ZABEN AMERIKA:
Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba!
Yanzu a wannan
karni na ashirin da daya (21) kasar Amerika it ace kasar da take jagorantar
tsarin jari hujja a duniya. Amerika it ace kasar da kusan tafi kowace kasa
karfin tattalain arziki, da kuma, karfin makamashi, wanda yanzu kusan shi ne
yake juya wainar siyasar duniya. Wato tsarin siyasa da karfin tattalin arziki,
a wannan karnin baka samun karfin tattalin arziki sai ka mallaki karfin
makamashi kamar yadda Henry Kissinger ya fada a hirar da ya yi da jaridar Daily
Squab a ranar 27 ga watan Nuwamban 2011, inda yake cewa “wanda yake da iko akan
makamshi, to ya sami iko akan kasashe” wannan iko da kasar Amerika take da shi
kusan shi ne ya bata ikon juya kasashen duniya yadda taga dama.
Siyasar kasar
Amerika ta sha bamban da siyasar sauran kasashen duniya musamman kasashen masu
tasowa. Siyasar kasar Amerika tana cike da sarkakiya da kutunguila da makirci
na kin karawa, sannan uwa uba kuma abinda yake jan linzamin siyasar kasar
Amerika shine ‘tattalin arziki’. Wato baka iya zama mai fada aji sai kana da
karfin tattalin arziki kamar yadda da yawa suke da masaniyar cewar kasar
Amerika kusan it ace ke kan gaba wajen jagorancin kasashen duniya mafiya karfin
tattalin arziki da ake kira da suna G20 da kuma kasashen masu karfin arzikin
masana’antu na G8 dama ko ‘G’ wacece, duk zaka samu Amerika it ace take da
karfin fada a ji a tsakanin Dukkan kasashen da suka kulla kawance.
Kusan tun bayan
faduwar kakkarfar tarayyar Soviet wadda Rasha ta yiwa jagoranci Amerika ta samu
damar cin karanta babu babbaka wajen yin yadda taga dama da kasashen duniya a
mastayin jagorarsu. Duka da rusashshiyar tarayyar Sobiya karkashin jagorancin
Rasha da kasar Amurka ba wani abu suke yiwa ba, illa irin dumbin arzikin
makamshi da Allah ya huwacewa wannan duniyar, sai dai sun dan sha bamban ta
wata fuska, domin ita kasar Rasha tafi mayar da hankalinta ne akan abinda ya
shafi makamashin iskar Gaz, wanda nasan da yawa jama’a suna sane da katafaren
kamfanin isakar gas dinnan na kasar Rasha da ake kira Gazprom. Dalilin da ya
sanya kasar Rasha tafi mayar da hankali akan abinda ya shafi makamshin isakar
gaz yana da alaka da yanayinsu na dusar kankara a Rasha da kuma gabashin Turai,
wanda wannan kamfani na Gazprom kusan shine babban kamfani mallakar Rasha da
yake samar da makamashin isakar gas ga ita kasar rashan da kuma kasashen da ke
gabashin Turai harma da na yammacin turai; sanna kuma ita a nata bangaren kasar
Amerika tafi mayar da hankali ne akan abinda ya shafi gurbataccan man fetur da
dangoginsa, saboda manayn masana’antun da take da shi.
Dan haka siyasar kasar
Amerika kusan tana tafiya ne kacokaan akan abinda ya shafi cigaba da mamayar
tattalin arzikin kasashen duniya. Ina jin jama’a bazasu manta da kamfanin kasar
Amerika mai suna Halliburton ba, wanda aka zarga da badakar cin hanci ta dubban
miliyoyin daloli akwanakin baya a Najeriya, shi wannan kamfani mallakar wasu
manyan attajiran kasar Amerika ne wandanda kuma sune suke juya akalar siyasar
kasar Amerika, shi wannan kamfani wanda cibiyarsa take a Texas, Iyalan Bush da
Iyalan Bin Laden suna da hannun jari mai girma acikinsa. A kashin gaskiya
siyasar Amerika kusan tafi ta kowace kasa makirci da mafiyanci da kutunguila da
kuma sarkakiya, sanannen abu ne cewar akwai alaka mai karfi tsakanin manyan
kamfanonin jari hujja na Amerika da ake kira Corporate Capitalism da gwamnatin
Amerika, domin wadannan gungu na mafiyawa sune suka shigar da duk wani shugaban
kasar Amerika fadar white House da kuma wakilan majalisar dokoki da ta dattabai,
dan haka sune suke samar da shugabannin Amerika da wakilai wadan da zasu kare
manufofinsu na kasuwanci.
Tsohon shugaban
kasar Amerika Franklin D Roosevelt ya
taba fada a gaban majalisar dokokin Amerika a ranar 29 ga watan Afrilun
shekarar 1938 cewa “cin gashin kai na tsarin demokaradiyya ba zai taba zama
cikin aminci ba, idan har akwai wasu tsirarun mutane da suka kafa wasu cibiyoyi
da karfinsu ya fi na gwamnatin demokaradiyyar da jama’a suka zaba. Wannan yana
nufin cewa gwamnati ta zama ta wasu dai-dai kun mutane da wasu cibiyoyi da zasu
ringa sarrafa ta daga nesa kenan”. A hakikanin gaskiya wannan shine abinda yake
faruwa dangane da siyasar kasar Amerika, duk ihun da wani shugaban kasar yake
yi ko daga Democrat yake ko daga Republican yana yi ne karkashin kulawar
wadannan shaidanun mafiyoyi.
Wani muhimmin
misali akan haka shine, daya daga cikin manyan kamfanonin mai na kasar Amerika
mai suna UNOCAL ya taba nuna maitarsa a bainar jama’a dangane da dumbin
albarkatun makamashin da suke kwance a tafkin Caspian sea, daya daga cikin
manyan shugaban kamfanin mai kula da alaka tsakanin kasa da kasa Mista John J
Merosca ya taba gabatarwa da kwamatin dake kula da alaka tsakanin kasashen na
majalisar dokokin Amerika a ranar 12 ga watan fabrairu na shekarar 1998 cewa “ akwai
dumbin albarkatun makamashi da Allah ya huwacewa yankin tekun Caspian” daga nanne kuma ya yi wata ishara mai cike da
kitumurura waddaa zata kai ga shimfida bututan da zasu kai ga hako wadannan
albarkatu da ke kwance a wannan tafki.
Yana da kyau mu
fahimta cewa babu wani bambanci na kuzo mugani dangane da siyasar cikin gida da
waje tsakanin manyan jam’iyyun kasar Amerika guda biyu wato Democrat da
Republican. Kasar Amerika kusan sha-kundum ce, siyasar kasar Amerika ta wuce
ayi kamfe da suna wutar lantarki ko ruwan famfo ko harkar lafiya ko harkar
ilimi, fiye da shekaru dari kasar Amerika ta fitar da kanta daga wannan
mastalar, dan haka wadannan sunyi kadan su mamaye siyasar kasar Amerika.
Bugu da kari, ga
duk wanda yake bibiyar yakin neman zaben da ake yi tsakanin Barack Obama da
Mitt Romney kusan batu ne guda uku da suke jayayya akansa! Abu na farko shi ne,
Shin kasar Rasha abokiyar gabar Amerika ce ko kuwa kawarta ce da akewa juna
kallon hadarin kaji, sannan kuma da batun Shin akaiwa Iran hari a yanzu ko kuwa
sai wani lokaci na nan gaba, duk kuwa da cewa shi kansa wannan batu na kasar
Iran wani batu ne mai cike da sarkakiyar gaske, haka kuma, da batun shin
Amerika zata jibge dakarunta a kasar Syria ko kuwa. Wanda wannan batu na Syria
yake kara nuna cewa ba mai karewa da wuri bane domin shima yana cike da makirci
da kutunguila irin ta shaidanun ifuritan Amerika masu juya tsarin jari hujja,
sannan da ibilisan kasashen irinsu Rasha da chana da Iran. Kada ka dada kada ka
raga wadannan sune manyan batutuwan da suka mamaye yakin neman zabe tsakanin
Obama da Romney.
Abinda zai kara
tabbatar da cewar duka wadannan jami’iyyu na Amerika bakisnsu daya, inda suka
saba shine wajen aiwatarwa, misali jami’iyyar Democrat ta Bill Clinton ta shiga
kasar Afghanistan ta hanayr tattaunawar Diplomasiyya, yayin da jam’iyyar
Republican ta George Bush ta shiga Afghanisatan ta hanayr amfani da karfin
soji, idan akwai bambanci to wannan shine bambancin dake tsakanin wadannan jam’iyyu
amma duk manufarsu day ace, kawai a aiwatarwa suka bambanta. Shugaban Obama ya
taba fada cewa gwamnatin kasar Amurka kamar wani jirgin kasa ne da ya yake
tafiya duk shugaban kasar Amerika sai dai ko ya kara gudunsa ko kuma ya rage
gudunsa, amma ba zai iya tsaida shi ba, ballantana kuma ya canza masa akala
daga yamma zuwa gabas, wannan shine kusan hakikanin makirci da kutunguilar
siyasar Amerika.
Haka kuma, shata
iyakokin manufar kasar Amerika dangane da kasashen duniya aiki ne na kwararrun
cibiyoyi, ba na jam’iyyar siyasa ba. Wato wannan yake kara tabbatar mana da
cewa su wadancan shaidanu karkashin Corporate capitalism sune suke yin uwa suyi
makarbiya a harkar siyasar kasar Amerika bayan anyi zabe an gama. Wannan yake
nuna Amerika ba kamar kasashene masu tasowa ba, ta yadda duk shugaban da yazo
yana iya rusa Dukkan ayyukan da magabacinsa ya yi, sannan ya dora nasa sabo,
Amerika tasha gaban haka, duk kwarewarka da wayo da dabara dole ka tafi akan
wannan tsari da kazo ka tarar.
Dan haka duk wasu
ihu da hayaniya da jam’iyyun Democrat da Republican zasu yi, bai wuce share
hanyar da za’a cimma wadannan manufofi na kasarba.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment