Tuesday, September 8, 2015

GWAMNA GANDUJE: Birnin Kano Na Bukatar Manya Manyan Lambatu Ba Jirgin Karkashin Kasa Ba


GWAMNA GANDUJE: BIRNIN KANO NA BUKATAR MANYA MANYAN LAMBATU BA JIRGIN KARKASHIN KASA BA 

A kwanakin baya muka jiyo Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta fara wani shiri da wani kamfanin kasar China dan samar da jirgin karkashin kasa a cikin birnin Kano, wanda aka ce zai ci biliyoyin kudade. Wannan yunkuri ne mai kyau, kuma cigaba ne ga jihar Kano,  idan an samar da tsari mai kyau. Domin a yadda alamu suka nuna wannan aiki ka iya zama barna da asarar dukiyar al'umma matukar aka kauda kai ga wasu ayyuka da suke na wajibi kuma muhimmai. Dan zai zama asarar dukiya a lokacin da Gwamnati ta kyale cikin birni babu manya manyan Lambatu na zamani da ruwa zai iya kwaranyewa a lokacin damuna irin wannan ba. Domin daga karshe wannan rami da za ai na titin karkashin kasa sai ya zama katuwar kwata lokacin damuna.

Kamar yadda al'umma suka shaida kuma suke gani, a wannan damuna ta wannan shekara, an samu ambaliyar ruwa a unguwannin cikin birnin Kano da dama da suka hada da Gwangwazo da Adakawa da Zaria Road da BUK Road da Kwana hudu da sauran unguwanni da yawa. Wannan kuma ya faru ne sakamakon rashin manya manyan Lambatu na karkashin kasa, wadan da ruwa zai bi ya kwaranye ba tare da ya cika gidajen mutane ba. Kusan yanzu manyan Birane na duniya haka ake tsarin samar da irin wannan Lambatu din. A dan haka ne muke kira ga mai girma Gwamna, da lallai ayi yunkurin samar da manyan Lambatu dan kaucewa ambaliyar ruwa a cikin birni da ke haifar da rushewar gidaje da asarar dukiyoyin al'umma.

A gaskiya  kwalbatocin da ake da su a yanzu basu wadatar ba, kuma galibinsu kan-kana ne, sannan al'umma kan cike su da shara a mafi yawancin lokuta. Dan haka, samar da irin wadancan manya na karkashin kasa zai taimaka ainun wajen rage asarar kudin da ake na gina kananan kwalbatoci duk Shekara. Kusan ya zama kamar al'adar Gwamnatocin kananan hukumomi, kamar ba suda wani aiki sai gina Lambatu da ba suda zurifi kuma ba suda inganci  basa iya jimawa basu lalace ba. Muna fatan Gwamna zai sauya wancan yunkuri na jirgin karkashin kasa,  zuwa ga samar da Manya manyan Lambatu na karkashin kasa a cikin birni. Allah ya kare asarar dukiya da rayukan al'umma a yayin wannan ambaliyar ruwa da ake samu a cikin birnin Kano. 

Yasir Ramadan Gwale
08-09-2015 

No comments:

Post a Comment