Saturday, September 26, 2015

Turmutsutsun Munna Laifin Saudiyya Ne


TURMUTSUTSUN MUNNA LAIFIN SA'UDIYYA NE?

Wannan ita ce irin kururuwar da Iran da 'yan kanzaginta suke yi, kuma suke kiran dole Sa'udiyya ta dauki alhakin duk abinda ya faru rasa rayukan da akai a wannan turmutsutsu. Kafafan yada labarai na Iran sunyi ta kawo rahotannin wata zanga zanga da akai a Tehran, masu muzaharar na kiran Musulmin duniya su tashi su kalubalanci Sa'udiyya akan wannan hadari da ya auku, wanda rahotannin da suke fitowa a hankali, suka nuna cewar da gayya mutanan Iran suka sabbaba turereniyar. Haka kuma, wasu bayanai da ba na hukuma ba sunce sama da mutanan Iran 400 suka sheqa barzahu a yayin wannan cikowwa da suka yi silar aukuwar ta. 

Wato abin mamaki ne a wannan lokaci Iran suyi uwa su yi makarbiya akan wannan kira, suna kira akan lallai Sa'udiyya ta dau alhaki game da wannan rasuwa. Sun manta dukkan irin ta'addanci da kisan kiyashi da Azzalumin Shugaban Syria Bashar  Assad yake yi, basu taba kiran sa da ya dauki alhakin duk mutanan da suka rasu a kasar ba. Amma da yake su ba masu adalci bane, kuma ba masu son zaman lafiya bane, kullum burinsu cusawa Musulmi kiyayyar Sa'udiyya  da nuna musu gazawar kasa mai tsarki wajen tafiyar da harkokin addini. Da kamata yayi Iran su yi kira ga Bashar Assad ya dauki alhakin dukkan abinda ya faru a Syria, nan ne zamu fahimci cewar wannan kururuwar da suke ba ta Iblis bace.

Allah ya sakawa Mamlakatul Arabiyatus Sa'udiyya da Alkhairi a bisa irin wannan hidima da suke basa gajiyawa. Sun samar da jami'an tsaro 100,000 domin laura da tsaro a yayin aikin Hajji,  suka samar da Kyamarori 5000 da aka kakkafa a duk inda ake aikin Hajji dan samun tsaro, baya ga aikin taimakon gaggawa da bayar da magani kyauta ga Mahajjata da kula da duk marasa lafiya kyauta, da motocin daukar marasa lafiya masu jiran ko-ta-kwana sama da guda dari, ga tsarin sufuri kyauta cikin nutsuwa, ga abinci da ruwan zamzam duk kyauta, Bugu da kari, ga Alqur’ani kyauta ga kowanne Mahajjaci da littattafan Musulunci cikin harsuna da dama. Duk wannan dama wasu ayyukan alkhairi da ban fado ba, duk ba wani abin yabawa bane a wajen Iran da 'yan kanzaginsu. 

Ba suda aiki kullum sai kokarin bankado inane Kasar Sa'udiyya ta gaza suyi suka ba wai su bada shawara a gyara ba. Dan haka kada wannan abun ya baka mamaki, mutanan da suka zagi Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam suka tozarta Nana Aisah uwar Muminai, wadda Manzon Allah yace a duniya ba wanda yake so sama da ita da mahaifinta, dan haka ba wani abin mamaki bane dan wadannan mutane sun zagi iywlan Al Saud. Dan haka, Sa'udiyya ba zata dauki alhakin abinda ba tada alhaki akai ba, idan ya so mutanan Iran da 'yan kanzaginsu  su koma Karbala da Najaf da yin Aikin Hajjinsu. Kasa Mai Tsarki Ta Sa'udiyya In sha Allah tana karkashin kariyar Allah Subhanahu Wata'ala, Iran da kawayenta da dukkan masu mara mata baya da 'yan kanzaginta zasu ji kunya In sha Allah. Allah ka taimaki Musulunci da Musulmi ka kunyata makiya ka tozarta su, ka hana Shiah sakat. Allah ka jikan Musulmi na hakika hakika a duk inda suke.

Yasir Ramadan Gwale 
26-09-2015

No comments:

Post a Comment