SHUGABANCI A SUDAN: BANGARANCIN DA YA HAIFAR DA YAKIN DARFUR
A Sudan Shugaban kasa da mataimakinsa, sun fito daga kabila daya, jiharsu daya garinsu daya. Abokaine tun suna yara, tare suka shiga aikin soja tare suka yi juyin mulki, tare suka kafa Gwamnati. Wannan tsabar san kai da nuna fifiko na daya daga cikin dalilan da suka sabbaba rikici a wasu yankuna na kasar, musamman mutanan da suke ganin kabilar Ja'alyiyya ta Shugaba Umar Hasan Albashir ko mutanan yankinsa na Shamaliyya sun mamaye komai na harkar tafiyar da Gwamnati.
Wannan batu na mamayar madafun iko da mutanan yankin Shugaba Albashir suka yi, shi ne jigo kuma kashin bayan rikicin yankin Darfur dake yammacin Sudan, duk da cewar akwai siyasa mai tarin yawa a ciki da kuma cakuda karya da gaskiya akan batun. Bisa radin kansa mataimakin Shugaban kasa wanda ake yiwa kallon shi ne Khalifa bayan Albashir, abokinsa ne kuma shakikinsa, Ali Usman Muhammad Taha aka wayi gari yayi murabus daga kan mukaminsa.
Har ya zuwa yanzu babu wasu tabbatattun dalilan da suka bayyana hakikanin dalilin Murabus din Taha, illa shaci fadi na manazarta. Sai dai bayan Murabus din Taha an sake maye gurbinsa da wani mutum daga yankin shamaliyya na Shugaba Albashir dake Arewacin Sudan. Ustaz Hasabu Muhammad Abdurahman shi ne mutumin da ya zama sabon mataimakin Shugaban kasa bayan murabus din Ali Usman Muhammad Taha.
Yasir Ramadan Gwale
29-08-2015
No comments:
Post a Comment