Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin
Lokaci a Watan Azumi #4
Bayan sallam irin ta addinin musulunci, Assalamu Alaikum warah
matullah, Ya ‘yan uwa masu girma, bayan na gaisheku gaisuwa irin ta musulunci
ina kuma gaisheku gaisuwa irin ta al’ada ina kwananku; kamar yadda muka somo
bayani kusan makwanni uku da suka gabata, cikin ikon Allah yauma zamu cigaba da
wannan bayani da muka dauko.
Ya ‘yan uwa masu girma, kamar yadda muka sani RAMADAN dai tafiya
ta tafi, yanzu mun kusa cinye goma ta biyu, a wannan wata mai albarka, muna
kuma tunkarar goma ta uku kuma ta karshe a wannan wata mai cike da dimbin
falala. Allah ya sa muna daga cikin wadan da za su sami rabauta a cikin wannan
wata. Ya ‘yan uwa hakika labari ya isa garemu cewar da yawan ‘yan uwanmu matasa
sunyi rauni ainun a wannan goma ta biyu wajen zagewa da yin ibada, lallai ya
kamata mu sani shi wannan wata kamar yadda Allah ya fada kwanaki ne
kididdigaggu dan haka suna da dumbin falala, bai kamata mu yi sake ba tare da
mun ribaci lokkutanmu ba.
Manzon Allah Sallalahu Alaihi wasallam, shi Allah ya turo da
sakon musulunci, kuma ya ce ya gafarta masa zunubansa idanma ya yi, idanma zai
yi nan gaba anyafe masa sallalahu alaihi wasallam, amma duk da haka Manzon
Allah bai shantake ba, hasalima kamar yadda uwar muminai take cewa yana zage
dantse sosai wajen yawan sallaloli da karatun alkur’ani da sadaka da kyauta,
har sai da takai manzon Allah yana sallah yana kuka yana gemunsa yana cikewa da
hawaye sallalahu alaihi wasallam, uwar muminai ta ce ya manzon Allah shin bazaka
saukakawa kanka ba, bayan Allah ya ce ya gafarta maka laifukanka, manzon Allah
ya ce mata “afala akuna abdan shakuran” ma’ana, shin bazan kasance bawa mai
nuna godiya ga ni’imar da Allah ya yi min ba. Ya ‘yan uwa masu girma mu kalli
yadda Manzon Allah yake sallah har kafafunsa masu daraja suna tsagewa duk dan
saboda ya nuna godiya ga ni’imar da Allah ya yi masa.
Ya ‘yan uwa ina ga ni da kai da bamu da garantin ranar tashin
alkiyama, lallai ya kamata mu ribaci wannan lokaci mu zage dantse wajen yin
ibadu, musamman wannan goma ta karshe wadda a cikinta ne ake sa ran dacewa da
ganin daren lailatul kadari, kuma a cikinsa ne ake yin I’itikafi wanda mutane
ke tarewa a masallaci kacokam domin neman yardar Allah, ya ‘yan uwa masu girma,
lokaci baya jira sai dai a jira shi, mu tuna, mutum nawa ne wadan da muke tare
da su a Ramadan da ya gabata amma kuma yanzu babu su, wannan falala ta wannan
shekarar ta wuce su, lallai ka sani ya dan uwana kaima ba kada yakinin zaka iya
samun nasarar riskar wani Ramadan din, don haka a yi hakuri a zage dantse wajen
ibada da kuma yawaita salloli, musamman a wadan nan kwanaki goma masu zuwa,
lallai idan kayi rauni a baya to yanzu ka fadawa zuciyarka cewar lallai ya
kamata ka zage dantse a wannan kwana goman.
Allah ya bamu ikon amfana da lokutanmu a cikin wadan nan kwanaki
masu zuwa, Allah kuma ya datar da mu da ganin Lailatun kadri, Allah ya karbi
ibadunmu kuma ya yafe mana kusakuranmu, wadan da muka sani da wadan da bamu
sani ba, kuma kada mu manta da sanya ‘yan uwanmu musulmi a cikin dukkan
addu’o’inmu na musamman, wadan da suke cikin tsanani Allah ya yafe musu,
kasarmu kuma Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya da kuma abinda lafiya zata
bukata. Allah ya shiryemu shirin addini. Yau ma anan zan dakata sai Allah ya
kaimu wani makon zamu dora Allah ya karbi ibadunmu.
Yasir Ramadan
Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment