamaye
arzikinsu. Tun bayan da Amerika ta shiga Iraqi kuma ta hambarar da marigayi
Saddam Hussein Allah ya jikansa, suka shiga watandar dan yan manfetur din da
yake a kasar domin a karon farko anbaiwa katafaran kamfanin mai na Amerika
Halliburtun ta hanyar reshensa mai suna KELLOG BROWN AND ROOTS kwangilar yashe
tare da tsabtace rijiyoyin manfetur na Iraqi wadanda aka kona, sannan kuma aka
sake baiwa kamfanin kwangilar sake samar da wasu sabbin cibiyoyin kula da
danyan manfetur a Iraqi wanda ya kai kudi wajen dala biliyan 900.
Babbar
alkiblar gwamnatin Bush da ta gabata shine, tana tare da ‘yan Mafiya masu
mamaye duk wata harka da ta shafi makamashi da manfetur. Manuniya akan haka
shine, daya daga cikin manyan kamfanonin mai na ARBUSO wanda shima Iyalan Bush
wato Bush kakan George Bush suke da hannun jari mai karfi a cikinsa, haka kuma
suma Iyalan Bin Laden suna da hannun jari mai gwabi a cikin wannan kamfani,
wadannan hannun jari da wadannan hamshakan Iyalai suka mallaka ita ce ta haifar
da wata alaka tsakaninsu mai cike da rudani, kuma mai cike da sarkakiya da
dabaibayi, domin daga baya anrinka samun rashin jituwa wadda tana harsashe zuwa
ga abinda ya faru na harin 11 ga watan satumba a 2001, domin jaridar The Los
Angels Times ta ranar 8 ga watan fabrairun 2004 ta buga wani labari mai taken “Abubuwan
da iyalan Bush suke dauka da daraja sune, yaki da dukiya da man fetur”.
Dick
Cheny wanda idan bamu manta ba shine ya yiwa George Bush mataimakin shugaban
kasa, shine kusan shugaban wani sashe na katafaren kamfanin nan na Halliburtun
kamar yadda muka fada shahararre ne a Najeriya a harkar manfetur da dangoginsa,
da kuma wasu kasashe da suka hada da na gabas ta tsakiya gaba daya da kuma
kasashen Indonesia da Burma, haka kuma, tsohuwar shugaban hukumar leken asiri
ta kasar Amerika kuma tsohuwar mashawarciya ta fuskar tsaro, har ila yau
tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Amerika lokacin gwamnatin Bush, Dr
Condolizzer Rice ta taba zama shugabar katafaren kamfanin mai na Chevron a
shekarun 1999 zuwa 2000, wanda shima kamfanine na daya daga cikin wadancan
shaidanu na Amerika wadanda sune suke juya duk wani shugaban kasar Amerika ya
so ko bai so ba.
Dan haka
domin wadancan gungu na Corporate Amercan Capitalism su cigaba da mamaye
arzikin manfetur dake yankin gabas ta tsakiya sunyi ta yin amfani da wasu
mutane a matsayin dodorido domin su sami damar yin yadda suke so, domin
gwamnatin Bush ta yi amfani da wasu mutane domin cimma waccan boyayyar manufa
irinsu Iyad Alawi a mastayin sabon shugaban Iraqi tun bayan hambare marigayi
Saddam Hussein Allah ya jikansa, haka harka zo kan mutane irinsu Nuri A-Maliki
da Ibrahim Al-Ja’afari duk wadannan mutane daga Amerika aka daukosu aka basu
mukamai domin su sharewa wadancan shaidanu hanyar mamaye danyan man da yake
kwance a Iraqi.
Mu hadu
a kasida ta gaba.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment