CPC Ba Su Da Kwarin Gwiwar
Cin-zaben 2015
“Ina fatan duk
mutumin da zai yi min martani ya tabbata ya karanta abinda na rubuta har
karshe.”
Bisa ga dukkan alamu wannan zaben na 2015 da yake tunkaromu
Jam’iyyar Hamayya ta CPC bata shiryawa cin zaben da gaske ba. Don bayanai da
rahotanni suna tabbatar da cewar kwarin gwiwar da CPC suke da shi, shi ne idan
aka samu hadewa da jam’iyyar ACN, kusan mafiya yawancin ‘yan cpc wannan shi ne
tunaninsu cewar idan an hade za’a iya cin zabe. Shakka babu Jam’iyyar ACN jam’iyya
ce da ta ke da tsari musamman a inda tayi kakagida wato yankin Kudu maso Yamma
ko ka ce yanki Yarabawa, hakika duk wanda ya kalli irin yadda suka mamaye
wannan yanki dole ya tabbatar da cewar suna da kyakykyawan shiri, da tsari
karkashin Jagorancin Shugabansu Asiwaju Bola Ahmwd Tinubu.
Karkashin Jagorancin shi wannan mutum Tinubu ACN ta karbe
ragamar iko daga PDP a jihar Ogun, jihar da ke zaman mahaifa ga tsohon shugaban
kasa Olushegun Obasanjo. Wanda wannan ba karamin aiki suka yi ba na karbe
ragamar ikon wannan jihar daga hannun PDP duk kuwa da cewar Obasanjo shi ne
kusan ya yi uwa ya yi makarbiya a PDP amma kuma jiharsa ta gagareshi, Wani abu
da zai baka mamaki da shi wannan mutum (Tinubu) wai shin kudi yake rabawa
mutanan yamma suke zaban jam’iyyarsa? Ko kuwa tsabar iya zance ne da iya
siyasa? hakika wannan tambaya ta jima tana yimin zillo a raina.
Alamu sun tabbatar da cewar ACN ba burinsu su kafa gwamnati a
Najeriya ba. Kawai suna bukatar kasancewar yankin yarabawa ya kasance karkashin
Jam’iyyar hamayya, domin a yadda suke ganin sun fi kowa wayewa da sanin ilimin
boko, kuma zaben da ya gabata na 2011 ya kara nunawa cewa basu da burin kafa
gwamnatin tarayya, kuma da wahala su yarda su yi tarayya da sauran ‘yan
Najeriya a cikin Jam’iyya daya, tabbas yau ko da a ce ACN zata kafa Gwamnatin
tarayya, lashakka yarabawa sai sun balle sun kafa jam’iyyar hamayya ta daban,
domin su sumfi gwammacewa su yi ta kasancewa ‘yan Hamayya ko Adawa, kamar yadda
Hausawa muke musu kirari da cewa “Yarabawa masu kwalo-kwalo” shakka babu
suna da kwalo-kwalo sosai da gaske. Kamar yadda na ce, duk wanda ya kalli zaben
da ya gabata, ACN ta fi mayar da hankalinta ne akan yankin Yarabawa ya ci zabe,
sabanin sauran jihohin Najeriya wanda suna ganin idan tayi ruwa rijiya idan
kuma bata yi ba daman haka ake zato.
Idan muka kalli yadda ACN suka yi ruwa suka yi tsaki akan shari’ar
da suka kai ta jihar Osun wanda Rauf Aregbesola yake zame musu dan takara, nu
nace akan wannan shari’ah kwarai da gaske har sai da hakarsu ta cimma ruwa,
amma kuma idan muka kalli zaben da ya gabata na jihar Benue shedu da bayanai
sun tabbatar da cewar ACN ita ce ta samu nasara a wannan jihar, amma uwar jam’iyyar
ta kasa basu maida hankali akan shari’ar wannan jihar ba kamar yadda suka yi a jihar Osun, wannan ya
kara tabbatar mana da cewar ba burinsu su mamaye Najeriya ba illa yankinsu
kawai.
Idan kuma, muka sake duba Arewa muka kalli Jam’iyyar CPC da
Jagoranta Gen. Muhammadu Buhari, zamu ga cewar tabbas babu wani shiri a kasa na
kafa gwamnati a 2015, kullum kawai surutai ake yi a kafafen yada labarai, da
tunanin waccan hadewa, babu wanda zai yi shakkar cewa CPC bata da dumbin magoya
baya a Arewa, tana da su na ban mamaki kuwa, amma zaka iya kiransu da cewar
taron tsintsiya ne babu shara, domin mafiya yawan ‘yan Jam’iyyar nema suke
jam’iyyar ta taimaka musu, ba wai su su taimakawa jam’iyyar ba. Kusan tun
kafuwar CPC ta kafu da rikici da hayaniya, domin da yawan mutane sun shiga
Jam’iyyar da tunanin samun makoma, wasu na ihun sai sun zama shugabanni a
Jihohi wasu a kananan hukumomi wasu a mazabu, wasu kuma suna son su zama ‘yan
takara ko ta halin kaka. Wannan rikicin ya hana CPC katabus a Arewa, kuma idan
ba hankali aka yi ba shine zai ci gaba da mamaye Jam’iyyar har zuwa lokacin
zabe mai zuwa.
Akwai dubban mutane suna nan sun dana tarko jira suke lokaci ya
yi su zo domin su shiga Rigar Buhari ko suma zasu dace da al’farmarsa domin
‘yan Najeriya su sahale musu, kuma kamar yadda ake kyautata zato ga Jagoran
Jam’iyyar Gen. Buhari mutumin kirki ne, haka ya kamata mutanan da ke cikin
jam’iyyar su kasance, amma kusan akasin haka ya fi faruwa, domin anyi sake da
karnuka da kuraye da muzurai da aladu duk sun shiga cikin jam’iyyar sunyi
kaka-gida kuma suna ta yi mata kafar ungulu tare da nuna cewar su sun shigo
Jam’iyyar ne saboda Buhari, wanda a zahiri halayyar su da dabi’unsu da
ayyukansu sun sha bamban da na Gen. Buhari. Saboda irin wannan kwamacala da
rikita-rikitar jam’iyyar CPC ta sanya ala dole, jagoran Jam’iyyar Gen. Buhari
ya dauki Jam’iyyar dungurungum ya mikata ga tsohon ministan Abuja Mallam Nasiru
el-Rufai ya yi mata garambawul, saboda yakini da yake da shi cewar el-Rufai
kwararre ne da zai iya saita jam’iyyar ta zauna kan turba.
Mafiya yawan ‘yan Najeriya duk zatonsu shi ne cewar jam’iyyar
CPC ta Gen. Buhari ce. Sai gashi mutane irin su Sule Yahaya Hamma da Rufai
Hanga suna ikirarin cewar Jam’iyyar tasu ce su suka kafa ta da sunansu su suka
samarmata da ofis da sunansu aka kafa wannan jam’iyya, dan haka sai wanda suke
so shi zai tsaya takara a cikin jam’iyyar, wannan ya haifar da yin jabun katin
shiga jam’iyyar a nan Kano inda na fito, kai rahotanni ma sun nuna cewar har
jabun katin tsayawa takara aka yi tun daga matakin unguwanni har zuwa kananan
hukumomi zuwa Jiha, wanda wannan batu kusan haka ya faru a jihohin Kano da
Bauchi da katsina da Neja kamar yadda muka karanta a Jaridu kuma wannan ne
dalilin da ya sanya uwar jam’iyyar dakatar da zaben shugabannin jam’iyyar a
wadancan johohi a ranar Asabar 11 ga watan Disambar 2010.
Kamar yadda muka sani tsarin jari hujja shine linzamin siyasar
wannan lokacin. Shakka babu, duk harkokin siyasa baza su yiyuba sai da kudi, to
yana daga cikin abinda CPC ta rasa shine wadan da zasu taimakawa Jam’iyyar ko
da badan Allah bane. Domin dai dole ka bude ofis a kusan galibin mazabu dole a
samar da abinda ake fada da yaren siyasa wato kayan aiki, dole ayi
abubuwa da dama wadan da suke bukatar kayan aiki, amma manyan masu kayan
aiki da suke a cikin jam’iyyar irinsu Sanata Rufai Hanga da Sule Hamma duk
sun shagaltu da yiwa juna kafar ungulu da shatile kafafuwan Jam’iyyar matukar
ba nasu bane suka sami takara ba, haka kuma jam’iyyar ta yi wawar asarar mutane
irinsu Adamu Aleiru da Gari Mallam a jihar kebbi, da Gamaliya dan takararta na
Gwamna a Jihar Taraba da sauransu da dama, ita asarar magoyin baya a siyasa ko
da babu abinda yake tsinanawa matsala ce, indai har zai fita bainar jama’a ya
ce yabar wannan tafiyar.
A nata bangaren ita ma Jam’iyyar PDP a shirye ta ke na kare
kambunta na ci-gaba da rike madafun iko. Shakka babu PDP aiki suke yi tukuru
domin samun Nasarar jam’iyyar a 2015, dan haka ne ma suke ta kokarin hadiye
‘yan CPC din. A loakcin da CPC suke ta dogon turanci da yawan mitin tsakanin
kaduna zuwa Legas shin a hade tsakanin ACN da CPC ko kuwa, su kuma a nasu
bangaren PDP suna nan suna raba dare suna mitin akan ya zasu samu nasara a
2015, Bahaushe ya ce shirin zaune yafi na tsaye, tabbas cpc shirin tsaye suke a
yayin da PDP suke shirin zune.
Idan muka kalli zaben gwamnonin da akayi a jihohi biyar wato
Sokoto da Adamawa da Kogi da Bayelsa da Cross-Rivers, ya nuna cewar PDP sun
shirya tsaf domin fuskantar CPC a 2015, domin da zaben sokoto ya zo kusan ‘yan
jam’iyyar musamman gwamnonin Arewa tarewa suka yi a sokoton har sai da suka ga
Alu ya kai labari duk kuwa da ana kallon kamar yana takun saka tsakaninsa da
shugaban kasa a wannan lokacin, kuma wani abu da zai tabbatar da yunkurin PDP
na sake kafa gwamnati, kusan idan mun lura ita PDP duk danta sai ya yi mata
aiki, ko da kuwa ba’a zaman lumana da shi a jam’iyyar, idan muka kalli zaben
Adamawa kowa yasan akwai tsamin dangantaka tsakanin Atiku Abubakar da Murtala
Nyako tun kusan zaben fitar da gwanin da aka yi tsakanin Atiku da Jonathan,
amma sai da Atiku ya fito ya taya Nyako yakin neman zabe domin samun nasarar
Jam’iyyar PDP.
Kamar yadda Sanata Gemade ya fada a karshen wannan makon cewar
tattaunawar CPC da ACN zata sake wargajewa ne, wannan magana ce mai yuwuwa.
Domin mutumne ya samu fili ya gina gida yana cikin gidansa sai abokinsa ya zo
ya ce ya fita daga cikin wannan gidan nasa ya zo su kafa wani sabon gidan mai
kayan alatu! Kaga abu ne da kamar wuya, to kusan haka batun CPC yake da ACN,
domin ni kam bantaba zaton cewa ACN zasu saki jam’iyyar da suka sha
gwagwarmayar rayata a yankin kudu maso yamma ba, rana a tsaka kuma su ce sun
barta sun koma CPC wannan kam da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Ko dai
shi Buhari ya yarda ya koma ACN dan ya zama dantakararsu na shugaban kasa, ko
kuma a dauki dogon lokaci ana ta mitin tsakanin Legas da Abuja da Kaduna har
lokaci ya kure daga karshe kuma tattaunawar ta sake karyewa. A sake komawa
gidan jiya.
Idan ance za’a hade shin jam’iyya biyu za’a zaba da dantakara
guda daya wanda wannan ya ci karo da tsarin hukumar zabe, ko kuwa kamar yadda
na fada yarabawa ne zasu bar ACN su koma CPC ko kuwa Gen. Buhari da magoya
bayansa ne zasu bar CPC su koma ACN? Lallai amsar wannan tamabayar zata nuna
alkiblar inda aka dosa, hakika halin da muke ciki yanzu lokaci yana kara
tafiya, kuma yana kara yiwa CPC karanci. Domin dai tsarin hukumar zabe ya ce
sai dan takarar ya samu kashi 25 na kuri’ar da aka kada a jihohi 23 sannan ya
iya zama shugaban kasa, mu dauki yankin Arewa maso yamma da Arewa maso gabas
shakka babu CPC tana da karfi kuma zata samu fiye da wannan kashin da tsarin
hukumar zabe ya yi tanadi, mu dauka ma CPC tana da goyon bayan jihohin Arewa 19
wanda ana bukatar sauran jihohi hudu kenan domin samun zabe, wanda kai tsaye
wani zai ce dan jihohi hudu ai ba matsala bane, wanda gagarumin aiki ne samun
wadan nan kuri’u a jihohi hudu daga kudu, domin kowa yasan cewa mafiya yawancin
jihohin kudu dangwale ake yi ba zabe ba. Kuma kar mu manta a Arewa muna da
jihar Plateau da Benue wanda ko ana ha-maza ana ha-mata baza su zabi Dan Arewa
musulmi ba.
Kuma suma a nasu bangaren masu adawa da CPC zasu yi ta hura mata
wutar rikici, su hana jam’iyyar sakat ta yadda zasu sami lagon jam’iyyar a
zaben. Tabbas alamu sun nuna cewar wannan shugaban me ci wato Goodluck Jonathan
yana son tsayawa wani zaben a 2015, wanda abu ne mai yuwuwa, amma PDP suna da
hasashe kuma suna da zurfin tunani, domin idan suka ga cewar GEJ zai kada Jam’iyyar
to shakka babu zasu fitar da dan takara daga Arewa wanda zasu marawa baya dan
ganin bata bare musu ba, kamar yadda rade-radi yake bayyana cewar ana yunkurin
tsayar da gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido da Gwamnan jihar Rivers Rotimi
Ameachi, wanda a turance wannan shi ne Plan B na jam’iyyar PDP, domin da
su rasa gara su dauko wanda suke ganin zai iya cin zabe ko da kuwa a wajen Jam’iyyar
yake.
Yasir Ramadan
Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment