Sunday, November 25, 2012

PDP DA ZABEN 2015


PDP DA ZABEN 2015

Buba wata hadaka da 'yan Hamayya zasu iya yi da zata kawar da PDP a matakin zaben Shugaban kasa. Ya kamata 'yan Najeriya mu gayawa kanmu gaskiya, Bahaushe ya ce shirin zaune yafi na tsaye, tabbas PDP suna da cikakken shiri da tsari na cigaba da mallakar kujerar shugaban kasa a Najeriya ko talakawa sunso ko basu so ba. 'Yan Hamayya kullum labari suke bayarwa cewa zasu yi hadakar da zata kawo karshen PDP, wanda wannan abu shafu labari ne. A Najeriya talauci ba karya bane, Talauci gaskiya ne, jama'a na fama da talauci a birane da kauyuka, PDP suna da kudin da zasu sayi kuri'u dan samun zabe kuma za'a sayar musu, duk mutumin da zai je masallaci ya saci takalmi ko Agogo, ko matar da zata je gidan biki ta zari takalman mutane bana jin za'a sayi kuri'unsu lokacin zabe suki sayarwa. Sannan ga jama'a da suke fama da kuncin tunani a birane da kauyuka sannan ga talauci ya yi musu daurin butar malama.

Tabbas Zabe ba shine zai kawo karshen Mulkin PDP a Najeriya ba. Idan da gaske muke son gyara ko dai 'yan Najeriya su dunguma su koma PDP, Bahaushe ya ce Sarkin Yawa yafi sarki karfi Alabashshi su samar da wanda suke so ya zama shugaban kasa ta karfi da yaji, ko kuma 'yan Najeriya su yi bore irin wanda ya kawar da Hosny Mubarak a Masar, ko kuma su cigaba da hakuri cikin Mulkin PDP. Amma indai zabe ake nufin zai kada PDP to lashakka za'a jima zaben bai kada PDPunba.

A kwanakin baya anyi zaben gwamna a Ondo wanda jam'iyyar Labour ta lashe wanda daman ita ke jan ragamar mulkin jihar. Kowa yasan cewa PDP ta tsayar da dan takarara kuma ya sha kaye a hannun gwamna me ci Mimiko, wannan ko shakkau ba ba wani abun mamaki bane, domin sanin kowa ne a zaben shugaban kasa da ya gabata Jami'yyar Labour ta fito fili balo-balo ta nuna goyon bayanta a zaben shugaban kasa da cewa su PDP suke yi, dan haka abun da ya faru a Ondo ramawa kura aniyar ta ne, PDP basu ki su fadi zabe a kowacce jiha ba, matukar sune suke da kujerar Shugaban kasa.

A 'yan kwanakin da suka gabata Majalisa ta zauna a kowacce mazabu a Najeriya domin jin ra'ayoyin 'yan Najeriya dangane da kundin tsarin mulki da za'ayiwa kwaskwarima. Wannan jin ra'ayi ya sake tabbatar da cewar 'yan Najeriya ba a shirye suke domin samun gyara ba. Idan muka buga misali da kanmu a Arewa su waye suka zauna suka shirya wani kuduri kwakkwara da da sunan Arewa wanda zai lalubo hanyoyin da zamu fita daga halin da muke ciki na kaka naka yi? Amsar ita ce babu, Ina malamai? Ina 'yan Boko? Ina tsaffin shugabanni? Duk kowa ya kame hannunsa sai aka bar 'yan Siyasa zallah da matasan da basu san inda Najeriya ta sanya a gaba ba, wai ra'ayinsu za'ayi amfani da shi a gyaran rayuwarmu ta nan gaba. Kaico!

Rahotannin da suka biyo bayan wannan jin ra'ayin sun nuna, babu wani guri da aka samar da wata kyakykyawar natija da sunan Arewa, 'yan daba da 'yan shaye-shaye kusan sunci kasuwarsu yadda suke so! Magana fa ake ta rayuwamaru gaba daya. idan har da gaske muke me yasa bamu yiwa wannan jin ra'ayi cikakken shiri ba, me ya sa bamu rufe kasuwanni da makarantu ba, limamai da ladanai da masu unguwanni da hakimai da dagatai da shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da sauran al'umma su fito kwansu da kwarkwatarsu ba? Muna tsammanin kowa yana can yana harkokinsa gyara zai zo? Duk wanda ya zaci haka to ya fahimci kuskure. A masar mata da maza suka bar gidajansu da kantunansu da makarantansu da guraran ayyukansu, suka zo filin ALLAH suna kiran sai shugaba Mubarak ya tafi, Bahaushe ya ce komai girman doka taron jama'a ya fita, babu girma babu arziki Mubarack ya kama gabansa.

Mu sani mu kara sakankancewa babu wani gyara da zai zo, alhali kowa ya kama gabansa. Dole sai mun fito mu duka mun taru munce ga abinda muke so sannan zamu samu. Amma abin haushi da takaici a wasu guraran wannan jin ra'ayi bai yuwuba, saboda 'yan jagaliya sun hana kuma ya hanu, amma da yau liman ya fito mai unguwa da sauran jagororin al'umma sun fito, shin kana jin akwai wani marar kunya da zai kawo wargi a wajen? Wallahi gyara bai taba zuwa cikin lalaci da san jiki da jin dadi ba. Mahtuma ghandi sai da yayi tafiya a kasa ta sama da mul 250 domin neman 'yanci, har hakarsu ta cimma ruwa.

Sannan kuma, Sakamakon zaben da akayi a jihohin Kebbi da Adamawa ya kara tabbatar da cewar duk balakoko da hayagaga da 'yan Arewa suke akan neman canji zance ne kawai. Domin babu wani abu da ya sauya, kuma haka za'ayi ta tafiya har zuwa 2015. Dama daya 'yan Arewa suke da ita ya zuwa yanzu, shine takawa Shugaban kasa Goodlock Burki daga tsayawa takara a zabe mai zuwa, sannan su samar da dan Arewa wanda zai tsayawa PDP takara. Amma matukar muka ce zamu kada PDP da Jam'iyyar Hamayya to wallahi wannan tatsuniya muke yi, zaben shugaban kasa jam'iyyun Hamayya ba da gaske suke ba, dan babu wani abu da ya nuna cewa da gaske akeyi. Kuma mu 'yan Arewa dole mu sani cewa zaben shugaban kasa ba zai taba cuwuwa a Arewa ba, idan ana cin zaben kenan. Idan kuma ana maganar satar zabe to PDP sunyi shal ALLAH ya kiyaye.

Yasir Ramadan Gwale

No comments:

Post a Comment