Tuesday, September 8, 2015

IBRAHIM BABANKOWA: Mutum Na Farko Da Ya Gano Gawar Tafawa Balewa Ya Kwanta Dama


IBRAHIM BABANKOWA: MUTUM NA FARKO DA YA GANO GAWAR TAFAWA BALEWA YA KWANTA DAMA

Yau muka wayi gari da labarin rasuwar Malam Ibrahim Ahmed Babankowa, wanda fitaccen mutum ne a Kano da Najeriya baki daya. Ba shakka rashinsa babban rashin ne kwarai. Domin daya ne daga cikin sauran 'yan mazan jiya da suka rage, sai dai yau shima ya amsa kiran mahaliccinsa, muna masa fatan tafiya cikin sa'a. Sai dai tarihi ba zai mance da Babankowa ba, bisa gano gawar Marigayi Firaministan Najeriya Tafawa Balewa da yayi bayan juyin mulkin 1966. Ga yadda abin ya faru, kamar yadda ya taba shaidawa Jaridar Vanguard:

Yadda Babankowa ya gano gawar Tafawa Balewa, bayan juyin mulki da kisan gilla da akai masa. Babankowa ya shaidawa Jaridar Vanguard abinda ya faru kamar haka: Kamar yadda Jaafar JaafarJaafar ya hakaito mana:

Babankowa: Na kasance Sango-Ota har wajen 15 ga Janairun 1966. Lokacin da aka yi juyin mulkin farko a Najeriya. A daren ranar da akai wannan juyin mulki, ina wajen binciken ababen hawa a Sango Ota a jihar Ogun, muna bakin aiki sai muka ga Kwambar motocin soji sun zo sun wuce ta gabanmu, akwai mota kirar Landroba da Fijo guda biyu da kuma wata Kanta. Sun fito daga Legas suka nufi Abekuta. A lokacin bamu zargi wani mugun abu ka iya faruwa ba kasancewar munga sojoji ne a cikin kaki, sai muke zaton ko zasu je aiki da ya shafi tabbatar da doka ne.

Abin da ban sani ba shi ne, ashe wadannan motoci dauke suke da Firaministan Najeriya zasu halaka shi. Mune mutane na karshe da muka ga gilmawar wadannan sojoji da kuma Firaminista a tare da su bamu sani ba. Daga baya muka fahimci, wadannan motoci sun tsaya kamar kilomita uku daga inda suka barmu. Suka shiga wani daji dake kusa da hanya, anan ne wadannan sojoji suka kashe Firaminista Tafawa Balewa da Okotie Eboh da sauran mutanen da ke tare da su. Wannan ya faru ne a daren Juma'ar 15 ga Janairun 1966 ranar da akai wannan juyin mulkin.Kamar awa daya da ta shige sai muka ga wadannan sojoji sun sake dawo sun nufi Legas. Bayan da gari ya waye ne muka fahimci cewar anyi juyin mulki.  Saidai rudani ya biyo bayan rahotannin da suke nuna cewar an dauke Firaminsta daga gidan sa zuwa wani waje da ba'a sani ba.

Vanguard: Ya akai ka gano inda aka yasar da gawar Firaminista?

Babankowa: eh, na gano ta ne bayan kwana hudu da wannan da yin wannan juyin mulki. Naje wajen wani Sha-Katafi dake Sango Ota, dan na karbi magani, a lokacin wannan sha-katafi shi ne kadai asibiti a wannan yanki. Anan  ne na saurari wasu marasa lafiya, cikin harshen Yarabanci, suna cewar akwai wani mugun doyi da suke ji a inda ke makwabtaka da su, amma basu san meye ke wannan doyin ba. Daga baya sai na gane cewar wadannan marasa lafiya dake wannan magana sun fito ne daga wani kauye dake kan hanyar Abekuta kusa da inda muka duba ababen hawa kwana hudu da suka shude.

Vanguard: Ya kayi da ka ji wannan batu?

Babankowa: Ina jin haka sai na sauya yanayin aikin namu. Na kasa ma'aikatanmu gida biyu, na tura runduna daya ta shiga yankin da muke zargi dan mu bincika, ta haka ne muka kawo zuwa ga wannan daji da aka kashe aka kuma yasar da gwarwakin su Firaminista. Abinda babu kyan gani ainun.

Vanguard: Me kuma kuka gano bayan nan?

Babankowa: Naga gawar Firaminista yashe a kasa ta fara rubewa, sannan naga gawar Minista Okotie da Kur Muhammad da kanar Abogo Largema da wasu mutum biyu. Na kadu matuka da ganin wadannan gawarwaki yashe a karkashin bishiya!  A sabida haka na yi gaggawa na sanarwa da Insfekta na 'yan sanda ta hanyar wani caji ofis dake Ikeja, dan sanda dake gurin Alhaji Kafaru Tinubu shi ya sadani da IG mukai magana. Na shaida masa cewar nagani kuma na shaida gawar Firaminista da wasu mutane a cikin daji. Daga nan ne na jira naji umarnin da za'a bani. Muna cikin wannan yanayi, ashe Insfekta yana hutu, wanda yake madadinsa shi ne Alhaji Kam-Salem. Daga nan aka bani umarnin kai tsaye na wuce babbar shalkwatar tsaro ta kasa dake Legas. Sabida bukatar gaggawa da ake na zuwa na, aka ce nayi amfani da jiniya idan na shigo Legas dan nayi sauri.

A lokacin da na isa Legas, tuni an bada sanarwa cewar Janar Aguiyi Ironsi ya karbe ragar ikon Gwamnati a matsayin Shugaban kasar Soja na farko. Har Aguyi Ironsi ya kaddamar da kansa a Shalkwatar tsaro dake Moloney. Isata wajen ke da wuya, natarar da wasu sojoji da suke jiran isowata, suka karbe dukkan kayan da suke tare da ni da suka hada da karamar bindiga da babba, suka kwabe mun takalmi da bel din da ke daure a kwankwaso na da hulata. Aka sanya ni gaba babu takalmi babu hula ba bel. A haka na isa ofis din Insfekta, isata ke da wuya sai natarar da Aguyi Ironsi zaune kusa da Alhaji Kam-salem. Ba wanda yayi mun magana can sai Gen. Aguyi Ironsi ya tambayeni cikin harshen Hausa, "ka ce kaga gawar Firaminista Balewa da ta wasu mutane"? Na amsa masa da cewar, eh haka ne. Ya sake tambaya ta, ta yaya akai kasan Firaminista? Na ce masa, nayi aiki da Sardauna a matsayin dogarinsa, kuma Sardauna da Balewa abokaine na kud-da-kud, dan haka na san Firaminista sosai.

Vanguard: Me kuma ya faru daga nan?

Babankowa: Daga nan aka sake fita da ni, inda Aguyi Ironsi ya bayar da umarnin a tsare ni a Naval Base dake Apapa, amma sai Insfekta yace, idan ba zaka damu ba ranka ya dade zamu tsare shi anan shalkwata, zamu gabatar da shi a duk lokacin da ka bukaci hakan. Gen. Ironsi ya karbi shawarar Kam-Salem suka cigaba da tsare ni a wajen. Can da tsakar dare, sai ga dogarin Firaminista Mista Kaftan wanda surikin Tafawa Balewa ne yazo da motar daukar gawa, da kuma wata kanta dauke da akwatunan daukar gawarwaki. Suka nemi a sake ni domin na jagorance su zuwa inda aka kashe su Firaminista.

Vanguard: Me ya faru da kuka je dajin?

Babankowa: Muna zuwa muka ga kumburarriyar gawar Firaminusta yashe a karkashin bishiya da hularsa zanna tana gefensa na dama. Yana sanye da farar kufta me alkyabba wanda tuni ta canza kala zuwa launin jini. A lokacin nan gawar Firaminista tuni ta fara zagwanyewa  har ta fara tsutsotsi! Daga nan ne muka nannadeta da farin kyalle, haka nan na tallefe shi akan cinya ta saboda mu nade gawar duka. Mune mutanan farko da muka fara zuwa kan gawar Firaminista. Da aka gama nadewa aka sanya gawarsa a akwatu, sai nayi mata alama da Larabci dan kar a kasa gane ta. Daga nan muka nufi sashin saukar manyan baki na filin jirgin saman Legas, inda muka taras da wasu kananan  jirage guda biyu suna jiranmu. Daga nan muka saka gawar Furaminista a jirgi tare da wasu danginsa dan zuwa Bauchi ayi mata sutura.

Isarmu Bauchi ke da wuya muka gabatar da gawarsa ga iyalansa. Babu wanda zai iya yiwa wannan gawa wanka a lokacin, kamar yadda addini ya shar'anta, sabida duk ta rube gaba daya kuma ta fara zagwanyewa! Haka nan mukai masa Sallah, aka bunne gawarsa. Hasbunallahu Wani'imal Wakeel! Wannan bakin tarihi ne da ba zamu taba mancewa da shi ba, an cutar da mu a zaman tare a kasarnan, Allah ka biwa wadannan bayin naka hakkin jinin su.

Marigayi Ahmad Ibrahim Babankowa shi ya baiwa jaridar Vanguard wannan labari mai matukar tayar da hankali. Ba shakka Inyamurai sun cucemu, Allah ya isa bamu yafe ba. Allah ya jikan Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello. Allah ya kai haske kabarinsu. Shima marigayi Ibrahim Babankowa muna yi masa adduar fatan alheri, Allah ya jikansa ya gafarta masa yasa aljannah ce makomarsa. Muna mika ta'aziyarmu ga iyalansa musamman Sani Babankowa Allah ya yafe masa.

Yasir Ramadan Gwale
08-09-2015

No comments:

Post a Comment