ABINDA YA SHAFI
ABBAS FAGGO YA SHAFEMU
A gobe ne idan
ALLAH ya kaimu Abbas Ahmed faggo zai bayyana a gaban kotu. Idan bamu manta ba,
Gwamnan Bauchi Malam Isa Yuguda da kwamishinan shari’ah na Bauchi suka sanya
aka kame tare da garkame Abbas saboda ya bayyana ra’ayinsa a shafinsa na
facebook akan facaka da almundahana da yace antafka da dukiyar al’ummar jihar Bauchi
a dalilin bikin dan gidan gwamna isa Yuguda. Lauyan dake kare Abbas ya bayyana
cewar a gobe ne za’a gurfanar da wanda
yake karewa a gaban kotu ta uku dake cikin garin Bauchi, kotun tana nan kusa da
gidan Muda Lawal a sabuwar GRA dake cikin garin Bauchi. Dan haka ana kira ga
duk masu rajin kare hakki ko ‘yancin Bil’adama cewa ga ranarsu, lokacin da zasu
nuna kauna da soyayya ga Adalci da daidaito da kuma ALLAH wadai da mulki na
danniya da karya tsarin mulki da dannewa mutane ‘yancin fadin albarkacin
bakinsu. Dan haka ina al’ummar Jihar Bauchi masu son ci gaba, ina kungiyoyin
dalibai masu neman kawo sauyi, ina kungiyoyin sa-kai ana kiranku gobe kuyi
tururuwa zuwa wannan kotu domin yin ALAH wadai da mulki irin na ‘yan
kama-karya, mulkin da yayi kama da na mallaka.
Wannan shari’ah
ta Abbas ba tashi bace shi kadai, abu ne da ya shafi dukkaninmu masu amfani da
kafar sadarwa ta Internet. Dole ayiwa Abbas adalci, domin adalci gareshi adalci
ne ga dukkaninmu. Lokaci yayi da zamu yi tir tare da tofin Alla-tsine ga tsarin
mulkin kama karya irin na su gwamna Isa Yuguda. karni na 21 ba lokacin kama
karya bane, kan mage ya waye. Shugaban kungiyar lauyoyi reshen jihar Bauchi ya
shaidawa Dr Aliyu Tilde cewar zaije wannan kotu tare da wata kakkarfar tawaga
ta lauyoyi domin ganin yadda wannan shar’ah zata gudana.
Manzon ALLAH
Salallahu Alaihi wasallam ya cewa sahabbai ku taimakawa dan uwanku da aka
zalunta, sannan ku taimakawa dan uwanku da yayi zalunci. Sai Sahabbai suka tambayi manzon ALLAH tayaya zamu
taimakawa dan uwanmu da yayi zalunci? Manzon ALLAH ya ce a duk lokacin da wani
dan uwanku yayi laifi idan kuka la’ance shi to kun taimakawa shaidan akansa,
idan kuwa kuka yi kokarin hanashi aikata wannan abinda da yayi to kun taimaka
masa akan shaidan. Dan haka, muna kira ga Gwamna Isa Yuguda yaji tsoron ALLAH
ya sauraremu tun kafin lokaci ya kure masa, tun kafin lokacin da zaiyi da ya
sanin da bazata amfaneshi ba. Kada Isa Yuguda ya manta cewa wani ne ya sauka
daga kan kujerar gwamna sannan ya hau, to haka shima nan gaba zai sauka wani ya
hau. Idan kuwa kaki ji to tabbas bazaka ki gani ba, domin akwai EFCC tana nan
tana jiranka, ka tuna magabatanka irinsu makwabcinka Danjuma Goje da Aliyu Akwe
Doma kaima wannan ranar tana jiranka! Lokacin da zaka ringa cewa inama dai na
saurari koke-koken al’umma da kiraye-kirayensu, zaka yi dana sani nan gaba
kadan kuma nadama ce karshenka Yuguda.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment