Monday, September 14, 2015

Mugun Nufin Su Ba A Kan Kasa Mai Tsarki Ta Sa'udiyya Ya Tsaya Ba


MUGUN NUFIN SU BA A AKAN KASA MAI TSARKI TA SA'UDIYYA YA TSAYA BA 

Daga lokacin da aka wayi gari, Musulmi wad’an da ba larabawa ba, suna matukar nuna k’yama ga Sa’udiyya da sauran larabawan gabas ta tsakiya, ko dai dan zugar da ake musu, ta karya, wai  Larabawa bisa jagorancin Saudiyya sunki taimakawa masu gudun hijra daga Syria, ko a nuna musu Sarakunan Sa'udiyya ba ruwansu da addini, o wata magana me kama da haka, idan mutane sukai kuskuren daukar wannan zugar, kiyayyar mutane tayi nisa akan Saudiyya da kuma Larabawa, a dalilin abinda ke faruwa a Syria, ko yarfen ba ruwansu da addini, to me yayi saura kuma? 

Sai a wayi gari an cusawa mutane kin Addinin Allah basu sani ba, domin matakin farko shi ne,  na kin masu addini (Larabawa-Saudiyya) domin a lokacin da kaji kana matukar kyamar mutum, to daga nan zaka fara kin duk wani abu nasa, idan kana kyamar mutum ko sadaka yayi sai kace ai Riya ce, idan yayi dariya kace ai Yak'e ne. To wannan shi ne hakikanin Barbarar Tunanin da Shiah da miyagun mutane daga Yammaci da gabashin duniya da ‘yan kanzaginsu daga cikin ‘yan Boko da basu san komai ba game da addini ko Larabawa ko Saudiyya ake musu wannan barbarar tunanin. 

Da yawansu, ba abinda suke sai k’ak’ale da kokarin ganin laifin Saudiyya, da nuna su masu fashin baki ne, ko a Washington ko a Cairo ko a Nairobi ko a Abuja suke, duk an musu barbarar tunani ne, daga zarar sunyi Magana sai jahilcinsu ya bayyana akan abinda suke kalubalanta, alhali basu sanshi ba. Abin da mamaki kaga mutum yana matukar nuna kyama ga Sa'udiyya da sauran larabawa haka kurum, alhali baya nuna irin wannan kyama ga fadar Vatican ko Israeli, amma zai yi dukkan rubuta dan ya munana KASA MAI TSARKI TA SA'UDIYYA. Mun yadda mun gamsu Saudiyya da sauran larabawa da Sarakunan su, ba ma’asumai bane, suna da laifuka irin nasu, kuma suna da tarin alkhairai masu yawa. A dan haka muke kaddara cewar Alkhairinsu ya rinjayi kishiyarsa a gani na zahiri a wajenmu, a sabida haka ne, bama ganin kasawarsu, muke yin duba zuwa ga alkhairinsu a koda yaushe.

Shiah anyi mata birki taki karbuwa dan haka basu da wani aiki da suke tunanin samun Nasara face kokarin dasawa mutane aqidar kin Saudiyya tare da kin Addini. Eh, haka ne, ba dan komai ba, sai dan suna gaba da addinin Allah, da masu riko da addini. Suna fatan ganin yawaitar fasadi a ban kasa. Ai masu wannan kanzagi da iya gano tare da kalubalantar Saudiyya tabaransu baya iya nuno musu duk wani Alkhairi nasu, mutum yaje Umara yaci gurasarsu yasha Laban din su, sai ya zo facebook yace ai basa son addini, kaji jahili! Haka kuma, basu iya gano abinda ke faruwa a C.A.R bare su nuna kiyayya ga kasar Santaral Afurka ba bisa yadda aka gallazawa Musulmi aka kokkoresu daga gidajensu, aka tilasta musu barin garuruwansu, tare da mai da su ‘yan gudun hijra; basu iya ganin halin da aka jefa Musulmi a Myanmar ko Burma ba, bal cewa ma suke ai Aung San Suu Kyi 'yar Demokaradiyya ce, basa ganin wani abin ki a tare da gallazawar da akewa Musulmi a kasar.

Dan haka, al’umma su fadaka kada wasu masu wankakken tunina irin na Iraniyawa, barbarar yanyawa su rudesu da iya zance da nuna musu cewar ai duk abinda ke faruwa na kwarar ‘yan gudun hijirar Syria laifin Saudiyya ne ko Larabawa,  wannan ba gaskiya bane, tsabar k'eta ce da mugun sharri. Sai mu tambaya, Ita Iran din me tayi na taimakawa Syriawan? Allahumma Rudda Kaiduhum Alaihim. 

Yasir Ramadan Gwale
14-09-2015

No comments:

Post a Comment