HALIN DA BASHAR ASSAD YA JEFA AL'UMMAR KASARSA TA SYRIA A CIKI
Hoton wannan yaron Aylan Kurdi dan Syria wanda igiyar ruwa ta tunkudo gawarsa gabar ruwan Turkiyya kusan shi ne abinda yafi daukar hankalin manyan Kafafan yada labarai a Gabas ta tsakiya da sauran duniya. Wannan hoto yana cike da tausayi matuka, duk mai Imani dole zuciyarsa ta raurawa idan yaga hoton wannan yaro. Ba shakka Shugaban Syria Bashar Assad da ya jefa iyayan wannan yaro har hakan yayi salwantar rayuwar sa ta irin wannan hanya mugu ne, kuma Azzalumin shugaba, abin takaici ne kuma abin Allah wadai. Bashar Assad ya cika a kirashi babban Azzalumin wannan karnin.
Bayan ya rushe kasar, ya kashe dubunanna al'ummar da basu san hawa ba basu san sauka ba, dawwamarsa a Mulki tafi dukkan rayukan mutanan Syria muhimmanci a wajensa. Mutanan kasar sun tarwatsa a duniya sun zama almajirai suna bi kwararo-kwararo suna neman abin da zasu Ci, basa mallakar komai sai kayan jikinsu. Hasbunallahu Wani'imal Wakeel, Ya Allah kayi mana sutura! Ba shakka wannan al'amari na Syria fitina ce gagaruma a wannan zamanin. Amma Allah yayi bushara ga masu hakuri wadan da suke maida komai zuwa ga kaddarawarsa Subhanahu Wata'ala.
Tambayar da mutane da yawa suke yi ita ce, me yasa kasashen yankin Gulf ko Khaleej da suka hada da Sa'udiyya da Qatar da Kuwait da Daular Larabawa da kuma Bahrain suka kasa taimakawa wadannan 'yan gudun hijra. Amsar wannan tambaya tana da sarkakiya da kuma bukatar kallon abinda ya faru tun farkonsa har ya zuwa yanzu, da kuma yanayin Siyasar Gabas ta tsakiya da Sarautar Sarakunan Gulf.
A bisa gaskiyar zance shi ne, kasashen Gulf da na zayyana, sune suke samar da kaso mafi rinjaye na kudaden da ake taimakawa wadannan 'yan gudun hijira a sansanoninsu dake Lubnan da Turkiyya da Jordan da tsirarun da ke Masar da Sudan. Haka kuma, abinda wasu zasu ce, shin me yasa wadannan mutane suke gudu tare da rige rigen shiga kasashe Turai maimakon kasashen Gulf su basu mafaka a yankinsu na Larabawa? Anan, wajen amsa wannan tambaya, akwai siyasa mai yawa da ta yiwa wannan batu tarnaki da dabaibayi. Da kuma sanin hakikanin siyasar mulkin Sarakunan wannan yanki.
Abinda yake faruwa shi ne, su wadannan kasashe na Gulf, suna bin tsarin Mulkiyya ne na Sarauta kamar yadda kowa ya sani, a dan haka, a dukkan wani abu da zai faru a Gabas ta tsakiya wadannan kasashe suna kallon komai da tsoron zai iya tasiri a sha'anin tafiyar da mulkinsu, ko kuma ma zai iya zama katuwar barazanar rugujewar mulkin nasu, dan haka ne, sukan fara duba bukatun siyasar mulkinsu akan komai. Kullum tsoron da Gulf suke ji shi ne abinda zai taba musu mulkin su, ko menene kuwa. Shi yasa duk da Alkhairan da rusasshiyar Gwamnatin Muhammad Mursi ta zo da shi, suka gwammace juya masa baya, dan suna ganin cigaba da wanzuwar Mursi barazana ne a garesu da mulkinsu.
Haka kuma, yana daga cikin abinda yake zamarwa kasashen Gulf barazana shi ne batun mamayar da baki 'yan kasashen waje sukai musu, misali Hadaddiyar Daular Larabawa ko UAE dake da yawan mutane wajen Miliyan 9.346 kusan kashi 80 baki ne suka mamaye su, haka kasar Qatar da mutanan ta basu wuce Miliyan 3 ba, amma baki 'yan kasashen waje sun kai kashi 90. Haka nan, Sa'udiyya dake da mutane wajen Miliyan 28 akwai baki 'yan kasashen kusan sama da Miliyan 7, idan kaje Kuwait ma haka batun yake, balle kuma Bahrain da Iran take jin kamar wata jiha ce daga cikin jihohin ta.
Dan haka, kullum abin da kasashen suke kallo shi ne, barazana ce babba baki 'yan kasashen waje su mamaye musu kasashe. Domin hakan ka iya zama silar rugujewar mulkin da Masarautun wadannan kasashe suke yi. Kada ka dada Kada ka rage wannan ita ce siyasar mulkin da kullum Gulf suke tsoron tabuwarta, domin a tare da su akwai babbar abokiyar gaba, wadda kullum take yi musu fatan masifar da bala'i, wannan kasa ita ce IRAN, wadda ta zama wani mugun gyambo a tare da kasashen Gulf.
A dan haka, kamar yadda kowa ya sani kasar Syria kasa ce da take da 'yan Shiah masu yawa, adan haka, yadda kasar ta rikice a yanzu idan Sa'udiyya ko Qatar ko Bahrain suka bayar da dama 'yan gudun hijirar Syria su fantsamo kasashen su, to babu makawa k'ulli za a yi da mugun zare, domin Sa'udiyya kanta tana fama da barazanar 'yan Shiah wadan suke daukar zugar Iran, haka nan kuma, Shia tare da goyon bayan Iran zasu shiga Bahrain domin karbe kasar daga hannun Ahlussunnah.
A saboda haka, wannan barazana ta tabuwar mulkin Sarauta na wadannan kasashe da kuma batun da Iran take da shi na ganin ta karbe ikon wadannan kasashe ya tashi daga hannun Ahlussunnah ya koma gun Shia shi ne yakan hana kasashen Khalij bayar da damar mutanan Syria su shigo musu kasashe domin neman mafaka, dan haka ne mutanan Syria suka Gwammace su ketara Teku su shiga kasashe Turai dan samun ingantacciyar rayuwa. Buguzum da kari Syria ba wata muhimmiyar kasa bace a Gabas ta tsakiya.
Amma mutane da yawa sabida san rai basa ganin laifin Assad da ya tilastawa kansa dawwama a Mulki koda mutanan Syria zasu kare, sannan basa kallon irin rawar da Iran take takawa wajen ganin Assad ya cigaba da kasancewa shugaba ta kowanne hali. Sannan duk wannan soki burutsu da masu baiwa Iran kariya suke basu taba tambayar shin tunda Gulf sun kasa me yasa ita Iran ta kasa taimakawa da wadannan 'yan gudun hijira ko da da kaifa da bargo ba ne?
Ba shakka, duk da wannan uzuri da kasashen Gulf suke da shi, halin da Siriyawa suke ciki a yanzu ya dace su dubesu da idon tausayi da jin kai da makwabtaka da 'yan uwantaka. Haka nan, wasu masu sharhi da yawa suna ganin Gulf ba suda wata hujja gamsasshiya da zata hanasu bude kofofinsu ga Siriyawa. Ba shakka, wannan gagarumar fitina da mutanan Siriya dama Khaleej suke ciki, Allah ne kadai zai iya yaye musu kunci da takaici da suke ciki. Ya Allah ka shiga cikin al'amarin mutanan Syria. Allah ka kawo karshen zalincin Bashar Assad.
Yasir Ramadan Gwale
04-09-2015
Allah dai yasa musa dace,Amma kasashen gabas ta tsakiya basu tabuka komai akan wannan matsalar,..saboda abin da kunya ace yan gudun hijira ga kasashen.larabawa amma na turawa suke tafiya duk da wulakanci da suke fuskanta.
ReplyDeleteA ra ayina saudiya tana da muhimmiyar rawa da zata taka Amma taki. ,
as far as i am concern,saudi govt is an integral part of the problem in the middle east