Saturday, October 6, 2012

ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (3)



ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (3)

Ina fata masu bina basu manta inda muka tsaya ba, a mukalar da ta gabata, wato mun tsaya da bayani, inda Amerika ta kitsa yakin Iraqi domin ta mamaye danyan man fetur, yanzu kuma zamu dan sauka daga kan wannan batu domin mu duba wani batun da yake da alaka da siyasar ta Amerika.

A shekarar 2009 da ta gabata Shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev ya kawo ziyarar aiki zuwa Najeriya, inda ya gana da tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa YarAdua. Wannan ziyara da shugaban Rasha Medvedev ya kawo zuwa Najeriya ba wata ziyara ce ta Allah da Annabi ba illa ta kokarin da kasar Rasha take yi na fadada ikonta akan makamshi, domin akarkashin wannan ziyara kamfanin Gazprom na Rasha ya rattaba hannu akan wata yarjejeniyar zuba jari a Najeriya da takai kusan dala Biliyan biyu da rabi ($2.5b) a Najeriya. Kuma sannan kamfanin ya sanya hannu akan wata kwangila da kamfanin NNPC na Najeriya ta shimfida bututun iskar gaz wanda zai tashi tun daga garin Warri a Najeriya domin ya isa kasar Rasha, wannan aiki na shimfida bututun iskar gaz zai tashi tundaga wannan gari na Warri ya ratsa ta Jamhuriyyar Nijar sanna ya bi ta garin Hassi Ramel dake kasar Al-jeriya, daga nan kuma ya hade da cibiyar da take baiwa nahiyar Turai iskar gaz dake gabar Tekun Meditareniya.

Duk wannan bayani bai wuce batun da ya shafi tattalin arziki ba tsakanin kasar Najeriya da kuma Rasha, ba komai wannan yake nunawa ba illa irin yadda kasar Rasha take son nuna karfinta ga abokiyar burminta Amerika akan harkar da ta shafi makamshi a duk inda yake a fadin duniya. Najeriya dai bata wuce wani dan karamin filin yaki ba a tsakanin kasar Rasha da kuma kasashen yammacin turai bisa jagoranci Amerika ba, domin babban filin daga ga wadannan kasashe shi ne yanki gabas mai nisa na tsakiya da kuma yankin gabas ta tsakiya, domin yankin gabas ta tsakiya nanne inda Allah ya huwacewa dimbin arzikin makamashin gurbataccan manfetur da dangoginsa, shi kuma, yankin gabas mai nisa na tsakiya wato Far East ko Asiya ta tsakiya wani yanki ne da Allah ya hore masa dimbin arzikin makamashin isakar gaz.

Wani marubuci Naomi Chvosky ya ce “a zahirin gaskiya Amerika tana son ta mallaki duk wani makamshi da ke fadin duniyar nan domin shimfida iko wanda zai taimakawa manyan masana’antunta” duba da wannan magana, zamu ga cewa mafi yawancin man fetur din da Najeriya take fitarwa yana zuwa Amerika ne kai tsaye, dan haka kuwa babu yadda Amerika zata bari kasar Rasha ta mamayi duk wata harka ta makamashi da ta shafi Najeriya.

Yanzu haka a wannan karnin da muke ciki na 21 gabaki daya hankalin kasar Amerika ya karkata ne zuwa ga abinda ya shafi makamashi musamman na iskar Gaz, wanda Rasha ta dade da yin fice akansa. Wannan ce ta sanya tsohon shugaban kasar Rasha da ya sauka Vladmire Putin ya karkato da hankalin Rasha zuwa ga abinda ya shafi harkar siyasar kasa da kasa da kuma sauran siyasar duniya da kuma tattalin arziki; domin a cikin ilimin kasa da kasa da ake kira da suna International Relations akwai wani muhimmin batu da ya ke magana akan siyasa da tattalin arziki, wannan ce ta sanya kasar Rasha taga babu yadda zata yi face ta kulla kawancen siyasa da kuma tattalin arziki da kasar Chana da Iran akan yankin Gabas mai nisa ta tsakiya ko kuma Asiya ta tsakiya, domin yanki ne mai sarkakiyar gaske, kuma mai dimbin arzikin makamashi.

Wani muhimmin darasi da kasar Rasha ta dauka daga yakin cacar baki tsakaninta da yammacin Turai a karkashin jagorancin kasar Amerika shine gasar kera makamai, domin wannan shine abinda ya yi saurin karya Rasha a hannun abokan gabarta, domin shugaban Amerika Ronald Regan ya ringa kiran rusashshiyar tarayyar Sobiya karkashin Rasha da cewa wata muguwar daula ce mai tsotse bargo da laka gabaki daya. Dan haka tun a shekarar 2000 da Putin ya zo a sabon shugaban Rasha ya yi kokari wajen mayar da Rasha wata muhimmiyar kasa a fagen kera makamai da kuma iskar gaz, domin har yanzu Rasha ita ce ke bin bayan Amerika a fage kera makamai, Rasha ta karfafa ikonta sosai akan kamfanin Gazprom wajen yawaita hannun jarinta a wannan kamfani.

Tsohon shugaban kasar Rasha Boris Yeltsin bai haifarwa da Rasha da komai ba a fagen siyasar tattalin arziki face samar da ‘yan mafiya masu son mamaye makashi ta ko wace fuska, wadanda mafiya yawancin wadannan ‘yan mafiya Yahudawa ne masu biyayya ga kasar Israela, irin wadannan gungu na ‘yan mafiya ne, Shugaba  Putin yayi ta kokarin ganin ya kakkabesu dan ganin ya shimfida nasa ikon, har kuma hakarsa ta cimma ruwa, inda yaci nasarar kafa na hannun damarsa wato shugaban Rasha na yanzu Dimitry Medvedev a matsayin shugaban kamfanin Gazprom, wannan mutum Medvedev shine suka yi musayar shugabanci da Putin bayan da wa’adin Putin ya kare a matsayin Prime Minista da kuma shugaban kasa, wanda wannan shine yake kara tabbatar da auren din-din-din tsakanin siyasa da kuma makamshi a wajen fadar gwamnatin Kremlins da ke Moscow.

Ita kanta kasar Rasha kasa ce da Allah ya huwacewa dimbin arzikin iskar gaz da ke kwance a karkashin dusar kankarar Saberia. Domin a manya manyan filayan da Rasha take da su a wannan yanki a kwai wani fili da ake kira da suna Urengoy wanda daya ne daga cikin wadannan filaye akwai dimbin makamshin iskar gaz da ya kai kimamin cubic metre Tiriliyan goma (10tr). A rahoton kungiyar Tranferency Internatinal akan kasar Rasha, ya nuna cewa ita ce wacce tafi kowace kasa arzikin iskar gaz a duniya domin ita kadai nata yakai kimanin kashi 24% na adadin dukkan Gaz din da ke wannan duniyar, a yayinda kasar Iran ke biye da Rasha da kaso 16%, sannan kuma, kasar Qatar ke biye da Iran da kaso 10%.

Watakila mai karatu ya ce daga maganar siyasar kasar Amerika kuma mun bige da bayani akan kasar Rasha. Shakka babu kamar yadda na fada kusan tun a farkon mukalarmu cewa siyasar Amerika tana cike da sarkakiya da kutunguila acikinta. Domin siyasar kasar Amerika bazata taba cika ba idan ba’a kawo wadannan bayanai da suka shafi Rasha ba, domin suna da alaka da abinda ya shafi makamashi. Sannan kuma idan mai karatu ya lura munyi batun biyayyar mafiyan kasar Rasha ga Yahudawan Israela, wanda wannan shi kansa wani batu ne mai zaman kansa dangane da abinda ya shafi siyasar Amerika, domin su wadannan mutane na Corporate Capitalism kusan suma Yahudawa ne, sai dai daga su har na Rasha din bawai ainihin yahudawan da Allah ya bamu labarinsu a al’qur’ani bane, domin galibin wadannan Yahudawan na yanzu su Netanyaho da Yizhaq Rabil da su Ariel Sharon da Olmet da su Bill Clinton da Bush da sauransu duk barbarar yanyawa ne, ba Yahudawa ne zuryan ba. Haka kuma, baza ka taba yin bayanin siyasar Amerika ba tare da anyi batun kungiyar leken asiri ta CIA ba da kuma harkar kafafen watsa labarai, wadannan wasu muhimman al’amura ne a siyasar Amerika, wanda zamu yi bayaninsu nan gaba insha ALLAH.

Idan muka duba kuma, zamu ga cewa alakar kasar Rasha da kamfanonin makamashi na yankin Asiya mai nisa, ya fara ne kusan tun kafin rugujewar tarayyar Sobiya, domin har yanzu wannan dadaddiyar alaka tana nan. A shekarar 2007 da ta gabata kamfanin makamashi na Rasha Gazprom ya karbi kusan kashi 75% na dukkan makamashin da kasar Turkministan ta fitar, wanda ya kai kimanin ma’aunin cubec metre biliyan 42.6. sannan kuma, daga kasar Kazakstan ya kai kimanin biliyan 8.5, haka kuma, itama kasar kazakhstan ya kai biliyan 9.4; anan dole mai karatu ya lura sosai domin akwai bambanci tsakanin kasar KAZAKSTAN da kuma KAZAKHSTAN. Wadannan kasashe sune kasashen da suka fi kowace kasa  arzikin iskar gaz a yankin Asiya mai nisa ta tsakiya, dan haka, adadin iskar gaz dinda kamfanin Gazprom ya karba daga wadannan kasashe ta kai kimanin tiriliyan 60.7 a ma’aunin cubec mitre acikin shekara guda daya kacal.

Muhimmancin da wannan yanki yake da shi, a wajen kasar Rasha ya dara wanda yankin gabas ta tsakiya yake da shi a wajen kasar Amerika, a saboda haka irin muhimmancin da yankin gabas ta tsakiya yake da shi a wajen Amerika kamar tankin mota ne a wajen mai tuka mota, dan haka duk irin sansanonin sojin da Amerika take da su a wannan yanki bai wuce na ganin duk arzikin manfetur din yankin bai subuce mata ba, hatta irin kariyar da Israela take samu daga Amerika duk yana ta’allake da wannan arziki na makamashin manfetur ne, domin yanzu da za’a wayi gari ace babu wannan arziki a yankin gabas ta tsakiya, ita kanta kasar Israela sai dai ta san inda dare ya yi mata.

A saboda kasar Rasha ta samu gindin zama wajen gaje moriyar arzikin wadannan kasashe na gabas mai nisa sai ta yi kokarin kafa wani kawancen da aka ce ba’a so a sami sabani, tsakaninta da kasashen wannan yanki wadan da suka hada da kasar Chana wadda ita ke zaman a matsayi na biyu bayan Rasha wajen cin-moriyar makamashin iskar gaz da yake fita daga wannan yanki, wannan kawance shi aka kira Shanghai Corporation Organization wanda ya kunshi kasashen Asiya ta tsakiya guda hudu da suka hada da Kazakhstan da Kyrgistan da Uzbakistan da kuma Tajkistan, tun bayan kafa wannan kungiya a shekarar 2001 sai ga kasar Amerika a 2006 ta kawo kokon bararta cewa wadannan kasashe su yiwa Allah su sanyata a matsayin ‘yar kallo a cikin wannan kawance, wanda karkashin jagoranci Rasha suka yi fatali da wannan roko na kasar Amerika.

Idan mai karatu bai manta ba,  a baya can  munyi maganar tekun caspean sea wanda muka ce yana da dumbin arzikin makamashi wanda har mafiyoyin Amerika suka fara nuna kulafucinsu akansa, da tunanin yadda za’a hako shi zuwa kasar Amerika. Insha Allah a mukala ta gaba zamu maida hankali ne akan wannan yanki, da bayanin yadda Amerika da Rasha  suka haifar da yakin kasar Afghanistan domin samun hanyar da zasu shirya bututun da zai dauko wannan arziki zuwa kasashensu, wannan batu na arzikin da yake a tekun Caspean sea shima wani batu ne mai sarkakiyar gaske dangane da siyasar kasar Amerika, amma da sannu insha Allah zamu warwareshi domin jama’a su fahimci yadda al’amarin yake.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale



No comments:

Post a Comment