‘Yan Najeriya Na
Wancakalar Da Babbar Dama
Sau da dama nakan yi mamaki yadda mu ‘yan
Najeriya muka cika yawan korafi akan rashin tabuka wani abun kuzo mugani da
masu muki suke yi. Kullum muna ta yamadidi da cewa masu mulki idan anzabesu
suna komawa su zama ‘yan dumama kujera da amshin shata ga iyayan gidansu wadan
da suke zama tsani na hayewarsu kan Dukkan wasu madafun iko.
Siyasa na da muhimmanci ga kowace kasa da
take bin tafarkin mulkin dimokaradiyya, dalili akan haka kuwa shine tsarin
siyasar demokaradiyya na Baiwa al’umma kasa damar zaben shugabannin ko wakilai
da zasu jagoranci al’umma ta Dukkan bangarori na gwamnati, wannan tsari na
demokaradiyya ya Baiwa al’ummar kasa damar zaben mutanan da suke ganin sun
cancanta da su share musu hawaye domin fitar da su daga halin kunci da masti na
rayuwa.
Al’ummar kasa suna bayar da goyon baya
ainun wajen ganin sun marawa mutumin da suke da yakin zai share musu hawaye, ya
samu kaiwa ga gaci domin yi musu shugabanci ko wakilci nagari. To amma babban
kuskuren da al’umma suke tafkawa wajen zaben shugabannin da wakilai shi ne shin
sanin tayaya talakawa zasu san mutumin da ya dace su zaba ya shuagabancesu ko
ya wakilce su? A lokuta da dama talakawa na korafin cewar sunyi zaben
tumun-dare musamman ga wakilai wadanda suke tafiya majalisar kasa su zama ‘ya
Aye da Nay.
Talakawa ko masu zabe suna da babbar dama
da kusan tun da Najeriya ta komo mulki irin na tsarin demokaradiyya ake ta
wanacakali da wannan muhimmiyar damar. Domin tsarin mulkin da yanzu ake neman
yiwa kwaskwarima ya yi tanadin cewa duk mutumin da baya yiwa al’umma wakilci na
gari suna iya yi masa kiranye ya dawo gida a sake zabe a tura sabon wakili,
amma wannan damar muna ji muna kallo ta saraya a garemu, duk kuwa da masu ilimi
da muke da su da suka san da zaman wannan ayar doka. Duk mutumin da muka zaba
muna ji muna kallo sai ya tafka tsiyarsa har ta tsawon shekaru hudu, ya kudance
ya zama hamshakin attajiri cikin ‘yan shekarun da basu kai cikin ‘yan yatsunsa
ba.
Mafiya yawan wadan da suke yin korafin
cewar sun zabi wakili ko shugaba yaje yana dumama kujera sune matasa. Wanda a
hakikanin gaskiya matasa a tsarin demokaradiyya sune gishirin tafiya, sau da
yawa ‘yan siyasa na amfani da matasa wajen cimma kaiwa zuwa ga wasu madafun
iko, ba laifi bane a yi amfani da matasa wajen tallata manufofi a tsarin
demokaradiyya, kamar yadda a baya bayannan ya nuna cewa a zaben da ya gabata na
Amerika matasa sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar shugaban Obama,
wannan ta sanya Obaman fashewa da kuka a gaban matasan lokacin da yake yi musu
jawabin godiyar sadaukar da kansu da sukayi.
Abinda yake laifi a tsarin siaysar
demokaradiyya shine ayi amfani da matasa wajen bangar siyasa domin samun nasara
ko ta halin kaka. A mafiya yawancin lokuta ana amfani da matasan ne domin
razana abokan hamayya da miyagun makamai, bayan anbasu kwayoyi da wiwi sunsha
sun cake. Abinda yafi zama abin mamaki shine su wadannan matasa ‘yan uwanmu
suna da masaniyar cewa shi wannan dan siyasa da ya basu kudi suka masa abinda
suk yi, ba tasu yake yi ba, sun san da cewar idan fa yaci zabe, basu isa su je
wajen da yake ba. Abinda yake zama abin mamaki shine shin matasan nan da suke
bari ana amfani da su dan cimma manufar zabe, duk da cewar sun san ‘yan siyasa
zasu yi watsi da su da zarar sun ci nasarar samun zabe, sun san ciwon kansu
kuwa? Suna da masaniyar cewa wadannan ‘yan
siyasa basu damu da su ba illa kawai sun maida su wata matattakala ta kaiwa
zuwa ga samun nasarar zabe? Amsar da muke san mu sani it ace yaushe ne
matasanmu zasu ki yarda ana amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa a bisa kudi
kalilan?
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
No comments:
Post a Comment