Julius Kambarage
Nyerere: Shugaba Mafi Kima A Afurka
Julius Nyerere kamar yadda aka
fi saninsa shine shugaban kasar Tanzaniya na farko, ya zama shugaban kasa tun
kasar tana amsa tsohon sunanta na Tanganyika. An haifi Nyerere a ranar 13 ga
watan Afrilu a shekarar 1922 a kauyan Butaima, mahaifinsa cif Zanaki mutumin
kirki ne da ake girmamawa, Nyerere ya fi shahara da sunan “Mwalimu” wanda a
yaren Suwahila yake nufin “Malami”. Bayan da ya yi karatu a jami’ar Makere da
ke kampala a kasar Uganda ya wuce jami’ar Edingbugh a kasar Burtaniya, daga nan
ya dawo gida ya zama malamin makaranta.
Kasancewar Nyerere mutum mai
kima a idanun jama’a wannan ya bashi damar sanin jama’a sosai da kuma zama tare
da tattaunawa da mutanansa domin basu shawarwarin yadda zasu warware
matsalolinsu na rayuwa. A shekarar 1954 ya jagoranci kafa wata jam’iyyar siyasa
mai suna Tanganyika African National Union, an zabe shi a matsayin Prime
Minista a shekarar 1961 a wannan lokacin ya kasance shugaban kasar tanganyika
na farko. A shekarar 1964 ya ci nasarar hade kan tsiburin Zanzibar da
Tanganyika inda suka zama kasa daya wadda aka radawa suna TANZANIYA, haka kuma
a shekarar 1967 ya kaddamar da shirin nan na Tanzaniya ta dogara da kanta wanda
aka fi sani da Arusha Declaration.
Nyerere ana kwatantashi da
mutum mai tsananin kishin al’ummarsa da kuma Nahiyar Afurka. Yayi matsakaiciyar
rayuwa a lokacin da yake shugaban kasa. Shuagab Nyerere dai bai zakewa turawa
ba kamar sauran shugabannin Afurka, a mafiya yawancin lokuta baya boye akidarsa
dangane da yadda turawa suka yi kaka-gida a nahiyar Afurka, sannan ya
kalubalanci prime ministan Burtaniya Harold Wilson da Ian Smith akan 'yancin
kasar Rhodesiya wadda ake kira Zimbabwe a yanzu, a saboda haka ne yafi kusanci
da kasar chana sama da sauran kasashen yamma, amma sunyi zaman lafiya da
tsohuwar rusashshiyar Tarayyar Sobiya da sauran kasashen duniya, musamman masu
adawa da mulkin danniya na turawan mulkin mallaka. Haka kuma, yana daya daga
cikin mutanan da suka jagoranci samun 'yancin kasashen Zambiya da Botsuwana da
Muzambique da Angola da kuma Rhodesiya ko Zimbabwe. Nyerere ya taba zuwa
Najeriya har fadar mai martaba sarkin Kano a zamanin mulkinsa.
Shugaba Nyerere ya sauka daga
shugabanci bisa radin kansa a shekarar 1985 domin ya koma ci-gaba da
matsakaiciyar rayuwarsa. Ana bayyanashi a matsayin wani mutum mai kaifin Harshe
da iya magana, shugaba Nyerere yana da kima sosai a idon takwarororinsa
Shugabannin Afurka, ya rasu a shekarar 1999 ba tare da ya mallaki ko da filin
da zai gina gida ba. Turawa suna yi masa kirari da mutum mai gaskiya da rikon
amana a lamuransa. Nyerere yana daga cikin shugabannin Afurka da suke da kima
ainun.
Yasir Ramadan Gwale.
No comments:
Post a Comment