RANAR GODIYAR ALLAH A AMERIKA
A ranar kowacce Alhamis ta karshen watan Nuwamba ita ce rana mafi
muhimmanci a wajen Amerikawa sama da duk wasu ranaku na ibada ko na bukukuwa. Amerikawa
sun dauki wannan rana da kima da kuma muhimmanci kwarai da gaske, domin acewarsu
rana ce da suke nuna godiya ga ALLAH bisa baiwa da ni’imar da ya yi musu,
miliyoyin Amerikawa na yin doguwar tafiya domin saduwa da Iyali da ‘yan uwa da
abokai, domin wannan rana, haka kuma, gwamnati kan bayar da hutun da ya kai
kwanaki hudu, domin mutane su sami zarafin tafiya su sadu da ‘yan uwansu da
suka jima basu ga juna ba.
Ita dai wannan rana ta samo asali ne tun kusan shekarar 1598 a jihar Texas
inda Asalin Amerikawa wato Indiyawan daji kan hadu domin yin murnar kammala
aikin gona lafiya tare da nuna godiya ga Ubangiji cewa anyi noma lafiya kuma
angama lafiya. Kusan bayanai sun tabbatar da cewa daga shekarar 1863 ta zama
cewa duk shekara sai wadannan Indiyawan daji sunyi maci tare da yin gangami
domin bikin wannan rana, wanda wannan yayi kama da bikin kalankuwa a al’adar
Hausawa ta dauri.
Kusan tun zamanin shugaban Amerika na farko George Warshington ake yin
wannan biki a hukumance, inda wasu kan shirya gangami tare da fadakarwa da
wayar da kan jama’a, wasu kuma kan zagaya domin barka da wannan rana, wasu kuma
kan zauna a gida su dagargaji naman talo-talo da sauransu. A mafiya yawancin
jihohin Amerika ana yin wannan biki, sai dai yakan sha-bamban daga wannan waje
zuwa wannan waje.
Amerikawa suna taran wannan rana ne da wasu muhimman abubuwa, misali wasu
kan canza sabuwar mota a wannan rana, wasu kuma kanyiwa gidajensu sabon fenti,
ko dasa sabbin furanni, wasu kuma kancanza ilahirin abubuwan da suka mallaka,
da suka hada da kayan sawa, gadaje da kujeru, talabijin, kwamfuta da sauransu.
Haka kuma, akan yiwa gidaje da wuraren shakatawa ado da furannin roba masu kawa
da kuma abun falfali da sauran kayan zayyana masu daukar ido.
Shaguna da kantuna da kasuwanni da guraren hada-hadar yau da kullum sukan
kasance a garkame a wannan rana. Da yawan ‘ya ‘yan da suka jima a wajen cirani
sukan zo su gaida iyayansu suyi hira da su, su tattauna labarun bayan rabuwa,
haka kuma, sukan raba kyaututtuka ga junansu da suka hada da kwamfutar tafi da
gidanka, wayar hannu, na’urar sauraron kade-kade da sauran dangin kayan
latironi, har ila yau kuma, sukan yi musayar kayan tande-tande wadan da ake
nannadewa a cikin wata irin leda ta musamman a saka acikin kwali.
Akanyi dafe-dafe da ciye-ciye sosai a wannan rana. Babban abinda aka fi ci
domin bikin wannan rana shine tsun-tsayen Talo-talo, a kafatanin kasar Amerika
akan yanka talo-talo sama da miliyan biyar domin yin ragadada aci tare da ‘yan
uwa da iyalai da kuma abokanai sannan kuma akanci kayayyakin itatuwa da suka
hada da ayaba da mangwaro da kuma matsatststun kayan marmari.
Amerikawa sun dauki wannan rana a matsayin ta hutu, dan haka basu zuwa
guraran ibada ko wajen fastoci. Sabanin sauran kasashen da suka kwai-kwayi
wannan al-adar ta gargajiyar Amerika, inda ake dunguma zuwa majami’u da
ikilishiyoyi domin yin ibada.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
No comments:
Post a Comment