Shugaba Obama
Zai Gudanar Da Garambawul A Fadar White House
Shekarunki 8 kina first
lady, sannan kin kara wasu shekaru takwas a majalisar dattabai haka kuma, kin
samu shekaru hudu kin matsayin sakatariyar harkokin wajen Amerika; dan haka
yanzu lokaci ya yi da zaki koma gida ki ci gaba da dafawa mijinki abinci. Ana sa
ran nan bada jimawa ba shugaban Obama na Amrika zai yi wani garambawul mai
girma a cikin gwamnatinsa dan sake shimfida mulki a karo na biyu, wannan
garambawul zai yi awon gaba da Madam Hillary Rodham Clinton inda ake sa ran
jakadiyar Amerika a majalisar dinkin duniya Dr Susan Rice zata maye gurbin
Hillary a fadar white house, wata majiya kuma na hasashen tsohon dan takarar
shugaban kasa Sanata John F Kerry zai maye gurbin Hillary.
Sannan Babban sakataren baitul malin Amerika Mista
Tim Gierthner shima wannan sauyi zai yi awon gaba da shi, inda ake sa ran
shugaban ma'aikatan fadar white house Dr. jack Lew zai maye gurbinsa. Sannan
shima babban sakataren tsaron Amerika Mista Leon Panetta da babban mashawarcin
tsaro Tom Danilon da mataimakinsa Denis McDonough duk suma wannan sauyi
zai yi awon gaba da su. Kusan wadannan sune manyan jami'an gwamnatin Obama a
shekaru hudu da suka gabata.
No comments:
Post a Comment