HAPPY BIRTH DAY:
Yasir Ramadan Gwale @ Goma sha Goma Gare
kan Gare!
Assalamu Alaikum
warahmatullahi Wabarakatuh. Alhamdulillah, ina mai amfani da wannan dama na yi
godiya ga Allah subahanahu wata’ala da ya kawoni wannan lokaci mai cike da
kalubale a rayuwata, lokacin da muke ta fadi tashin ganin ansamu rayuwa
ingatacciya. Allah ta’ala ya fada acikin littafinsa mai tsarki cewa “ban halicci
Dan-Adam da Al-jani ba sai dan su kadaitani da bauta” . . . Hakika manufar
halittar Dukkan wani abu mai numfashi a ban kasa, shi ne ya kadaita Allah da
bauta, Allah madaukakin sarki ya umarcemu ta hanyar da’a ga dokokinSa, da kiyaye shari’ar
da ya sanya mana, wanda ya aiko Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam ya zo
mana da ita. . . . . . . Allah abin
godiya.
Kusan, ni namanta
da cewa a ranar 2 ga oktoba aka haifeni, sai da wani dan uwa jiya ya aikomin da
sakon inbox yana yi min tuni da cewa gobe fa ranarka ce, da naga wannan sakon
da farko ban fahimce shi ba, sai da wani
ya sake aikomin da HBD sannan na fahimta. Na yi addu’ah kuma na roki Allah ya
bani ikon ganin goben, Alhamdulillahi yau gamu a goben jiya.
Tunda sanyin
safiyar yau Turakata(wall) ta fara daukar harami, abinda ya fara daukar
hankalina shine yadda naga jama’a na ta makalamin abin FALFALI wanda yake nuna
cewa lallai yau akwai DANASHA kena, wasu masu himma har ALIBIDI naga sun kawo, dukka
ina godiya da farinciki a gareku.
Nasan da yawa ba
suna tayani murna bane akan na kara tsufa, domin rayuwar yanzu aka fara insha
Allah, sai dai abinda na lura da yawa suna min murna shekaru sun kara tafiya,
girma na kara zuwa, ni kuma ina kallon cewa ina kara kusa ne zuwa ga Ajalina,
domin kwanaki na da shekarun da aka
dibamin a duniya, naci wani adadi a cikinsu yazuwa yanzu.
Alhamdulillah,
ina godiya kwarai da gaske, bisa soyayya da ‘yan uwa suka nunamin, sannan ina
cewa AMIN da babban baki ga wadan da suka yimin addu’a ta fatan alheri da samun
nasara a rayuwa. Allah ya sadamu da alherinsa duniya da lahira. Nima ina addu’ah
ta fatan alheri gabaki dayanku. A madadin Yasir Ramadan Gwale (Abu-Uthman) da
Ummu-Uthman muna cewa mun gode, Allah ya saka da alheri ya bar zumunci. Haka nan
bazamu manta da zazzagawa ba suma sunyi abin kwarai, sai dai bamu ga soyayyun
doyoyi suna ta karakaina ba . . . . Lol
Nagode.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment