Wednesday, October 3, 2012

KISAN DALIBAI A MUBI: Najeriya Ba’a Taki Zaman Lafiya Ba!



KISAN DALIBAI A MUBI: Najeriya Ba’a Taki Zaman Lafiya Ba!

Labarin  da muka wayi gari da shi a jiya wanda ya fito daga garin MUBI a jihar Adamawa, labari ne mai tayar da hankai, kuma mai karkada zukata. Hakika wannan babban abin tashin hankali ne ace anje har wajen kwanan dalibai anyi musu irin wannan kisa na gilla! Wannan yake kara nuna sukurkucewar al’amura a Najeriya kuma Wallahi ba’a taki zaman lafiya ba.

Rahotanni dai sun nuna cewar bayan zaben shugabannin kungiyar dalibai ta SUG ne wanda aka yi tsakanin Bahaushe dan Arewa da Inyamuri dan kudu maso gabas, wanda sakamakon zaben ya nuna cewar dan Arewa shine ya samu nasarar wannan zabe. Mako guda bayan wannan zabe aka bi kusan gabaki daya daliban da suka samu nasarar wannan zabe aka yi musu kisan gilla; wannan babban al’amari ne domin rayukan mutane akalla 42 ba wasa bane.

Har ila yau, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar mutane ne sanye da kayan jami’an tsaro suka dinga aikata wannan mummunan aiki na ta’addanci, yayin da aka ringa kiran sunan daliban daya bayan daya suna fitowa, wasu ana harbesu da binduga wasu kuma anyanka su a makogaro. Wannan abinda ya faru shakka babu daliban da basu sami nasara a wannan zaben ba su suka aikata shi, domin babu wani maganar boye-boye a cikin wannan lamari.

Amma saboda rashin adalci da rashin gaskiya, sai ake neman alakanta wannan al’amari da cewa Boko Haram ne suka aikata domin a dauke hankalin mutane daga ainihin inda gaskiya take. Duk wata kwaskwarima da za’a yiwa wannan al’amari tabbas dalibai ‘yan kudancin Najeriya musamman Inyamurai da basu sami nasara a wannan zabe ba, baza su taba fita daga zarginmu ba.

Lallai ne hukumomi su gudanar da binciken na gaskiya domin gano hakikanin wadan da suka aikata wannan mummunan aikin ta’addanci domin hukunta su kamar yadda doka ta tanada, ko kuma sakamakon da zai biyo baya ya kasance mara kyau kwarai da gaske. Kuma Wallahi matukar ba’a yi adalci ba, hukumomi su sani sun dauki hanyar yamutsa kasar nan. Dole a binciko masu laifi kuma a hukunta su, sannan dole a biya diyyar duk daliban da suka rasa rayukansu a sanadiyar wannan al’amari.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

No comments:

Post a Comment