HADARIN MAKKAH DA HALIN MUTANAN AFURKA
Ba shakka abin da ya faru a jiya na rasuwar sama da mutum 700 a hanyar su ta zuwa jikan Jamra abin tashin hankali ne da ban tsoro. Muna addu'ah Allah ya jikan wadan da suka rasu a sanadiyar wannan hadari, masu raunuka kuma Allah ya basu lafiya. Kana kuma, Allah ya saka wa hukumomin Sa'udiyya bisa yadda basa gajiyawa wajen samar da tsarin gudanar da aikin Hajji cikin nutsuwa da kaucewa afkawa hadarin da ana iya kauce masa. Allah ya yi musu sakamako na alkhairi akan wannan aikin alheri da suke babu dare babu rana.
Wannan hadari na jiya, ba irin sa ne karon farko ba a wannan waje, hasalima a Shekarar 1996 an samu hasarar rayuka sama da 1000 a sanadiyar turmutsutsu da Alhazai kan yi a wajen jifan Jamra. Wannan ta sanya hukumomin Kasa Mai Tsarki basu yi kasa a guiwa ba wajen fadada wajen jifa da kuma kokarin kaucewa samun mugun cinkoson da zai kai ga hasarar rayuka.
A bayanan da ba na hukumomi ba ya nuna cewar wannan hadari ya faru ne da mafiya yawancin mutanan Afurka bakake, sakamakon kaucewa bin tsarin shiga da fita a wajen jifa. Ance a dadi mafi yawa na wadan da suka rasu mutanan mu ne, muna kara adduar Allah ya jikan su ya gafarta musu. A dan haka, tilas ne mu sake lale a yanayin yadda muke gudanar da rayuwarmu ta rashin bin doka da ka'Ida.
Wannan hoton da na saka na samo shi ne daga turakar facebook ta Malam Ibraheem I. Waziri. Haka kuma, karara wannan hoto ya nuna halin irin namu na rashin bin tsari da dokar duk wani abu da ake so ya kasance cikin doka da oda, kamar yadda kuke gani a wannan hoto, hanya ce an tsara ga ta inda mutane zasu bi, amma sai suka kaucewa bin hanyar da aka tsara suka kirkiri ta su Sabuwa abinda ya janyo mutuwar ciyayin da aka shuka a wajen dan ya bada kaye.
Wata rana Malamin Sheikh Abdulwahab Abdallah Imam Ahlussunnah Wal Jama'ah yake cewa "bisa la'akari da halayenmu, kai kace mu bakaken mutane an haliccemu ne dan mu karya doka, da yin komai gaban kanmu" ba shakka wannan magana ta Malaminmu haka take, domin yanayin mu yayi kama da na al'ummar da bata san bin tsari da doka da oda. Wanda kamar yadda yake, bin doka da oda shi ne, wayewa, burgewa, cinyewa, rashin bin doka kuwa ba shakka shi ne ci baya, da koma bayan tunani.
Irin wannan rashin san bin doka namu, ba abu bane da za'a zargi wasu mutane ace sune ke da laifi, abu ne da kusan ko ina haka muke, kowa na karya doka mai sauki musamman ta hanya da babu mai kula da masu bin ka'Ida. Malami da Dan Boko da Limamai da dalibi da mabiya duk munyi tarayya wajen rashin bin doka da oda. Ka shiga unguwannin mu, kaga yadda muke rayuwa, bamu da tsarin magudanun ruwa masu kyau, bamu da tsarin zubar da shara mai kyau.
Kai sabida tsabar rashin kan gado da rashin bin doka, takai mutum mai hankali babba ba yaro ba zai hau tsakiyar randabawul (Roundabout ) ya kwaye al'aurarsa yana fi tsari ko ba-haya a lokacin da mutane ke tsaka da harkokin yau da kullum, na taba ganin haka a shataletalen 'yan kura dake kasuwar Sabon Gari a Kano. To wannan fa kadan ne na irin halayyar mu ta rashin san bin doka da oda. Abin Mamaki shi ne, mutane sun zama kamar birrai burinsu karya dukkan tsari, da hukuma zata ware makewayi na jama’a dan biyan bukatar larura wallahi idan ka shiga sau daya ba zaka so ka kuma shiga ba. Ka shiga dukkan wani makewayi na kowa-da-kowa dake Ma'aikatu da Jami'o'i da makarantu zaka sha mamaki inda masu Ilimi da hankali ke yin ba-haya a kasa ba tare da sunbi ka'Ida na yadda ya kamata ayi ba.
Misalin irin haka suna da yawa a cikin rayuwarmu, dan haka, tilas da ni da kai mu sanyawa kanmu dokar bin dukkan wata ka'Ida da muka ci karo da ita a ko inane. Abin mamaki da yawa ma sun dauka rashin wayewa ne mutum ya tsaya bin ka'Ida, idan mutum ya cika san yin komai bisa tsari sai ya zama abin zargi, ana ce masa ya cika kakale ko shi dan Boko ne, ko wani zance na aibantawa.
Haka kuma, ya zama tilas a sanya shi a tsarin jadawalin karatu wajen cusawa al'umma bin doka da oda da yin da ' a ga dukkan dokoki da suka shafi muhalli da rayuwa dan kaucewa tashin hankalin da ana iya kauce masa. Allah ka sa mu zama shiryayyar al'umma mai bin doka da oda, mai kiyaye ka'Ida. Wadannan bayin Allah da suka rasa rayukan su a wannan hadari Allah ya jikan su ya gafarta musu, Allah ya yafe musu laifukan su.
Yasir Ramadan Gwale
25-09-2015
No comments:
Post a Comment