Wednesday, September 30, 2015

Kiyayyarsu Ga Saudiyya


KIYAYYAR SU GA SAUDIYYA

Bama shakkar kasancewar wasu daga cikin Larabawa masu matukar nuna bambanci da wariyar launin fata. yanayin launinmu bakake, da farare wata hikima ce ta Allah. Amma mafiya yawan masu zagin Sa'udiyya ba suna yi bane, domin nuna kyama ga bambanci launin fata, illa suna nuna matukar kiyayyarsu gareta ne sabida kasancewarta, Daula ta SUNNAH da suka tsaya tsayin daka wajen yada tauhidi da kadaita Allah da Bauta.

Wannan wani mugun ciwo ne, da ya tsayawa Iran a makoshi, shi ysa kullum burinsu kambama duk wani abu na kuskuren mamlaka, domin jefa kiyayyarta a zukatan usulmi wadan da Ba larabawa, wanda hakan yana bayuwa ne zuwa ga kiyayyar Addini. Suna mugun kin Sa'udiyya basa sonta, sabida abinda suke kira WAHABIANICI.

Mu kuma muka ce munji mun gani, mu din Wahabiyawa ne, cikin makiya ya kumbura ya fashe. Da damansu wallahi ba zasu iya bayyana cewar su SHIAH suke yi ba, sabida sun san karya ce, bata ce, kuma ba addini ba. Shi yasa a koda yaushe suke fakewa da kankanan abubuwa domin bayyana kiyayyarsu a fili.

Ba zaka sha mamaki, sai ka taba Iran nan zaka ga martani ta ko ina. Mu kuma mun san karya ne, Iran Jamhuriyya ce ta Shedanu da shedanci babu wani Alkhairi ko kadan a tare da su, banda farirci da kafurci da nesanta mutane ga barin Addini. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, bai gushe ba yana adduar Allah ka fishshemu dariyar makiya. Allah ka maida musu kaidinsu garesu.

Yasir Ramadan Gwale
30-09-2015

Saturday, September 26, 2015

Turmutsutsun Munna Laifin Saudiyya Ne


TURMUTSUTSUN MUNNA LAIFIN SA'UDIYYA NE?

Wannan ita ce irin kururuwar da Iran da 'yan kanzaginta suke yi, kuma suke kiran dole Sa'udiyya ta dauki alhakin duk abinda ya faru rasa rayukan da akai a wannan turmutsutsu. Kafafan yada labarai na Iran sunyi ta kawo rahotannin wata zanga zanga da akai a Tehran, masu muzaharar na kiran Musulmin duniya su tashi su kalubalanci Sa'udiyya akan wannan hadari da ya auku, wanda rahotannin da suke fitowa a hankali, suka nuna cewar da gayya mutanan Iran suka sabbaba turereniyar. Haka kuma, wasu bayanai da ba na hukuma ba sunce sama da mutanan Iran 400 suka sheqa barzahu a yayin wannan cikowwa da suka yi silar aukuwar ta. 

Wato abin mamaki ne a wannan lokaci Iran suyi uwa su yi makarbiya akan wannan kira, suna kira akan lallai Sa'udiyya ta dau alhaki game da wannan rasuwa. Sun manta dukkan irin ta'addanci da kisan kiyashi da Azzalumin Shugaban Syria Bashar  Assad yake yi, basu taba kiran sa da ya dauki alhakin duk mutanan da suka rasu a kasar ba. Amma da yake su ba masu adalci bane, kuma ba masu son zaman lafiya bane, kullum burinsu cusawa Musulmi kiyayyar Sa'udiyya  da nuna musu gazawar kasa mai tsarki wajen tafiyar da harkokin addini. Da kamata yayi Iran su yi kira ga Bashar Assad ya dauki alhakin dukkan abinda ya faru a Syria, nan ne zamu fahimci cewar wannan kururuwar da suke ba ta Iblis bace.

Allah ya sakawa Mamlakatul Arabiyatus Sa'udiyya da Alkhairi a bisa irin wannan hidima da suke basa gajiyawa. Sun samar da jami'an tsaro 100,000 domin laura da tsaro a yayin aikin Hajji,  suka samar da Kyamarori 5000 da aka kakkafa a duk inda ake aikin Hajji dan samun tsaro, baya ga aikin taimakon gaggawa da bayar da magani kyauta ga Mahajjata da kula da duk marasa lafiya kyauta, da motocin daukar marasa lafiya masu jiran ko-ta-kwana sama da guda dari, ga tsarin sufuri kyauta cikin nutsuwa, ga abinci da ruwan zamzam duk kyauta, Bugu da kari, ga Alqur’ani kyauta ga kowanne Mahajjaci da littattafan Musulunci cikin harsuna da dama. Duk wannan dama wasu ayyukan alkhairi da ban fado ba, duk ba wani abin yabawa bane a wajen Iran da 'yan kanzaginsu. 

Ba suda aiki kullum sai kokarin bankado inane Kasar Sa'udiyya ta gaza suyi suka ba wai su bada shawara a gyara ba. Dan haka kada wannan abun ya baka mamaki, mutanan da suka zagi Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam suka tozarta Nana Aisah uwar Muminai, wadda Manzon Allah yace a duniya ba wanda yake so sama da ita da mahaifinta, dan haka ba wani abin mamaki bane dan wadannan mutane sun zagi iywlan Al Saud. Dan haka, Sa'udiyya ba zata dauki alhakin abinda ba tada alhaki akai ba, idan ya so mutanan Iran da 'yan kanzaginsu  su koma Karbala da Najaf da yin Aikin Hajjinsu. Kasa Mai Tsarki Ta Sa'udiyya In sha Allah tana karkashin kariyar Allah Subhanahu Wata'ala, Iran da kawayenta da dukkan masu mara mata baya da 'yan kanzaginta zasu ji kunya In sha Allah. Allah ka taimaki Musulunci da Musulmi ka kunyata makiya ka tozarta su, ka hana Shiah sakat. Allah ka jikan Musulmi na hakika hakika a duk inda suke.

Yasir Ramadan Gwale 
26-09-2015

Thursday, September 24, 2015

Hadarin Makkah Da Halin Mutanan Afurka


HADARIN MAKKAH DA HALIN MUTANAN AFURKA 

Ba shakka abin da ya faru a jiya na rasuwar sama da mutum 700 a hanyar su ta zuwa jikan Jamra abin tashin hankali ne da ban tsoro. Muna addu'ah Allah ya jikan wadan da suka rasu a sanadiyar wannan hadari, masu raunuka kuma Allah ya basu lafiya. Kana kuma, Allah ya saka wa hukumomin Sa'udiyya bisa yadda basa gajiyawa wajen samar da tsarin gudanar da aikin Hajji cikin nutsuwa da kaucewa afkawa hadarin da ana iya kauce masa. Allah ya yi musu sakamako na alkhairi akan wannan aikin alheri da suke babu dare babu rana.

Wannan hadari na jiya, ba irin sa ne karon farko ba a wannan waje, hasalima a Shekarar 1996 an samu hasarar rayuka sama da 1000 a sanadiyar turmutsutsu da Alhazai kan yi a wajen jifan Jamra. Wannan ta sanya hukumomin Kasa Mai Tsarki basu yi kasa a guiwa ba wajen fadada wajen jifa da kuma kokarin kaucewa samun mugun cinkoson da zai kai ga hasarar rayuka.

A bayanan da ba na hukumomi ba ya nuna cewar wannan hadari ya faru ne da mafiya yawancin mutanan Afurka bakake, sakamakon kaucewa bin tsarin shiga da fita a wajen jifa. Ance a dadi mafi yawa na wadan da suka rasu mutanan mu ne, muna kara adduar Allah ya jikan su ya gafarta musu. A dan haka, tilas ne mu sake lale a yanayin yadda muke gudanar da rayuwarmu ta rashin bin doka da ka'Ida. 

Wannan hoton da na saka na samo shi ne daga turakar facebook ta Malam Ibraheem I. Waziri. Haka kuma, karara wannan hoto ya nuna halin irin namu na rashin bin tsari da dokar duk wani abu da ake so ya kasance cikin doka da oda, kamar yadda kuke gani a wannan hoto, hanya ce an tsara ga ta inda mutane zasu bi, amma sai suka kaucewa bin hanyar da aka tsara suka kirkiri ta su Sabuwa abinda ya janyo mutuwar ciyayin da aka shuka a wajen dan ya bada kaye.

Wata rana Malamin Sheikh Abdulwahab Abdallah Imam Ahlussunnah Wal Jama'ah yake cewa "bisa la'akari da halayenmu,  kai kace mu bakaken mutane an haliccemu ne dan mu karya doka, da yin komai gaban kanmu" ba shakka wannan magana ta Malaminmu haka take, domin yanayin mu yayi kama da na al'ummar da bata san bin tsari da doka da oda. Wanda kamar yadda yake, bin doka da oda shi ne, wayewa, burgewa, cinyewa,  rashin bin doka kuwa ba shakka shi ne ci baya, da koma bayan tunani.

Irin wannan rashin san bin doka namu, ba abu bane da za'a zargi wasu mutane ace sune ke da laifi, abu ne da kusan ko ina haka muke, kowa na karya doka mai sauki musamman ta hanya da babu mai kula da masu bin ka'Ida. Malami da Dan Boko da Limamai da dalibi da mabiya duk munyi tarayya wajen rashin bin doka da oda. Ka shiga unguwannin mu, kaga yadda muke rayuwa, bamu da tsarin magudanun ruwa masu kyau, bamu da tsarin zubar da shara mai kyau.

Kai sabida tsabar rashin kan gado da rashin bin doka, takai mutum mai hankali babba ba yaro ba zai hau tsakiyar randabawul  (Roundabout ) ya kwaye al'aurarsa yana fi tsari ko ba-haya a lokacin da mutane ke tsaka da harkokin yau da kullum, na taba ganin haka a shataletalen 'yan kura dake kasuwar Sabon Gari a Kano. To wannan fa kadan ne na irin halayyar mu ta rashin san bin doka da oda. Abin Mamaki shi ne, mutane sun zama kamar birrai burinsu karya dukkan tsari, da hukuma zata ware makewayi na jama’a dan biyan bukatar larura wallahi idan ka shiga sau daya ba zaka so ka kuma shiga ba. Ka shiga dukkan wani makewayi na kowa-da-kowa dake Ma'aikatu da Jami'o'i da makarantu zaka sha mamaki inda masu Ilimi da hankali ke yin ba-haya a kasa ba tare da sunbi ka'Ida na yadda ya kamata ayi ba.

Misalin irin haka suna da yawa a cikin rayuwarmu, dan haka, tilas da ni da kai mu sanyawa kanmu dokar bin dukkan wata ka'Ida da muka ci karo da ita a ko inane. Abin mamaki da yawa ma sun dauka rashin wayewa ne mutum ya tsaya bin ka'Ida,  idan mutum ya cika san yin komai bisa tsari sai ya zama abin zargi, ana ce masa ya cika kakale ko shi dan Boko ne, ko wani zance na aibantawa. 

Haka kuma,  ya zama tilas a sanya shi a tsarin jadawalin karatu wajen cusawa al'umma bin doka da oda da yin da ' a ga dukkan dokoki da suka shafi muhalli da rayuwa dan kaucewa tashin hankalin da ana iya kauce masa. Allah ka sa mu zama shiryayyar al'umma mai bin doka da oda, mai kiyaye ka'Ida. Wadannan bayin Allah da suka rasa rayukan su a wannan hadari Allah ya jikan su ya gafarta musu, Allah ya yafe musu laifukan su. 

Yasir Ramadan Gwale 
25-09-2015

Tuesday, September 15, 2015

SA'UDIYYA: Sarki Salman Bin Abdulaziz Ya Biya Diyyar Hadarin Makkah


SA'UDIYYA: SARKI SALMAN YA BIYA DIYYAR HADARIN HARAMIN MAKKAH 

Kafafan yada labarai na Sa'udiyya sun ruwaito Sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud ya bayar da umarnin biyan diyya ga duk wanda ya rasu a hadarin Haramin Makkah da ya auku ranar Juma'ar makon jiya. Sarkin ya bada umarnin baiwa iyalan duk wanda ya rasu a sanadiyar wannan hadari Riyal Miliyan daya, kimanin Naira Miliyan 60, haka kuma, Sarki Salman ya bayar da umarnin biyan duk wanda ya jikkata zunzurutun kudi Riyal 500,000. Kimanin Naira Miliyan 30. Bugu da kari, kuma Sarkin ya ce duk wanda jinya ta hana shi yin aikin Hajji a wannan shekara, ya dauki nauyinsa ya dawo Shekara mai zuwa domin sauke Farali. 

Ba shakka wannan labari ne mai dadin ji da faranta rai, muna addu'ah ta musamman ga Sarki Salman akan Allah ya saka masa da alheri ya kara masa lafiya da nisan kwana. Wannan alama ce ta tausayi da jin kai da dattako. Allah ya taimaki Sa'udiyya kasa mai tsarki. Masu yiwa Sa'udiyya mummunan fata da masu cewa ita ba kasar mai tsarki bace sai su mutu da bakin ciki da damuwa. Allah ya taimaki Musulunci da Musulmi ya kaskantar da Shiah da masu mara mata baya da 'yan kanzaginsu. 

Yasir Ramadan GwaleGwale
15-09-2015

Monday, September 14, 2015

Mugun Nufin Su Ba A Kan Kasa Mai Tsarki Ta Sa'udiyya Ya Tsaya Ba


MUGUN NUFIN SU BA A AKAN KASA MAI TSARKI TA SA'UDIYYA YA TSAYA BA 

Daga lokacin da aka wayi gari, Musulmi wad’an da ba larabawa ba, suna matukar nuna k’yama ga Sa’udiyya da sauran larabawan gabas ta tsakiya, ko dai dan zugar da ake musu, ta karya, wai  Larabawa bisa jagorancin Saudiyya sunki taimakawa masu gudun hijra daga Syria, ko a nuna musu Sarakunan Sa'udiyya ba ruwansu da addini, o wata magana me kama da haka, idan mutane sukai kuskuren daukar wannan zugar, kiyayyar mutane tayi nisa akan Saudiyya da kuma Larabawa, a dalilin abinda ke faruwa a Syria, ko yarfen ba ruwansu da addini, to me yayi saura kuma? 

Sai a wayi gari an cusawa mutane kin Addinin Allah basu sani ba, domin matakin farko shi ne,  na kin masu addini (Larabawa-Saudiyya) domin a lokacin da kaji kana matukar kyamar mutum, to daga nan zaka fara kin duk wani abu nasa, idan kana kyamar mutum ko sadaka yayi sai kace ai Riya ce, idan yayi dariya kace ai Yak'e ne. To wannan shi ne hakikanin Barbarar Tunanin da Shiah da miyagun mutane daga Yammaci da gabashin duniya da ‘yan kanzaginsu daga cikin ‘yan Boko da basu san komai ba game da addini ko Larabawa ko Saudiyya ake musu wannan barbarar tunanin. 

Da yawansu, ba abinda suke sai k’ak’ale da kokarin ganin laifin Saudiyya, da nuna su masu fashin baki ne, ko a Washington ko a Cairo ko a Nairobi ko a Abuja suke, duk an musu barbarar tunani ne, daga zarar sunyi Magana sai jahilcinsu ya bayyana akan abinda suke kalubalanta, alhali basu sanshi ba. Abin da mamaki kaga mutum yana matukar nuna kyama ga Sa'udiyya da sauran larabawa haka kurum, alhali baya nuna irin wannan kyama ga fadar Vatican ko Israeli, amma zai yi dukkan rubuta dan ya munana KASA MAI TSARKI TA SA'UDIYYA. Mun yadda mun gamsu Saudiyya da sauran larabawa da Sarakunan su, ba ma’asumai bane, suna da laifuka irin nasu, kuma suna da tarin alkhairai masu yawa. A dan haka muke kaddara cewar Alkhairinsu ya rinjayi kishiyarsa a gani na zahiri a wajenmu, a sabida haka ne, bama ganin kasawarsu, muke yin duba zuwa ga alkhairinsu a koda yaushe.

Shiah anyi mata birki taki karbuwa dan haka basu da wani aiki da suke tunanin samun Nasara face kokarin dasawa mutane aqidar kin Saudiyya tare da kin Addini. Eh, haka ne, ba dan komai ba, sai dan suna gaba da addinin Allah, da masu riko da addini. Suna fatan ganin yawaitar fasadi a ban kasa. Ai masu wannan kanzagi da iya gano tare da kalubalantar Saudiyya tabaransu baya iya nuno musu duk wani Alkhairi nasu, mutum yaje Umara yaci gurasarsu yasha Laban din su, sai ya zo facebook yace ai basa son addini, kaji jahili! Haka kuma, basu iya gano abinda ke faruwa a C.A.R bare su nuna kiyayya ga kasar Santaral Afurka ba bisa yadda aka gallazawa Musulmi aka kokkoresu daga gidajensu, aka tilasta musu barin garuruwansu, tare da mai da su ‘yan gudun hijra; basu iya ganin halin da aka jefa Musulmi a Myanmar ko Burma ba, bal cewa ma suke ai Aung San Suu Kyi 'yar Demokaradiyya ce, basa ganin wani abin ki a tare da gallazawar da akewa Musulmi a kasar.

Dan haka, al’umma su fadaka kada wasu masu wankakken tunina irin na Iraniyawa, barbarar yanyawa su rudesu da iya zance da nuna musu cewar ai duk abinda ke faruwa na kwarar ‘yan gudun hijirar Syria laifin Saudiyya ne ko Larabawa,  wannan ba gaskiya bane, tsabar k'eta ce da mugun sharri. Sai mu tambaya, Ita Iran din me tayi na taimakawa Syriawan? Allahumma Rudda Kaiduhum Alaihim. 

Yasir Ramadan Gwale
14-09-2015

Sunday, September 13, 2015

SA'UDIYYA: Kasa Mai Tsarki


SA'UDIYYA: KASA MAI TSARKI 

Da farko ina amfani da wannan damar wajen Jajantawa Khadimul Haramain Ash-Sherifain Sarki Salman Bin Abdulaziz da dukkan al'ummar Musulmi bisa wannan ibtila'i da ya faru a Masallacin Allah mai alfarma da ke Makkah a Juma'ar da ta gabata. Ba shakka komai da ke faruwa muqaddari ne daga Allah,  kamar yadda wannan rubzowar da gini ko karfen gini yayi, sanadiyar iska mai karfin gaske tare da ruwan sama mai yawan gaske. Allah Ta'ala Ya jika  wadan da sukai shahada, sun rasu a waje mafi tsarki da daraja a ban-kasa, sannan Allah ya karbi rayuwarsu a daya daga cikin ranaku masu martaba ranar Juma'a a daidai lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi yace sa'ar karshe ta Juma'a lokaci ne mai falala da ake amsa addu'ah, a kuma cikin yanayi na ruwan sama, suna wadan da gini ya fadowa, wanda alama ce ta mutuwar shahada, Allah ya jikan su ya gafarta musu. Allah ya kare aukuwar hakan anan gaba.

Kamar yadda kowa ya sani dakin Allah Mai Alfarma waje ne da ake ibada awanni Ashirin da hudu a kowacce rana, dan haka al'umma daga ko ina a duniya, sukan dunguma su shagala cikin Ibada a wannan waje mai tsarki. Haka kuma, sanin kowa ne cewar fiye da shekaru Goma da suka gabata wannan waje (Harami)  bai taba zama ba'a yin wani aiki da ya shafi gyaran wannan Masallaci a ciki ba, ko dai fadada shi abinda ya shafi kara girman Haraba dan samun sukunin masu Ibada cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da sauran dangin nau'o in siyana. Irin wannan hidimtawa wannan waje da Sarakunan Sa'udiyya sukai abin a yaba musu ne kuma a jinjina musu, kullum kashe kudi ake a wajen nan kamar babu gobe, wadannan mutane basu taba yin bara ko rokon a taimaka musu zasu gyatta wannan waje da ya shafi dukkan Musulmin duniya ba. Wannan kadai abin a cira musu tuta ne, Allah ya saka musu da alheri, ya yalwata arzikinsu, ya basu ikon hidimtawa Musulunci. Wannan duk wani bayani ne da sai wadan da suka saba zuwa zasu fahimci yadda ake kashe wa wannan waje zunzurutun dukiya.

Tare da haka kasar Sa'udiyya bata gaza ba wajen taimakawa al'umma musamman wadan da bala'i ya shafa nan da can. Sunyi kokari matuka wajen sanya farin ciki a zukatan al'ummatai da yawa. Zai zama katon zalinci da rashin tsoron Allah da mugun nufi, wasu 'yan gaza gani, su ce wannan abinda ya faru wai laifin Sa'udiyya ne, wasu kuma suyi kwaskwarima su ce ai kamfanin dake aikin ya kamata a tuhumeshi, wasu kuma suce, me yasa ma ake aikin alhali Alhazai sun fara hallara a Makkah domin ibadar aikin hajj na wannan Shekarar,  wasu ma cewa suke ai dole Sa'udiyya su biya diyyar rayukan da suka salwanta.  Da sauran soki burutsu da yawa da galibi masu barbarar tunani daga Iran suke yi.

Masu wadancan korafi da kalubale, sun mance cewar wannan abu ya auku ne, a lokacin da ruwan sama mai karfin gaske ya sauko tare da iska mai karfi ya haddasa. Wannan abu duk da ana aiki, ba shakka kamfanin dake aikin yayi kokari wajen gudanar da aiki tsawon lokaci ba'a taba samun ta'adi mai yawa irin wannan ba, wanda kai tsaye ba zaka ce laifin ma'aikata bane, domin ba a tsaye kawai kayan aikin suka rubzo ba, ba kuma tsaka da gini ake wasu manyan tubala suka rikito ba. Duk da haka, da kansa Gwamnan Makkah bayan ya zagaya yaga irin adadin da wannan barna tayi, ya bayar da umarnin gudanar da bincike nan take, domin samun ingantattun bayanai dan sanin ko akwai sakaci ko kuwa daga Allah ne. Ba shakka, Gwamnan Makkah ya katse hanzarin 'yan yaga riga masu zakwadi da ganin baikensu,  wanda dama kullum neman gazawarsu ake dan a samu abin fade. Muna kuma da yakini ba zasu kasa biyan diyyar rayukan da aka rasa ba.

Haka kuma, wasu dan tsananin kifewa, sai karaji suke wai ai Sa'udiyya daman ba kasa ce me tsarki ba, Makkah da Madina ne kawai birane masu tsarki a cikinta! To idan kace Sa'udiyya ba kasa bace me tsarki tsammaninka ka rage darajarta a idan wadan da kasar take da kima a wajensu? Shekaru nawa muka taso muka ji ana cewa Sarki Mai Martabar, Sultan Mai Alfarma, Gwamna Mai Girma da sauransu? Shin akwai wani abin damuwa da jin zafi dan an kira Sarki da Mai Martaba shin me yasa baka taba kalubalantar dan me yasa ake kiran Sarkin Musulmi da Mai Alfarma ba,  sannan a kira Sarki da Mai Martaba yayin da ake kiran Gwamna da Maigirma? Shin akwai wani abu da zai ragu daga darajar Sarki dan ba'a kirashi Mai Martaba ba? To wannan fa shi ne tunanin wasu, wai dan me yasa za'a kira Sa'udiyya da kasa mai tsarki. Albashirin masu wannan tunani ko ransu ya so ko Kada ya so, har duniya ta tashi Najeriya da sauran Garbi Ifriqiyya zamu ci gaba da Kiran Sa'udiyya da sunan kasa mai Tsarki idan ya so sai a koma da baya ace karya ne ba kasa bace me tsarki.

Daga karshe, ina tukewa da cewar ko anki ko anso kwalba ita ce uwar turare. Allah ya taimaki Khadimul Haramain Ash-Sherifain Sarki Salman Bin Abdulaziz bisa wannan hidima da suke yiwa Masallatan Allah masu Alfarma na Makkah da Madina. Allah ka daukaka Musulunci da Musulmi, Allah ka kaskantar da Kafurci da Shianci da masu daurewa Shiah gindi da masu mara musu baya da 'yan kanzaginsu, Allah ka kunyata magauta da daukakar Sunnah da Masu taimakawa yaduwar Sunnah.

Yasir Ramadan Gwale 
12-09-2015

Tuesday, September 8, 2015

GWAMNA GANDUJE: Birnin Kano Na Bukatar Manya Manyan Lambatu Ba Jirgin Karkashin Kasa Ba


GWAMNA GANDUJE: BIRNIN KANO NA BUKATAR MANYA MANYAN LAMBATU BA JIRGIN KARKASHIN KASA BA 

A kwanakin baya muka jiyo Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta fara wani shiri da wani kamfanin kasar China dan samar da jirgin karkashin kasa a cikin birnin Kano, wanda aka ce zai ci biliyoyin kudade. Wannan yunkuri ne mai kyau, kuma cigaba ne ga jihar Kano,  idan an samar da tsari mai kyau. Domin a yadda alamu suka nuna wannan aiki ka iya zama barna da asarar dukiyar al'umma matukar aka kauda kai ga wasu ayyuka da suke na wajibi kuma muhimmai. Dan zai zama asarar dukiya a lokacin da Gwamnati ta kyale cikin birni babu manya manyan Lambatu na zamani da ruwa zai iya kwaranyewa a lokacin damuna irin wannan ba. Domin daga karshe wannan rami da za ai na titin karkashin kasa sai ya zama katuwar kwata lokacin damuna.

Kamar yadda al'umma suka shaida kuma suke gani, a wannan damuna ta wannan shekara, an samu ambaliyar ruwa a unguwannin cikin birnin Kano da dama da suka hada da Gwangwazo da Adakawa da Zaria Road da BUK Road da Kwana hudu da sauran unguwanni da yawa. Wannan kuma ya faru ne sakamakon rashin manya manyan Lambatu na karkashin kasa, wadan da ruwa zai bi ya kwaranye ba tare da ya cika gidajen mutane ba. Kusan yanzu manyan Birane na duniya haka ake tsarin samar da irin wannan Lambatu din. A dan haka ne muke kira ga mai girma Gwamna, da lallai ayi yunkurin samar da manyan Lambatu dan kaucewa ambaliyar ruwa a cikin birni da ke haifar da rushewar gidaje da asarar dukiyoyin al'umma.

A gaskiya  kwalbatocin da ake da su a yanzu basu wadatar ba, kuma galibinsu kan-kana ne, sannan al'umma kan cike su da shara a mafi yawancin lokuta. Dan haka, samar da irin wadancan manya na karkashin kasa zai taimaka ainun wajen rage asarar kudin da ake na gina kananan kwalbatoci duk Shekara. Kusan ya zama kamar al'adar Gwamnatocin kananan hukumomi, kamar ba suda wani aiki sai gina Lambatu da ba suda zurifi kuma ba suda inganci  basa iya jimawa basu lalace ba. Muna fatan Gwamna zai sauya wancan yunkuri na jirgin karkashin kasa,  zuwa ga samar da Manya manyan Lambatu na karkashin kasa a cikin birni. Allah ya kare asarar dukiya da rayukan al'umma a yayin wannan ambaliyar ruwa da ake samu a cikin birnin Kano. 

Yasir Ramadan Gwale
08-09-2015 

IBRAHIM BABANKOWA: Mutum Na Farko Da Ya Gano Gawar Tafawa Balewa Ya Kwanta Dama


IBRAHIM BABANKOWA: MUTUM NA FARKO DA YA GANO GAWAR TAFAWA BALEWA YA KWANTA DAMA

Yau muka wayi gari da labarin rasuwar Malam Ibrahim Ahmed Babankowa, wanda fitaccen mutum ne a Kano da Najeriya baki daya. Ba shakka rashinsa babban rashin ne kwarai. Domin daya ne daga cikin sauran 'yan mazan jiya da suka rage, sai dai yau shima ya amsa kiran mahaliccinsa, muna masa fatan tafiya cikin sa'a. Sai dai tarihi ba zai mance da Babankowa ba, bisa gano gawar Marigayi Firaministan Najeriya Tafawa Balewa da yayi bayan juyin mulkin 1966. Ga yadda abin ya faru, kamar yadda ya taba shaidawa Jaridar Vanguard:

Yadda Babankowa ya gano gawar Tafawa Balewa, bayan juyin mulki da kisan gilla da akai masa. Babankowa ya shaidawa Jaridar Vanguard abinda ya faru kamar haka: Kamar yadda Jaafar JaafarJaafar ya hakaito mana:

Babankowa: Na kasance Sango-Ota har wajen 15 ga Janairun 1966. Lokacin da aka yi juyin mulkin farko a Najeriya. A daren ranar da akai wannan juyin mulki, ina wajen binciken ababen hawa a Sango Ota a jihar Ogun, muna bakin aiki sai muka ga Kwambar motocin soji sun zo sun wuce ta gabanmu, akwai mota kirar Landroba da Fijo guda biyu da kuma wata Kanta. Sun fito daga Legas suka nufi Abekuta. A lokacin bamu zargi wani mugun abu ka iya faruwa ba kasancewar munga sojoji ne a cikin kaki, sai muke zaton ko zasu je aiki da ya shafi tabbatar da doka ne.

Abin da ban sani ba shi ne, ashe wadannan motoci dauke suke da Firaministan Najeriya zasu halaka shi. Mune mutane na karshe da muka ga gilmawar wadannan sojoji da kuma Firaminista a tare da su bamu sani ba. Daga baya muka fahimci, wadannan motoci sun tsaya kamar kilomita uku daga inda suka barmu. Suka shiga wani daji dake kusa da hanya, anan ne wadannan sojoji suka kashe Firaminista Tafawa Balewa da Okotie Eboh da sauran mutanen da ke tare da su. Wannan ya faru ne a daren Juma'ar 15 ga Janairun 1966 ranar da akai wannan juyin mulkin.Kamar awa daya da ta shige sai muka ga wadannan sojoji sun sake dawo sun nufi Legas. Bayan da gari ya waye ne muka fahimci cewar anyi juyin mulki.  Saidai rudani ya biyo bayan rahotannin da suke nuna cewar an dauke Firaminsta daga gidan sa zuwa wani waje da ba'a sani ba.

Vanguard: Ya akai ka gano inda aka yasar da gawar Firaminista?

Babankowa: eh, na gano ta ne bayan kwana hudu da wannan da yin wannan juyin mulki. Naje wajen wani Sha-Katafi dake Sango Ota, dan na karbi magani, a lokacin wannan sha-katafi shi ne kadai asibiti a wannan yanki. Anan  ne na saurari wasu marasa lafiya, cikin harshen Yarabanci, suna cewar akwai wani mugun doyi da suke ji a inda ke makwabtaka da su, amma basu san meye ke wannan doyin ba. Daga baya sai na gane cewar wadannan marasa lafiya dake wannan magana sun fito ne daga wani kauye dake kan hanyar Abekuta kusa da inda muka duba ababen hawa kwana hudu da suka shude.

Vanguard: Ya kayi da ka ji wannan batu?

Babankowa: Ina jin haka sai na sauya yanayin aikin namu. Na kasa ma'aikatanmu gida biyu, na tura runduna daya ta shiga yankin da muke zargi dan mu bincika, ta haka ne muka kawo zuwa ga wannan daji da aka kashe aka kuma yasar da gwarwakin su Firaminista. Abinda babu kyan gani ainun.

Vanguard: Me kuma kuka gano bayan nan?

Babankowa: Naga gawar Firaminista yashe a kasa ta fara rubewa, sannan naga gawar Minista Okotie da Kur Muhammad da kanar Abogo Largema da wasu mutum biyu. Na kadu matuka da ganin wadannan gawarwaki yashe a karkashin bishiya!  A sabida haka na yi gaggawa na sanarwa da Insfekta na 'yan sanda ta hanyar wani caji ofis dake Ikeja, dan sanda dake gurin Alhaji Kafaru Tinubu shi ya sadani da IG mukai magana. Na shaida masa cewar nagani kuma na shaida gawar Firaminista da wasu mutane a cikin daji. Daga nan ne na jira naji umarnin da za'a bani. Muna cikin wannan yanayi, ashe Insfekta yana hutu, wanda yake madadinsa shi ne Alhaji Kam-Salem. Daga nan aka bani umarnin kai tsaye na wuce babbar shalkwatar tsaro ta kasa dake Legas. Sabida bukatar gaggawa da ake na zuwa na, aka ce nayi amfani da jiniya idan na shigo Legas dan nayi sauri.

A lokacin da na isa Legas, tuni an bada sanarwa cewar Janar Aguiyi Ironsi ya karbe ragar ikon Gwamnati a matsayin Shugaban kasar Soja na farko. Har Aguyi Ironsi ya kaddamar da kansa a Shalkwatar tsaro dake Moloney. Isata wajen ke da wuya, natarar da wasu sojoji da suke jiran isowata, suka karbe dukkan kayan da suke tare da ni da suka hada da karamar bindiga da babba, suka kwabe mun takalmi da bel din da ke daure a kwankwaso na da hulata. Aka sanya ni gaba babu takalmi babu hula ba bel. A haka na isa ofis din Insfekta, isata ke da wuya sai natarar da Aguyi Ironsi zaune kusa da Alhaji Kam-salem. Ba wanda yayi mun magana can sai Gen. Aguyi Ironsi ya tambayeni cikin harshen Hausa, "ka ce kaga gawar Firaminista Balewa da ta wasu mutane"? Na amsa masa da cewar, eh haka ne. Ya sake tambaya ta, ta yaya akai kasan Firaminista? Na ce masa, nayi aiki da Sardauna a matsayin dogarinsa, kuma Sardauna da Balewa abokaine na kud-da-kud, dan haka na san Firaminista sosai.

Vanguard: Me kuma ya faru daga nan?

Babankowa: Daga nan aka sake fita da ni, inda Aguyi Ironsi ya bayar da umarnin a tsare ni a Naval Base dake Apapa, amma sai Insfekta yace, idan ba zaka damu ba ranka ya dade zamu tsare shi anan shalkwata, zamu gabatar da shi a duk lokacin da ka bukaci hakan. Gen. Ironsi ya karbi shawarar Kam-Salem suka cigaba da tsare ni a wajen. Can da tsakar dare, sai ga dogarin Firaminista Mista Kaftan wanda surikin Tafawa Balewa ne yazo da motar daukar gawa, da kuma wata kanta dauke da akwatunan daukar gawarwaki. Suka nemi a sake ni domin na jagorance su zuwa inda aka kashe su Firaminista.

Vanguard: Me ya faru da kuka je dajin?

Babankowa: Muna zuwa muka ga kumburarriyar gawar Firaminusta yashe a karkashin bishiya da hularsa zanna tana gefensa na dama. Yana sanye da farar kufta me alkyabba wanda tuni ta canza kala zuwa launin jini. A lokacin nan gawar Firaminista tuni ta fara zagwanyewa  har ta fara tsutsotsi! Daga nan ne muka nannadeta da farin kyalle, haka nan na tallefe shi akan cinya ta saboda mu nade gawar duka. Mune mutanan farko da muka fara zuwa kan gawar Firaminista. Da aka gama nadewa aka sanya gawarsa a akwatu, sai nayi mata alama da Larabci dan kar a kasa gane ta. Daga nan muka nufi sashin saukar manyan baki na filin jirgin saman Legas, inda muka taras da wasu kananan  jirage guda biyu suna jiranmu. Daga nan muka saka gawar Furaminista a jirgi tare da wasu danginsa dan zuwa Bauchi ayi mata sutura.

Isarmu Bauchi ke da wuya muka gabatar da gawarsa ga iyalansa. Babu wanda zai iya yiwa wannan gawa wanka a lokacin, kamar yadda addini ya shar'anta, sabida duk ta rube gaba daya kuma ta fara zagwanyewa! Haka nan mukai masa Sallah, aka bunne gawarsa. Hasbunallahu Wani'imal Wakeel! Wannan bakin tarihi ne da ba zamu taba mancewa da shi ba, an cutar da mu a zaman tare a kasarnan, Allah ka biwa wadannan bayin naka hakkin jinin su.

Marigayi Ahmad Ibrahim Babankowa shi ya baiwa jaridar Vanguard wannan labari mai matukar tayar da hankali. Ba shakka Inyamurai sun cucemu, Allah ya isa bamu yafe ba. Allah ya jikan Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello. Allah ya kai haske kabarinsu. Shima marigayi Ibrahim Babankowa muna yi masa adduar fatan alheri, Allah ya jikansa ya gafarta masa yasa aljannah ce makomarsa. Muna mika ta'aziyarmu ga iyalansa musamman Sani Babankowa Allah ya yafe masa.

Yasir Ramadan Gwale
08-09-2015

Monday, September 7, 2015

Asirin 'Yan Shiah Ya Tonu


ASIRIN 'YAN SHIA'AH YA TONU

A makon da ya gabata ne, Shugaban hadaddiyar kungiyar Izala ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jagoranci tawagar kungiyar Malaman Musulunci ta Africa, inda suka kaiwa sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadar Gwamnati. Bayan wannan ziyara ne hotunan wannan ziyara suka bayyana a kafafen sadarwa inda aka ga Shugaban kasa tare da Malaman Musulunci Africa. A hoton akwai manyan Malaman Sunnah na Nigeria da suka hada Sheikh Bala Lau da Imamu Ahlussunnah Wal Jama'ah Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Dr. Muhd Sani Umar Rijiyar Lemo da Sheikh Alhassan Said Jos da Sheikh Hassan Yakub Katsina da sauran Malamai daga kasashen Africa da suka kai wannan ziyara.

Ashe wannan ziyara bata yiwa Mabiya Addinin Shiah na Najeriya dadi ba. Inda suka bi wannan ziyara da mugun sharri da hakan ya kwaye musu zani tare da tsiraita shi'ah  bainar jama'ah. Jaridar AlMizan ta 'yan Shiah, ta Juma'ar makon jiya, ta buga hoton waccan ziyara tare da yi masa taken, "Israeli Na Zawarcin Shugaban kasa Buhari". 'Yan Shiah da yake miyagu ne makaryata, sun saba shararata,  sai suke kokarin canjawa abin suna da nufin nunawa mabiyansu cewar Malaman Sunnah da suka kai wannan ziyara, tare da daurin gindin kasar Israeli suka je. Kaga wannan tsabar karya ne da sharri da jafa'i.

Da yake su 'Yan Shiah mugayen Jahilai ne. Sun jahilci meye Gwamnati da yadda ake mu'amala tsakanin Gwamnati da Gwamnati. Sun manta cewar kasar Israeli na da Jakada a Najeriya kuma itama Najeriya nada nata jakadan a Isaeli wanda duk wata huldar Diplomasiyya tsakanin kasa da kasa ana yinta ne tsakanin wadannan bangarori guda biyu dake Abuja da Tel Aviv. To, amma su Shaih da yake sun jahilci wannan sai suke kokarin nunawa mabiyansu cewar Malaman nan ai Israeli suke yiwa aiki, kuma ita ta sanya su.

Shin yanzu dan Allah su ba zasu ji kunyar bayyana hakan ba? Bahaushe yace idan mai fadar magana wawa ne to daga masu sauraro akwai wadan da ba wawaye bane. Dan haka, anan Allah ya tonawa Shiah asiri. Shugaban kasa Muhammadu Buhari da aka kaiwa waccan ziyara, zai fahimci mugun sharri na mabiya Shiah gareshi da kuma al'ummar Najeriya. Domin yasan cewar ziyarar da aka kai masa ba tada wata alaka ko ta kusa ko ta nesa da Israeli. Haka kuma, duniya na kara fahimtar irin mugun kulli da mummunan fata da Shiah suke yiwa Najeriya.

Dan haka, anan ya dace al'umma su fahimta cewar Shiawa ba mutanan Alkhairi bane, kullum fatansu sharri da makida ga al'ummar Muslmi. Sam basa fatan ganin al'ummar Musulmi sun hada kai waje guda dan yiwa addinin Allah aiki. Ko da yaushe fatansu, shi ne sharri da rarrabuwa tsakanin Musulmi. Muna fatan Allah ya dafawa ayyukan waccan kungiya ta Malman Africa. Allah ka shiga cikin al'amarinta.  Allah ka taimaki Musulunci da Musulmi, ka rusa Shiah da mabiyanta da shugabanninta. Allah ka taimaki duk masu taimakon addininka.

Yasir Ramadan Gwale
07-09-2015

Sunday, September 6, 2015

Allah Ya Kara Daukaka Malam Nuhu Ribadu


ALLAH YA KARA DAUKAKA MALAM NUHU RIBADU 

Jiya Asabar fitacciyar Jarida a Nigeria THISDAY tayi bikin karrama wasu fitattun mutane a Nigeria a saboda irin kwazonsu da san cigaban kasa da suka nuna. Malam Nuhu Ribadu na daya daga cikin mutanan da wannan jarida ta karrama da Award mai suna "Game Changer", a sabida irin kwazo da jajircewarsa da ya nuna wajen ganin an Yaki cin hanci da Rashawa a Najeriya. Ba shakka, karrama fitattun mutane da suka nuna kwazo da gaskiya a aikin su abu ne da ya dace. Malam Nuhu Ribadu mutum ne mai gaskiya da tsoron Allah, wanda ya samu wannan shaida a dukkan sassan Najeriya. Ina amfani da wannan damar wajen taya shi murnar samun wannan kyakkyawar Shaida.

 2019 RIBADU MUKE FATA! 

Yasir Ramadan Gwale
06-09-2019

Friday, September 4, 2015

Halin Da Bashar Assad Ya Jefa Al'ummar Kasarsa Ta Syria A ciki


HALIN DA BASHAR ASSAD YA JEFA AL'UMMAR KASARSA TA SYRIA A CIKI 

Hoton wannan yaron Aylan Kurdi dan Syria wanda igiyar ruwa ta tunkudo gawarsa  gabar ruwan Turkiyya kusan shi ne abinda yafi daukar hankalin manyan Kafafan yada labarai a Gabas ta tsakiya da sauran duniya. Wannan hoto yana cike da tausayi matuka, duk mai Imani dole zuciyarsa ta raurawa idan yaga hoton wannan yaro. Ba shakka Shugaban Syria  Bashar Assad da ya jefa iyayan wannan yaro har hakan yayi salwantar rayuwar sa ta irin wannan hanya mugu ne, kuma Azzalumin shugaba, abin takaici ne kuma abin Allah wadai. Bashar Assad  ya cika a kirashi  babban Azzalumin wannan karnin. 

Bayan ya rushe kasar, ya kashe dubunanna al'ummar da basu san hawa ba basu san sauka ba, dawwamarsa a Mulki tafi dukkan rayukan mutanan Syria muhimmanci a wajensa. Mutanan kasar sun tarwatsa a duniya sun zama almajirai suna bi kwararo-kwararo suna neman abin da zasu Ci,  basa mallakar komai sai kayan jikinsu. Hasbunallahu Wani'imal Wakeel, Ya Allah kayi mana sutura! Ba shakka wannan al'amari na Syria fitina ce gagaruma a wannan zamanin. Amma Allah yayi bushara ga masu hakuri wadan da suke maida komai zuwa ga kaddarawarsa Subhanahu Wata'ala. 

Tambayar da mutane da yawa suke yi ita ce, me yasa kasashen yankin Gulf ko Khaleej da suka hada da Sa'udiyya da Qatar da Kuwait da Daular Larabawa da kuma Bahrain suka kasa taimakawa wadannan 'yan gudun hijra. Amsar wannan tambaya tana da sarkakiya da kuma bukatar kallon abinda ya faru tun farkonsa har ya zuwa yanzu, da kuma yanayin Siyasar Gabas ta tsakiya da Sarautar Sarakunan Gulf.

A bisa gaskiyar zance shi ne, kasashen Gulf da na zayyana,  sune suke samar da kaso mafi rinjaye na kudaden da ake taimakawa wadannan 'yan gudun hijira a sansanoninsu dake Lubnan da Turkiyya da Jordan da tsirarun da ke Masar da Sudan. Haka kuma, abinda wasu zasu ce, shin me yasa wadannan mutane suke gudu tare da rige rigen shiga kasashe Turai maimakon kasashen Gulf su basu mafaka a yankinsu na Larabawa? Anan, wajen amsa wannan tambaya, akwai siyasa mai yawa da ta yiwa wannan batu tarnaki da dabaibayi. Da kuma sanin hakikanin siyasar mulkin Sarakunan wannan yanki.

Abinda yake faruwa shi ne, su wadannan kasashe na Gulf, suna bin tsarin Mulkiyya ne na Sarauta kamar yadda kowa ya sani, a dan haka, a dukkan wani abu da zai faru a Gabas ta tsakiya wadannan kasashe suna kallon komai da tsoron zai iya tasiri a sha'anin tafiyar da mulkinsu, ko kuma ma zai iya zama katuwar barazanar rugujewar mulkin nasu, dan haka ne, sukan fara duba bukatun siyasar mulkinsu akan komai. Kullum tsoron da Gulf suke ji shi ne abinda zai taba musu mulkin su, ko menene kuwa. Shi yasa duk da Alkhairan da rusasshiyar Gwamnatin Muhammad Mursi ta zo da shi, suka gwammace juya masa baya, dan suna ganin cigaba da wanzuwar Mursi barazana ne a garesu da mulkinsu.

Haka kuma, yana daga cikin abinda yake zamarwa kasashen Gulf barazana shi ne batun mamayar da baki 'yan kasashen waje sukai musu, misali Hadaddiyar Daular Larabawa ko UAE dake da yawan mutane wajen Miliyan 9.346 kusan kashi 80 baki ne suka mamaye su, haka kasar Qatar da mutanan ta basu wuce Miliyan 3 ba, amma baki 'yan kasashen waje sun kai kashi 90. Haka nan, Sa'udiyya dake da mutane wajen Miliyan 28 akwai baki 'yan kasashen kusan sama da Miliyan 7, idan kaje Kuwait ma haka batun yake, balle kuma Bahrain da Iran take jin kamar wata jiha ce daga cikin jihohin ta.  

Dan haka, kullum abin da kasashen suke kallo shi ne, barazana ce babba baki 'yan kasashen waje su mamaye musu kasashe. Domin hakan ka iya zama silar rugujewar mulkin da Masarautun wadannan kasashe suke yi. Kada ka dada Kada ka rage wannan ita ce siyasar mulkin da kullum Gulf suke tsoron tabuwarta, domin a tare da su akwai babbar abokiyar gaba, wadda kullum take yi musu fatan masifar da bala'i,  wannan kasa ita ce IRAN, wadda ta zama wani mugun gyambo a tare da kasashen Gulf.

A dan haka, kamar yadda kowa ya sani kasar Syria kasa ce da take da 'yan Shiah masu yawa, adan haka, yadda kasar ta rikice a yanzu idan Sa'udiyya ko Qatar ko Bahrain suka bayar da dama 'yan gudun hijirar Syria su fantsamo kasashen su, to babu makawa k'ulli za a yi da mugun zare, domin Sa'udiyya kanta tana fama da barazanar 'yan Shiah wadan suke daukar zugar Iran, haka nan kuma, Shia tare da goyon bayan Iran zasu shiga Bahrain domin karbe kasar daga hannun Ahlussunnah. 

A saboda haka, wannan barazana ta tabuwar mulkin Sarauta na wadannan kasashe da kuma batun da Iran take da shi na ganin ta karbe ikon wadannan kasashe ya tashi daga hannun Ahlussunnah ya koma gun Shia shi ne yakan hana kasashen Khalij bayar da damar mutanan Syria su shigo musu kasashe domin neman mafaka, dan haka ne mutanan Syria suka Gwammace su ketara Teku su shiga kasashe Turai dan samun ingantacciyar rayuwa. Buguzum da kari Syria ba wata muhimmiyar kasa bace a Gabas ta tsakiya.

Amma mutane da yawa sabida san rai basa ganin laifin Assad da ya tilastawa kansa dawwama a Mulki koda mutanan Syria zasu kare, sannan basa kallon irin rawar da Iran take takawa wajen ganin Assad ya cigaba da kasancewa shugaba ta kowanne hali. Sannan duk wannan soki burutsu da masu baiwa Iran kariya suke basu taba tambayar shin tunda Gulf sun kasa me yasa ita Iran ta kasa taimakawa da wadannan 'yan gudun hijira ko da da kaifa da bargo ba ne?

Ba shakka, duk da wannan uzuri da kasashen Gulf suke da shi, halin da Siriyawa suke ciki a yanzu ya dace su dubesu da idon tausayi da jin kai da makwabtaka da 'yan uwantaka. Haka nan, wasu masu sharhi da yawa suna ganin Gulf ba suda wata hujja gamsasshiya da zata hanasu bude kofofinsu ga Siriyawa. Ba shakka, wannan gagarumar fitina da mutanan Siriya dama Khaleej suke ciki, Allah ne kadai zai iya yaye musu kunci da takaici da suke ciki. Ya Allah ka shiga cikin al'amarin mutanan Syria. Allah ka kawo karshen zalincin Bashar Assad. 

Yasir Ramadan Gwale 
04-09-2015

Thursday, September 3, 2015

MASU SUKAR NADE-NADEN SHUGABA BUHARI SUNA KAN TURBA MAI KYAU


MASU SUKAR NADE-NADEN SHUGABA BUHARI SUNA KAN TURBA MAI KYAU 

A hakikanin gaskiya har yanzu ina jin zafin kisan gillar da Inyamurai suka yiwa Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto da ma irin kisan da aka yiwa Murtala Mohammed. Ban san su ba, ban taba ganin su ba, amma ba shakka naji zafi kuma raina ya so su  yadda naji tarihi ya karantamin irin kisan da akai musu ba da Hakki ba. Watakila da Inyamurai basu kashe wadannan gwaraza ba da tuni  yankin Arewa baya cikin halin da yake ciki na koma baya ta kowanne fanni a yanzu. Na kan tambayi kaina, da ace su Tafawa Balewa da su Ahmadu Bello da su Murtala Mohammed da su Malam Aminu Kano suna raye har kawo wannan lokacin da wanne irin cigaba nake zaton Nigeria take ciki, da watakila matsalolin da ake kuka da su da mu da muka zo daga baya ba zamu taba saninsu ko wani abu mai kama da su ba.

Inyamurai sun cuce mu a zaman tare da Allah ya hadamu, sun kashe mana iyaye, suka cusa mana haushi, suka bakanta mana, sannan suka mamaye mana kasuwanni, suka turasasa mana sayen hajojinsu 'yan jabu a wasu lokutan. To ba mu da yadda zamu yi, Allah ne yaga dama ya hadamu zaman tare a kasa daya, dan haka ya zama tilas a garemu mu koyi yadda zamu zauna da juna lafiya, tare da yiwa juna adalci a duk lokacin da muka samu dama. A ganina zamu zauna lafiya ne da mutanan kudu a lokacin da suka yi mana fahimta ta gaskiya cewa mu mutanan Arewa ba azzalumai bane, ba ha'intarsu zamu yi a zamantakewar mu da su ba! Ya za ai su yi mana wannan fahimtar? Muna zamu bada dama ta hanyar tafiya tare da su a gwamnatance,  Ba mamaki ba wai fahimtar mu ne basu yi ba, illa tsabar Hassada da da kyashi da kiyayya da gaba da suke da ita garemu. Allah shi ne masanin abinda ya faku a garemu.

Game da yadda wasu ke sukar Shugaban Kasa Buhari akan rashin nada Inyamuri dan kudu maso gabas ko dan kudu maso kudu a mukamin sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ni kam banga laifin Buhari ba, sannan masu sukar hakan suma suna kan turba. Domin kuwa, mukamin sakataren Gwamnati babban mukami ne, kuma shi ne zuciyar Gwamnati, dan haka Shugaban kasa na da hakkin ganin ya nada mutumin da zai kiyaye masa amana ba tare da ya tozarta ta ba. Masu suka kuwa, musamman daga Arewa, suna nuna hakikanin halin mutumin Arewa na tausayi da jin kai da rashin san babakere da handama, suna da ra'ayin ayi Gwamnati ne da zata tafi da kowa tare, wanda wannan tunani ne mai kyau, kuma abin a yaba ne.

Abinda da yawan mutane musamman masoya Buhari suka manta shi ne, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan siyasa ne, kuma siyasa ce ta kawo shi kujerar Shugaban kasa. Dan haka siyasa ce ta bada damar kalubalantarsa a bisa yadda yake tafiyar da Gwamnati, dan haka zai zama koma baya da dakushewar tunani mutane su dinga ganin laifi ne a kalubalanci Shugaban kasa Buhari a siyasance, har kaji wasu na zagi da cin mutunci dan an soki manufofinta Gwamnatin siyasa. Hamayya ko Adawa a siyasa wajibi ne, domin hakan shi ne ya bambanta mulkin siyasa da na kama karya irin na soja.

Shugaban kasa Buhari shi ne mutumin da Allah ya danka amanar Najeriya a hannunsa, wadan da suka zabe shi da wadan da basu zabe shi ba. Kuma, tabbas ne a ranar gobe kiyama sai Allah ya tambaya shi akan yadda ya tafiyar da mulkin Najeriya. Muna masa fatan cin wannan jarabawa, haka kuma, Allah ba zai tambayi Buhari me yasa bai bawa Inyamurai sakataren Gwamnati ba, illa zai tambaya shi idan bai yi musu adalci ba. Yana da kyau, Shugaban kasa, ya haska wa al'umma musamman wadan da basu zabe shi ba, cewar shi shugaba ne na kowa ba wani sashi ba.

Haka kuma, ba yadda muka iya dole mu zauna da juna lafiya indai ana zaman tare a Najeriya. Ya zama tilas mu da Inyamurai da sauran kabilun kasarnan mu nunawa juna cewar zamu iya adalci a duk lokacin da muka samu shugabanci, dole a samu zullumi a duk lokacin da wani sashi suke ganin kamar ba za ai musu adalci ba, imma ta hanyar rabon mukamai ne ko ta hanyar tafiyar da Gwamnati, dan haka babban kalubalen da yake kan Shugaban kasa shi ne, ya gamsar da Inyamurai da sauran kananan kabilu cewar ba zai musu rashin adalci ba a matsayinsa na Shugaban kasa.

Bayan haka, ya zama dole a duk lokacin da aka ga Gwamnati na yin wasu abubuwa na nuna wariya a kalubalance ta, domin wannan shi ne Demokaradiyya kuma shi ne mulkin siyasa. Dan haka, masu kalubalantarsa  (Shugaban kasa) da nad'e nad'ensa  suna kan turba mai kyau, domin haka siyasa ta gada, kuma shi kansa Shugaban kasa ya shafe kusan shekaru 12 yana kalubalantar salon Mulkin Gwamnatin PDP da ya shud'e. Allah ya taimaki Najeriya.

Yasir Ramadan Gwale 
30-08-2015

SHUGABANCI A SUDAN: Bangarancin Da Ya Haifar Da Yakin Darfur


SHUGABANCI A SUDAN: BANGARANCIN DA YA HAIFAR DA YAKIN DARFUR

A Sudan Shugaban kasa da mataimakinsa, sun fito daga kabila daya, jiharsu daya garinsu daya. Abokaine tun suna yara, tare suka shiga aikin soja tare suka yi juyin mulki, tare suka kafa Gwamnati. Wannan tsabar san kai da nuna fifiko na daya daga cikin dalilan da suka sabbaba rikici a wasu yankuna na kasar, musamman mutanan da suke ganin kabilar Ja'alyiyya ta Shugaba Umar Hasan Albashir ko mutanan yankinsa na Shamaliyya sun mamaye komai na harkar tafiyar da Gwamnati. 

Wannan batu na mamayar madafun iko da mutanan yankin Shugaba Albashir suka yi, shi ne jigo kuma kashin bayan rikicin yankin Darfur dake yammacin Sudan, duk da cewar akwai siyasa mai tarin yawa a ciki da kuma cakuda karya da gaskiya akan batun. Bisa radin kansa mataimakin Shugaban kasa wanda ake yiwa kallon shi ne Khalifa bayan Albashir, abokinsa ne kuma shakikinsa,  Ali Usman Muhammad Taha aka wayi gari yayi murabus daga kan mukaminsa.

Har ya zuwa yanzu babu wasu tabbatattun dalilan da suka bayyana hakikanin dalilin Murabus din Taha, illa shaci fadi na manazarta. Sai dai bayan Murabus din Taha an sake maye gurbinsa da wani mutum daga yankin shamaliyya na Shugaba Albashir dake Arewacin Sudan. Ustaz Hasabu Muhammad Abdurahman shi ne mutumin da ya zama sabon mataimakin Shugaban kasa bayan murabus din Ali Usman Muhammad Taha.

Yasir Ramadan Gwale
29-08-2015

RE: Malamai Masu Ci Da Addini


RE: Malamai Masu Ci Da Addini 

Abbas Yushau Ya Rubuta game da rubutun da nayi dazu kan ziyarar Kuka ga Buhari:

Yasir Ramadan Gwale wannan Magana taka haka take, Marigayi Sheikh Abubakar Gumi Allah ya jikansa sanda yana da rai yayi muamala da Shugabannin Najeriya  musulminsu da Kiristocinsu, takai idan yayi tafiya akan hanyarsa ta zuwa gida ya kan tsaya a legas su tattauna da Shugaba Manjo Janar Muhammadu Buhari, Shugaba Ibrahim Babangida da Sauransu, Kai akwai lokacin da Shugaban Kasa na soja kuma dan Kabilar Igbo, Manjo Janar Johnson Thomas Umunakwe Aguiyi Ironsi ya kirawo Marigayi Sheikh Abubakar Gumi Fadar Dodan Barack yacewa Malam yaje kasashen larabawa yayi musu bayani cewa juyin mulkin da aka yi na watan Janairun 1966 an yi shi ne da kyakkyawar manufa, nan take Shekh Gumi yacewa Janar Ironsi ba zai je ba saboda duk wadannan kasashe sun zaga da sardauna, saboda haka domin mutuntakarsa ba zai koma yace an kashe su Sardauna da kyakkyawar manufa ba, haka yace shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo ma yana girmama shi inda yace ba musulmi bane amma kuma ba kiristan azziki bane da dai sauransu, Kuma wannan mu'amala da sheikh Gumi yayi bai hana shi gaya musu Gaskiya ba, kuma bai tara abin Duniya ba.

28-08-2015