Tuesday, September 15, 2015

SA'UDIYYA: Sarki Salman Bin Abdulaziz Ya Biya Diyyar Hadarin Makkah


SA'UDIYYA: SARKI SALMAN YA BIYA DIYYAR HADARIN HARAMIN MAKKAH 

Kafafan yada labarai na Sa'udiyya sun ruwaito Sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud ya bayar da umarnin biyan diyya ga duk wanda ya rasu a hadarin Haramin Makkah da ya auku ranar Juma'ar makon jiya. Sarkin ya bada umarnin baiwa iyalan duk wanda ya rasu a sanadiyar wannan hadari Riyal Miliyan daya, kimanin Naira Miliyan 60, haka kuma, Sarki Salman ya bayar da umarnin biyan duk wanda ya jikkata zunzurutun kudi Riyal 500,000. Kimanin Naira Miliyan 30. Bugu da kari, kuma Sarkin ya ce duk wanda jinya ta hana shi yin aikin Hajji a wannan shekara, ya dauki nauyinsa ya dawo Shekara mai zuwa domin sauke Farali. 

Ba shakka wannan labari ne mai dadin ji da faranta rai, muna addu'ah ta musamman ga Sarki Salman akan Allah ya saka masa da alheri ya kara masa lafiya da nisan kwana. Wannan alama ce ta tausayi da jin kai da dattako. Allah ya taimaki Sa'udiyya kasa mai tsarki. Masu yiwa Sa'udiyya mummunan fata da masu cewa ita ba kasar mai tsarki bace sai su mutu da bakin ciki da damuwa. Allah ya taimaki Musulunci da Musulmi ya kaskantar da Shiah da masu mara mata baya da 'yan kanzaginsu. 

Yasir Ramadan GwaleGwale
15-09-2015

No comments:

Post a Comment