Wednesday, November 14, 2012

Yuwuwar Juyin Juya Hali A Najeriya



Yuwuwar Juyin Juya Hali A Najeriya

Najeriya kusan ita ce kasar da muka fi kowace sanin halin da take ciki, amma ban taba jin labarin wata kasa da ake irin abinda ake yi a Najeriya ba. Hakika abin na Najeriya ya wuce munshairin, shugabannin suna mahaukaciyar sata da ta shallake hankali da tunanin dan adam mai lafiyayyan hankali, ga kazamin cin-hanci da rashawa da ya dabaibaiye kusan Dukkan wasu harkoki a Najeriya, babu maganar bangaren gwamnati da bangaren ‘yan kasuwa duk inda ka latsa abin daya ne, kawai sai dai wani yafi wani muni, ko kuma gwargwadon yadda kudi ke zirga-zirga.

A Najeriya ne kadai inda ake irin wannan mahaukaciyar satar kuma a ringa yabawa barayin da suka dibga irin wannan sata. Misali tsohon shugaban hukumar kula da tashashin jiragen ruwa ta Najeriya Olabode George da manajan darakta Aminu Dabo da mukarrabansu sun tafka wawar gararuma da dukiyar kasa da ta kai kusa Naira Biliyan 85, amma da aka tabbatar da laifinsu kuma kotu ta dauresu shekaru biyu kacal, wai lokacin da zasu fito daga kaso, sai ga jama’a sunyi tururwa wajen taryansu daga gidan sarka, wannan babban abin takaici ne da rashin sanin ‘yancin kai da wawanci, idan ba haka ba, tayaya mutanan da kowa yasan laifinsu shine sun yiwa kasa sata aka daure su amma jama’a na tururwa wajen yi musu san barka, sai ka kasa fahimta shin muran ake taya su sunyi sata ko kuwa me?

Haka kuma, kamar yadda rohoto na baya bayan nan wanda kwamatin da gwamnati ta kafa karkashin tsohon shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin kasa ta’annati EFCC Malam Nuhu Robadu akan ya binciko badakalar da ake yi da kudadan man-fetur, kuma sunyi bankada mai girman gaske, wanda kuma alamu suka nuna ana neman yiwa wannan rahoton bita da kulli. Shi dai rahoton na Malam Nuhu Ribadu ya ce antafka kazamar sata a harkar man-fetur inda ya ce ansace kudi sama da Naira Tiriliyan 2.8 Hasbinallahu wani’imal Wakeel! Sai gashi tun lokacin da shugaban yake gabatar da rahoton binciken nasa aka nemi a yiwa abin kafar ungulu, domin daga cikin ‘yan kwamatin wanda alamu suka tabbatar da cewar daman an saka su ne domin su yiwa rahoton yankan baya, sai mataimakin shugaban kwamatin wanda bayanai suka tabbatar da cewar ko sau daya bai-taba halartar zaman kwamatin ba sai daga karshe yazo yana cewa wai rahoton yayi tsauri! Saboda kawai kwamatin ya zargi iyayan gidansa da rubdaciki da dukiyar kasa.

Wannan aiki na bankada da kwamatin Malam Nuhu Ribadu ya yi wani muhimmin al’amari ne. Domin da farko lokacin da aka bayar da sanarwar kafa wannan kwamiti karkashin Jagorancin Ribadu, ‘yan Najeriya da yawa sunga wallensa cewa daman amfani gwamnati ta yi da shi a zaben da ya gabata. Duk da cewar Ribadun ya sha nanata cewa wannan batu karya ne, jama’a basu yarda da shi ba, sai yanzu da ya yi wannan bankada mai girman gaske a harkar man-fetur jama’a ke yaba masa tare da nuna cewa ya yi kokari wajen wannan aiki.

Tabbas a Najeriya barayi bazasu daina sata ba. Domin matukar akwai dumbin arzikin mai a Najeriya to kuwa suma barayin suna nan sun bude bakin jakunkunansu domin jidar dukiyar kasa suje su boye a kasashen waje. Bangaren da yafi kowa ne bangare muhimmanci a Najeriya shine bangaren Shir’ah amma harkar rashawa da cin-hanci tayi masa daurin gwarmai. Sai kayi mamakin harkar shar’ah a Najeriya inda ta dosa, a Najeriya ne kotu mai alkalai ta wanke tsohon gwamnan jihar delta James Ibori cewa mai gaskiya ne, tsarkakakke ne daga Dukkan zargin cin-hanci da halarta dukiyar haram, amma abin mamaki kuma sai gashi kotu a kasar Burtaniya ta kamashi da laifi kuma ya amsa laifinsa. Anan ne mutum zaiyi tambaya anya kuwa a Najeriya kotuna shari’un da suke yi na gaskiya ne kuwa? Domin mutumin da kotu ta tsarkake shi daga zargin halatta kudin haram, sai gashi kuma kotu a wajen Najeriya ta ce yana da laifin halatta dukiyar haram kuma ya amsa da bakinsa cewa haka ne! Wannan yake kara nuna babban abin tsoro dangane da harkar shari’ah a Najeriya.

Dan haka lokaci yayi da ‘yan Najeriya zasu fito su yaki wannan mummunan cin hanci da rashawa da ci da gumin talakawa. Sanin duk dan Najeiya ne cewa halin da ake ciki na matsin rayuwa da kamfar kudi a hannun talakawa ya kai magaryar tukewa, su kuma wadannan miyagu azzalumai da sunan masu rike da madafun iko basu da wata niyya ta daina wannan satar, bil-hasali ma har gasar sayan jirage suke yi da kudin da suka sata, to dan haka ya zama dole al’ummar kasa su yi fito-na-fito da miyagun masu mulki.

Kamar yadda muka samu labari halin matsi da kuncin rayuwa ya sanya bore wa shugabannin kasashen larabawa wanda ya yi awan gaba da shugabannin ‘yan kama karya irinsu Hosny Mubarack a Masar da Zainul Abiden Ben Ali a Tunisiya da Ghaddafi a Libya da kuma irinsu Ali Abdallah Saleh a Yeman. Lalli duk wani hali na matsi da al’ummar wadan-can kasashe na larabawa suka shiga nafila ne akan abinda yake faruwa a Najeriya, dan haka mune a hakku mu fito muyi Allah-wadarai da wadannan gungu na azzaluman masu mulki.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment