Tsokaci Kan
Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi #5
Bayan sallama irin ta addinin musulunci Assalamu Alaikum
Warahmatullah, Ya ‘yan uwa masu girma, ina yi mana barka da sake saduwa a
wannan makon, kuma mako na karshe a cikin wannan wata mai albarka na Ramadan,
da wannan shafi ya kwashe kusan makwanni yana kawo muku maudu’in da muka ambata
a sama, hakika wannan ita ce ranar Litinin ta karshe a wannan wata da muka
shafe lokaci muna azumtarsa, muka kara kusanta kanmu zuwa ga mahaliccinmu Subahanahu
wata’ala.
Kamar yadda Bahaushe ke cewa komai ya yi farko shakka babu zai
yi karshe. Tun kafin zuwan Ramadan da kwanaki koma watanni muke ta addu’a Allah
ya nuna mana wannan wata, to dai yau gashi muna cikin kwanakin da muke karkare
wannan ibada ta Azumi, mun dauki lokaci muna kauracewa ci-da-sha da jima’i da
tundaga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana ba don komai ba sai dan gasgata
alkawarin Allah, sai dan gasgata sakon da Allah ya turo ManzonSa Salallahu
Alaihi Wasallam da shi, muna kara shaidawa babu abin bauta da gaskiya bisa
cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne.
Ya ‘yan uwa masu girma, saninmu ne mun shafe tsawon wadan nan
kwanaki muna karatun al-qur’ani da salloli na nafila da na farilla da zikiri da
yawan addu’o’i. Ya ‘yan uwa lallai mu sani Ramadan makaranta ce da ba’a
kammalata har sai randa wa’adi ya tsaya akanmu, lallai wa’azozi da darusan da
muka koya ba wai kawai zasu tsaya a iyakar kwanakin Ramadan bane kawai, a’a zasu
dore ne har iyakar karshen Rayuwarmu, mu yawaita karatun al-qur’ani da sallolin
nafila da addu’o’i kamar yadda muka yi a Ramadan.
Wasu da yawa sunan nan sunyi ibada karbabbiya, kuma Allah ya
yarda da su, ya yi musu rahama daga cikin rahamarSa subanahu wata’ala, saboda
sun mika lamuransu ga Allah, sun karanta al-qur’ani sunyi kuka sun zubar da
hawaye, sunyi azkar safe da yamma. Muna fatan Allah ya sanya muna daga cikinsu.
Wasu kuma suna nan babu abinda suka yi illa wahalar da kansu da kishirwa da
yunwa domin da dama wasu Azumin da yake bakinsu bai hana su karya da yaudara da
cin-amana da cin mutunci ba da gulma da kinibibi da yaudara da sata da kisan
kai da zina da shaye-shaye! kai wasu ma Azumin da suke bai hanasu kallon fina
finan batsa da kallon tsiraici ba, muna rokon Allah ya sa bama daga cikin wadan
nan mutane. Hakika mun aikata kurakurai da dama acikin wannan wata mai albarka,
muna rokon Allah ya yafe mana kurakuran da muka aikata, wadan da muka sani da
wadan da bamu sani ba.
A yayin da muke shirin bankwana da wannan wata na Ramadan, muna
kara kusantar lokacin Idin karamar sallah ne (Idil Fitr) jama’a da dama
hankalinsu yanzu ya karkata zuwa ga hidundumun da suka shafi masalar duniya,
wato kayan sallah da kuma irin kayan tande-tande da lashe-lashe da ake ta
kokarin tanadi domin bikin sallah tare da iyalai da ‘yan uwa da abokan arziki,
lallai ba haramun bane a musulunci muci me kyau mu sha me kyau kuma mu sanya
sutura mai kyau.
Ya ‘yan uwa masu girma, kamar yadda mukaji malamai suna fada
daga manzon Allah salallahu alaihi wasallam cewar, a wadannan kwanaki goma da
suka rage ne ake sa ran dacewa da daren lailatul kadari, wanda Allah ya ce
alkhairinsa ya fi na watanni dubu, haka kuma wannan dare ana sa ran dacewa da
shi ne a kwanakin da ake kira wuturi, wato 19, 21, 23, 25, 27, 29 lallai yanzu
kwanakin da suka rage mana sune 27 da 29 kada mu yi sake da wadan nan kwanaki
lallai mu dage da addu’o’i da rokon Allah dukkan bukatnmu na alkhairi.
Daga karshe, ina mai amfani da wannan damar wajen rokon Allah ya
yafe mana kurakuran da muka aikata a cikin wannan watan wadan da muka sani da
wadan da bamu sani ba, Allah ya sa ibadunmu karbabbu ne, Allah ya sa muna daga
cikin wadan da Allah ya yarda da ayyukansu a cikin wannan wata; halin da muke
ciki na zullumi da tashin hankali a wannan kasa tamu muna rokon Allah ya yaye
mana ya bamu lafiya da zaman lafiya, Ya Allah muna tawassali da wannan ibada da
mukayi, muna tawassali da kyawawan sunayanka tsarkaka madaukaka Allah ka dawo
mana da zama na aminci acikin garuruwanmu, Allah ka bamu zaman lafiya mai
dorewa.
Hakika baza mu manta da ‘yan uwanmu da suke a asibitociba cikin
halin rai kwakwai mutu kwakwai, Ya Allah ka basu lafiya, mu da muke da lafiya
Allah ka kara mana lafiya, ‘yan uwanmu Musulmi da suke cikin matsanancin hali a
kasar Syria da Burma da Afghanistan da Iraqi da Somalia da duk inda musulmi
suke Allah ka amintar da su, Allah ka kaimusu dauki. Allah ya yafewa wadan da
suka rigamu gidan gaskiya mu kuma Allah ya kyauta namu karshen.
Har ila yau zanyi amfani da wannan damar domin yin godiya ga
hukumar gudanarwa ta wannan gida mai albarka bisa wannan dawainiya da suke na
kokarin tunasar da al’ummar kulluma rana, Allah ya saka da alheri, haka kuma ina
addu’ar fatan alheri ga abokanan da muke gabatar da shirye-shirye tare da su
Allah ya sakawa kowa da alheri. Haka suma zaratanmu kuma sarakan aiki wato
Auwal Adamu Tahir Sabon Gida da Aliyu Danlabaran Zaria wallahi babu abinda zamu
ce da ku sai godiya da fatan alheri, wannan zumunci da mukayi Allah ya sa ya
dore har zuwa ga ‘ya ‘yanmu da jikokinmu, sannan shima madugu uban tafiya
yayanmu Mallam Muhammad MK hakika bakinmu ya yi kadan wajen nuna godiyarsa da
farincikinsa a gareka, hakika ka cancanci a gaishe ka da dukkan gaisuwa irin ta
girmamawa bisa wannan muhimmin aiki, Allah ya saka maka da alheri, ya yawaita mana
irinku acikin al’umma, Allah ya sanya albarka a cikin rayuwarka da rayuwar iyalinka
da zurriyarka, Allah ya sakawa kowa da alheri.
Wassalamu Alaikum Warahmatullah.
Yasir Ramadan
Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment