Thursday, September 3, 2015

MASU SUKAR NADE-NADEN SHUGABA BUHARI SUNA KAN TURBA MAI KYAU


MASU SUKAR NADE-NADEN SHUGABA BUHARI SUNA KAN TURBA MAI KYAU 

A hakikanin gaskiya har yanzu ina jin zafin kisan gillar da Inyamurai suka yiwa Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto da ma irin kisan da aka yiwa Murtala Mohammed. Ban san su ba, ban taba ganin su ba, amma ba shakka naji zafi kuma raina ya so su  yadda naji tarihi ya karantamin irin kisan da akai musu ba da Hakki ba. Watakila da Inyamurai basu kashe wadannan gwaraza ba da tuni  yankin Arewa baya cikin halin da yake ciki na koma baya ta kowanne fanni a yanzu. Na kan tambayi kaina, da ace su Tafawa Balewa da su Ahmadu Bello da su Murtala Mohammed da su Malam Aminu Kano suna raye har kawo wannan lokacin da wanne irin cigaba nake zaton Nigeria take ciki, da watakila matsalolin da ake kuka da su da mu da muka zo daga baya ba zamu taba saninsu ko wani abu mai kama da su ba.

Inyamurai sun cuce mu a zaman tare da Allah ya hadamu, sun kashe mana iyaye, suka cusa mana haushi, suka bakanta mana, sannan suka mamaye mana kasuwanni, suka turasasa mana sayen hajojinsu 'yan jabu a wasu lokutan. To ba mu da yadda zamu yi, Allah ne yaga dama ya hadamu zaman tare a kasa daya, dan haka ya zama tilas a garemu mu koyi yadda zamu zauna da juna lafiya, tare da yiwa juna adalci a duk lokacin da muka samu dama. A ganina zamu zauna lafiya ne da mutanan kudu a lokacin da suka yi mana fahimta ta gaskiya cewa mu mutanan Arewa ba azzalumai bane, ba ha'intarsu zamu yi a zamantakewar mu da su ba! Ya za ai su yi mana wannan fahimtar? Muna zamu bada dama ta hanyar tafiya tare da su a gwamnatance,  Ba mamaki ba wai fahimtar mu ne basu yi ba, illa tsabar Hassada da da kyashi da kiyayya da gaba da suke da ita garemu. Allah shi ne masanin abinda ya faku a garemu.

Game da yadda wasu ke sukar Shugaban Kasa Buhari akan rashin nada Inyamuri dan kudu maso gabas ko dan kudu maso kudu a mukamin sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ni kam banga laifin Buhari ba, sannan masu sukar hakan suma suna kan turba. Domin kuwa, mukamin sakataren Gwamnati babban mukami ne, kuma shi ne zuciyar Gwamnati, dan haka Shugaban kasa na da hakkin ganin ya nada mutumin da zai kiyaye masa amana ba tare da ya tozarta ta ba. Masu suka kuwa, musamman daga Arewa, suna nuna hakikanin halin mutumin Arewa na tausayi da jin kai da rashin san babakere da handama, suna da ra'ayin ayi Gwamnati ne da zata tafi da kowa tare, wanda wannan tunani ne mai kyau, kuma abin a yaba ne.

Abinda da yawan mutane musamman masoya Buhari suka manta shi ne, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan siyasa ne, kuma siyasa ce ta kawo shi kujerar Shugaban kasa. Dan haka siyasa ce ta bada damar kalubalantarsa a bisa yadda yake tafiyar da Gwamnati, dan haka zai zama koma baya da dakushewar tunani mutane su dinga ganin laifi ne a kalubalanci Shugaban kasa Buhari a siyasance, har kaji wasu na zagi da cin mutunci dan an soki manufofinta Gwamnatin siyasa. Hamayya ko Adawa a siyasa wajibi ne, domin hakan shi ne ya bambanta mulkin siyasa da na kama karya irin na soja.

Shugaban kasa Buhari shi ne mutumin da Allah ya danka amanar Najeriya a hannunsa, wadan da suka zabe shi da wadan da basu zabe shi ba. Kuma, tabbas ne a ranar gobe kiyama sai Allah ya tambaya shi akan yadda ya tafiyar da mulkin Najeriya. Muna masa fatan cin wannan jarabawa, haka kuma, Allah ba zai tambayi Buhari me yasa bai bawa Inyamurai sakataren Gwamnati ba, illa zai tambaya shi idan bai yi musu adalci ba. Yana da kyau, Shugaban kasa, ya haska wa al'umma musamman wadan da basu zabe shi ba, cewar shi shugaba ne na kowa ba wani sashi ba.

Haka kuma, ba yadda muka iya dole mu zauna da juna lafiya indai ana zaman tare a Najeriya. Ya zama tilas mu da Inyamurai da sauran kabilun kasarnan mu nunawa juna cewar zamu iya adalci a duk lokacin da muka samu shugabanci, dole a samu zullumi a duk lokacin da wani sashi suke ganin kamar ba za ai musu adalci ba, imma ta hanyar rabon mukamai ne ko ta hanyar tafiyar da Gwamnati, dan haka babban kalubalen da yake kan Shugaban kasa shi ne, ya gamsar da Inyamurai da sauran kananan kabilu cewar ba zai musu rashin adalci ba a matsayinsa na Shugaban kasa.

Bayan haka, ya zama dole a duk lokacin da aka ga Gwamnati na yin wasu abubuwa na nuna wariya a kalubalance ta, domin wannan shi ne Demokaradiyya kuma shi ne mulkin siyasa. Dan haka, masu kalubalantarsa  (Shugaban kasa) da nad'e nad'ensa  suna kan turba mai kyau, domin haka siyasa ta gada, kuma shi kansa Shugaban kasa ya shafe kusan shekaru 12 yana kalubalantar salon Mulkin Gwamnatin PDP da ya shud'e. Allah ya taimaki Najeriya.

Yasir Ramadan Gwale 
30-08-2015

No comments:

Post a Comment