ZABEN AMERIKA:
Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (5)
Harin 11 ga watan satumba na 2001 da aka kai tagwayen gine-gine cibiyar
kasuwanci ta duniya a New York cike yake da abin mamaki da kuma
tuhumce-tuhumce. Lokacin da abin zai faru annunawa duniya cewa ga wani jirgi
nan da ba na yaki ba, ya taho ya tunkuyi wannan gini, a zahiri wannan shine
abinda aka ringa bayyanawa mutane a kafafan watsa labai, to amma wani abu mai
cike da sarkakiya shine, bayan da aka doki wannan gini babu ko alamar wannan
jirgi, wanda abin mamaki ne kwarai da gaske, ace jirgi ya doki gini amma kuma
babu baraguzan jirgin, wannan ya sanya shakku sosai dangane da ainihin abinda
ya doki wannan gini, shin jirginne da gaske? Ko kuwa wani abune daga cikin
ginin ya tarwatsa shi? Bugu da kari, bayan da aka ce jirgi ya doki ginin a hawa
na can sama, sai gashi ginin dake hawa na daya da na biyu duk sun kama da wuta,
zai zama abin mamaki kwarai da gaske ace irin haka ta faru, sannan kuma da abin
ya faru ginin ya kama zagwanyewa yana yin kasa, duka wadannan abubuwan mamaki
ne, domin ya akayi baraguzan jirgin suka bace bat sama ko kasa? Sannan ta yaya
gine-ginen kasa suka kama da wuta? Sannan tayaya akayi daga dukan gini sai ya
zagwanye gabaki daya? Yana da kyau mai karatu ya sani duk wannan anyi ne domin
a rudi duniya da sanya shakku a tattare da mutane.
Yana da kyau mu fahimta duk wannan abin
da ya faru fitina ce wadda CIA suka shirya ta, tare da manyan kiristoci domin
su tayar da hankali duniya, kuma akayi amfani da rubabbun musulmi masu son abin
duniya domin cimma wannan mugun nufi na matsafa ‘yan mafiya. Kuma duk sunyi
karatunsu a Amerika aka yi amfani da su domin cimma wannan boyayyar manufa,
daga cikin mutanan da Amerika tayi amfani da su akwai Shugaban Afghanistan na
yanzu Hameed Karzai wanda Ba-Amerike ne dan Aghaninstan yana aiki a kamfanin mai
a Amerika aka dauko shi domin a yi amfani da shi wajen rusa musulunci da
Afghanistan, lokacin da ya zo ko birnin kabul bai gama sani, sannan kuma Amerika
sunyi amfani da wani mutum Zalmey Khalil Zadeh a matsayin jakadansu a
Afghanistan; a can kuma munga yadda aka yi amfani da su Nuri Al-maliki da Iyad
Alawi a Iraqi.
Da aka tambayesu (Amerika) cewa ina
buraguzan jirgin da ya doki wannan gini? sai suka ce ya narke ya shiga cikin
karikitan ginin. Wanda kamar yadda muka sani mafi yawan hatsarin jirgi idan ya
faru yakan bar sassan jikinsa, amma wannan da ya faru babu ko da kusa daga
cikin sashin jirgin, kuma suka yi amfani da kafafen watsa labaransu suka sanya
mutane suka yarda cewar sassan jirgin sun narke a cikin baraguzan ginin.
Kamar yadda bayanai suka nuna, shi
wannan gini ba dai-dai yake da sauran gine-gine ba, domin babu kasa kokadan a
cikin ginin, karafane da gilasai da alminiyo a cikin gini gabaki daya. Wanda bayan
wannan abu ya faru munga kura da hayaki sun turnuke, ta ina aka samu kura da
hayaki a cikin ginin da akayi da karafa da gilasai? Mazon ALLAH Salallahu
Alaihi Wasallam ya ja hankalin al’umma akan yadda a karshen zamani fitina zata
kasance kamar kura da hayaki, kuma Alamu ne na zuwan mahadi yadda kura da
hayaki zasu turnuke, daga nan kuma sai wasu fituntunu su biyo baya (Al-muttaki
al-hindi, Al-burhan fi alamat al-mahdi Akhiriz zaman) Dan haka wannan hayaki da
ya biyo bayan rubzawar wadannan gine-gine alama ce da take nuna zuwan fitina,
wadda ya zuwa yanzu ta bayyana kowa ya ganta.
Daga cikin hikima ta injiniyoyi, ta nuna
cewa wannan ginin ya tsufa yana iya faduwa, ginin yana bukatar a rushe shi a
sake gina sabo. A gurare da dama a duniya akwai irin wannan hikimar ta rushe
tsohon gini, sukan yi amfani da na’ura mai rushe gini, kamar yadda wannan na
Pentagon ya faru, sannan a kama mutane da laifi, bayannan a sake su rana a
tsaka, bayan ankama wanda ake son kamawa tun can usuli, wannan shine kusan abin
da ya faru. A saboda ana zargin musulmi ne da kai wannan hari wannan shi ne zai
bayar da damar mamaye Afghanistan da Iraqi da sauransu?
Domin mai karatu ya sake tabbatar da
cewar wannan abu da ya faru duk shiri ne, na mafiyawan Amerika, ita wannan
cibiya bayanai sun tabbatar da cewa wadannan Yahudawa barbarar yanyawa sune
kusan suke mamayeta a kullum da harkoki na hada-hada, amma ranar da abin zai
faru babu ko daya daga cikinsu da yaje wajen, sannan kuma anga wasu mutane daga
nesa da suke ta dauko hotunan ginin ‘yan mintoci kadan kafin faruwar wannan al’amarin,
abinda ya sake tabbatar min da cewa Amurkawa ne da kansu suka rusa wannan gini.
Akwai wani fim mai suna THE SWORD FISH, ina fatan mai karatu ya samu dama ya
kalli wannan fim din shakka babu zai tabbatar da cewar wannan abin da ya faru
na rushewar wannan ginin daman can shiryayye ne. Kawai suna amfani da kafafan
watsa labarai ne sun cin duniya da buguzum.
Bayan da wannan abin na 11 ga satumba ya
faru, sai majalisar dokokin Amerika suka yi wata fargar jaji, inda suka kafa
wata hukuma mai suna The National Commission On Terrorist Attack Upon The Us
wadda aka fi sani da (9-11 Commission)
inda nan da nan Shugaba Bush ya sanya hannu dan tabbatar da wannan hukuma domin
ta bayyana hakikanin abinda ya faru a wannan rana ta 11 ga satumba, inda suka
dauke hankalin duniya daga ainihin inda gaskiya take zuwa sai abinda suka
fadawa mutane, wannan hukuma sun saki wani rahoto na kanzon kurege akan abinda
ya faru, kana iya duba wannan rariya domin ganin abinda suka ce http://www.9-11commission.gov/report/index.htm duk wannan ba komai yake nunawa ba illa kaiwa makura na makircin Amrika ga
kasashen musulmi da kuma mamaye arzikinsu.
Haka kuma, marubucin littafin The Ghost
Wars, mista Steve Call ya yi wasu bayanai masu sarkikiya a cikin wannan littafi
da ya wallafa a shakarar 2004, inda ya yi bayanin cikakke akan kungiyar leken
asiri ta CIA da kuma bayanin yadda gwamnatin Bush ta shiga Afghanistan da kuma abinda
ya shafi Bin Laden. A wani fim Documentary wanda gidan talabajin na Al-jazeera
suka haska acikin watan Yuli mai suna I KNEW BIN LADEN wanda suka yi isharori
masu sarkakiya akan abinda ya faru, domin anyi hira da mutane na kusa da Bin Laden.
Kungiyar leken asirin Amurka ta CIA
kusan ta fara aikin leken asiri a kasashen duniya kusan tun zamanin shugaban
Amurka na farko wato George Warshington, amma bata zama cikakkiyar hukuma ta
gwamnati ba sai zamanin da akayi yakin duniya na biyu inda ta rika bada rahotannin
asiri, a lokacin ne shugaban Amurka na wancan lokacin Franklin D Rooservelt ya
nada babban lauyan binrnin New York Williams J Danovan a matsayin shugabanta na farko, wanda tsohon
masanin yaki ne, kuma tsohon masanine a harkar da ta shafi binciken kwakwaf.
CIA kusan babu wata kungiya mai hadari a
duniya sama da ita. Wannan kungiya kusan dukkan kasashen duniya babu inda bata
aiki, sannan babbar hanyarsu ta samun bayanai sune ta hanyar amfani da
jakadunsu dake kasashen duniya domin aiko musu da rahotannin yadda al’amura ke
kasancewa, suna amfani da mutane da yawa a cikin kasashen su domin su ringa
basu bayanai na asiri, ba tare da wadan da ake aikin da su sun san me ke faruwa
ba. A shekarar 2004 shugaba Bush ya sake inganta aikin CIA inda ya sanya hannu
a ranar 14 ga watan Disamba akan gyaran fuska da akayiwa dokokin CIA da suka kira
Terrorism Prevension Act.
Tambayar da wata kila wasu ‘yan uwa zasu iya yi
ita ce wannan abinda ya faru na 11 ga satumba shine silar mamaye Afghanistan da
Iraqi ko kuwa akwai wata manufar daban? Kuma ina matsayar yunkurin kamfanin
Unocal na shimfida bututun iskar gaz a Afghanistan ya tsaya? Insha ALLAH zamu
zo da bayani akan haka, anan gaba.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment