Shiri Na
Musamman Dangane Zaben Amurka
Ita dai kasar Amurka kasa ce da
ta samu daukaka a wannan karni inda a halin yanzu ita kadai ce tilo a cikin
kasashe da ke da matsayin mai karfi sai Allah ya isa. Duniya, baki daya, na
zura ido ne ga abubuwan da ke gudana a kasar Amurka domin kwaikwayo ko kuma
tsara yadda makomar sauran kashen duniya zata kasance.
Wannan matsayi da ta samu kuwa
ya samo asali ne daga irin gwagwarmaya da wahalhalu da ta sha a hannun
Birtaniya a lokacin da ta yi mata mulkin mallaka.
Lokacin da tayi kokarin
kubucewa daga hannun Birtaniya an kai ruwa rana wanda daga karshe suka samu
nasarar samun yanci. Wannan yanci da Amurkawa suka samu sai suka yi amfani da
shi wajen tsarin da zai raba su daga komawa irin kangin da suka fito. Babban abinda
suka dabbaka shi ne yancin dan adam ta wajen magana da harkokin rayuwa. Sun
kuma bawa kokarin daidaita mutane mahimmanci. Kai a saboda wannan ne lokacin da
aka yi kokarin kawar da bauta kasar ta shiga yakin basasa.
Wannan yanci dai shi ne abinda
bakaken fata suka yi amfani da shi a cikin shekarun alif dari tara sittin wajen
samar musu matsayi daidai da duk wani dan adam a kasar Amurka.
A kunshe a cikin dimokradiyyar
Amurka akwai wannan tsari na yanci. A Amurka matukar ba wata ta'asa ko aikin
assha, bayyananne, mutum ya aikata ba yana da damar ya fito yayi takara kuma a
zabe shi, in har mutane sun gamsu da nagartarsa da kuma manufofinsa.
Wanna salo ya karawa kasar
Amurka tagomashi a duniya da kuma sauran tsare-tsare masu inganci da suka maida
ita farin wata a cikin kasashen duniya.
Zaben bana dai za'a kara ne
tsakanin Shugaba mai ci a yanzu, Barack Hussein Obama II da Willard Mitt
Romney. Shugaba Obama na takara ne a karkashin jam'iyyar Demokrat a inda shi
Romney yake takara a karkashin jam'iyyar Rifublikan.
Tarihin jam'iyyar Demokrat ya
samo asali daga shekarar alif dari bakwai da casa'in da biyu (1792) inda ta
ware daga wata jami'iyya mai rajin juyawa tsarin tarayya baya da ake kira Anti
Federalist. A shekarar alif dari takwas da ashirin da takwas ne jam'iyyar ta
zama jam'iyyar Demokrat bayan zaman gamin gambizar da suka yi da yan Refublikan
ya watse.
Manyan manufofin ita wannan
jam'iyya ba su wuce tabbatar da yanci ba da kuma samarwa mutane sake da
walwala.
Ita kuwa jam'iyyar Refublikan ta
kafu ne a shekarar alif dari takwas da hamsin da hudu a saboda manufar ruguje
cinikin bayi da bauta da suka tsaya a kai. Wannan ya sa ta samu karbuwa sosai a
arewacin Amurka da kuma rashin tagomashi a kudancin Amurka.
Babbar manufar jam'iyyar
Refublikan (wacce ake kuma kira da GOP ko Grand Old Party) shi ne kare masu
hannu da shuni domin su tara dukiya mai yawa. Haka kuma suna da hali irin na
yan mazan jiya.
To shi dai Barack Hussein Obama
shi ne shugaban Amurka na arba'in da hudu kuma na farko da ke da jinin bakar
fata. Shi dai an haife shi a Honalulu a jihar Haway (Hawaii). Baban sa baki ne
dan kasar Kenya wanda ya je kasar Amurka karatu inda ya hadu da mahaifiyarsa,
wacce take farar fata ce yar Amurka.
Shi dai lauya ne da yayi aiki a
matsayin lauyan masu neman kwatar yanci a jihar Chikago ya kuma koyar da ilimin
shari'ar tsarin mulki a makarantar koyon aikin lauya ta jami'ar Chikago.
Ya zama dan majalisar dattijan
jihar Chikago har karo uku kafin ya zama dan majalisar dattijai ta kasa daga
jihar Chikago a shekarar 2004 bayan sha kaye a kokarinsa na samun zuwa majalisa
wakilai a shekarar 2000.
Obama shi ne bakar fata na
farko da ya zama shugaban mujallar Haward Law Review, wacce mujalla ce mai kima
a harkar shari'a a Amurka.
Williard Mitt Romney hamshakin
dan kasuwa ne kuma tsohon gwamnan jihar Massachusetts. An haife shi a garin
Ditroit da ke jihar Michigan. Mahaifinsa wani babba ne a harkar kere-keren
motoci.
Karatun Romney dai
tsince-tsince ne. Ya shiga jami'ar Stanford amma ba'a je ko'ina ba ya tsallake
ya barta. Daga baya ya sake shiga wani kwas da makarantar shari'a ta Havard ta
ke yi tare da hadin gwiwar makarantar kasuwanci ta Havard. Ya gama wannan
karatu a 1975.
Hasashen masana ya fi bada
karfi ga samun nasarar Shugaba Obama duk da cewa kuri'ar jin ra'ayin jama'a na
nuni da cewa har yanzu ba wanda ya bawa wata rata ta azo a gani.
Babban abinda Amurkawa ke
dubawa wajen wa zasu zaba a wannan zabe bai wuce wanda zai taimaka wajen fitar
da su daga kangin talauci da suka samu kansu a ciki ba.
Obama yayi kokari mutuka wajen
ganin Amurkawa sun koma aiki kuma tattalin arzikinsu ya karu. Duk da an samu
cigaba kadan ta wannan fanni wasu na ganin kokarin da akayi ya gaza fatansu.
Obama yayi kamfe a shekarar
2008 a bisa doron tsamar da kasar Amurka daga yakin Iraki da Afghanistan da
kuma rufe kurkukun Guantanamo. Haka kuma yayi alkawarin inganta rayuwar
Amurkawa.
Wani babban abu da Shugaba
Obama ya ba muhimmanci shi ne inshorar lafiya ga Amurkawa.
Amurkawa da yawa na ganin cewa
Obama ya taka rawar gani wajen fannoni da dama na al'amuran kasar Amurka amma
babba abin damuwarsu shi ne, duk da cewa an samu cigaba, kason marasa ayyukan
yi a kasar har yanzu ya da dan yawa. Kusan kashi bakwai da digo tara cikin dari
ne ke gararamba ba aikin yi.
Kamfe din Obama a wannan karon
an yi masa lakabi ne da (ci) gaba (forward).
Romney da yan kamfe dinsa sun
maida hankali ne wajen kushe manufofin gwamnatin Obama tare da yin amfani halin
matsi da Amurkawa ke fama da shi wajen nuna cewa Obama bai taka rawar gani ba
saboda haka ba dalilin barinsa yayi tazarce. Suna caccakar tsarin inshorar
lafiyar da ya fito da shi.
Idan aka yi la'akari da
abubuwan da ka je su zo da wuya Romney ya kada Obama. Na farko dai Romney yana
fama da matsalar addininsa. Ma fi yawancin Amurkawa na kallon yan
darikar Mormon a mazaunin yan kungiyar asiri ba kiristocin kirki ba.
Na biyu akwai matsalar wani
bangare na jam'iyyarsu masu akida yan mazan jiya da ake kira yan Tea Party. Shi
dai Romney ba shi da akidar yan mazan jiya wanda haka ne ma ya sa shi dauko
Paul Ryan a mazaunin mataimaki don ya samu karbuwa a wajen yan tea party.
Amurkawa da yawa na da amannar
cewa duk da rashin samun sa'ar fitar da su daga kangin talauci gaba daya, Obama
ya fi Romney alamun fahimtar halin da mutane ke ciki da kuma sanin hanyar da
zai fito da su. Kai hasalima mutane, musamman masu shirye-shiryen barkwanci a
talabijin, na caccakar Romney a kan cewa shi hamshakin mai kudi ne wanda bai
san wahala ba tun tashinsa. Haka kuma kamfuna da dama sun mutu a hannunsa. Ga
maganar haraji da ake ganin yana kwange wajen biyan abinda ya kamata.
Duk da cewa Romney ya samu dan
tagomashi bayan muhawarar da suka yi ta farko da Obama da kuma tabukawar da ake
ganin yayi a sauran biyun, duk da cewa Obama ya fi shi kokari, ra'ayuyyka sun
fi karkata ga cewa Obama ne zai lashe zaben talata amma da tazara da bata taka
kara ta karya ba.
Wani abu da ya karawa
bada karfin gwiwar cewa Obama zai samu nasara shi ne iska mai tafe da
ruwa da aka yiwa lakabi da Sany. Obama ya yi amfani da wannan damar wajen shiga
cikin talakawa da wadanda masifar ta same su tare da nuna alhininsa. Kai har
wani gwamna dan Rifublikan na New Jersey ya jinjinawa Obama a kan irin rawar da
ya taka a lokacin wannan masifa.
Zaben kasar Amurka an la'akari
da yawan masu kada zabe da kowacce jiha ke da shi ba wai yawan kuri'un da
jama'a suka kada ba. Wannan tsari dai ana kiransa da electoral college.
A halin yanzu Obama yana da
tabbacin 186 daga cikin 270 da ake bukata kafin mutum ya samu darewa kan
kujerar mulki. Haka kuma akwai 57 da bakwai da ake ganin zasu tafi ne ga Obama.
Romney na da tabbacin 170 akwai kuma 36 da ake ganin sun karkata ne zuwa gare
shi.
Wannan zabe dai ana ganin
nasararsa tana hannun wanda ya samu rinjayen wadanda basu gama zartar da wa
zasu zaba ba.
Ko ma dai ya faru gobe, ko ma
wanene ya ci zaben maufofin Amurka ba zasu taba canjawa ba. Saboda haka ga mu
sauran kasashen duniya duk kanwar ja ce.
No comments:
Post a Comment