Kotu a Zamfara Ta Daure Wani Matashi Shekara Daya
Saboda Ya Saci Hular Dan Minista
Kotun shari’ar Musulunci da ke kanwuri a gusau ta Jihar Zamfara ta
zartarwa da wani matashi mai suna Shehu Jiga wanda aka fi sani da Lalo daurin
shekara daya a gidan kaso tare da biyan tara ta Naira 20,000 saboda kama shi da
laifin Satar hular dan gidan Minista Safiyanu Bashir Yuguda, ita dai hular an
kiyasta kudinta da cewar ya kai kimanin Naira 47,000.
Kamar yadda bayanai suka tabbatar, yana daga cikin al’adar danginsu
Lalo sukan kai ziyarar barka da Sallah ga ‘yan uwansu da danginsu ciki kuwa
harda karamin Ministan ayyuka Alh. Bashir Yuguda, wanda yake zaune a unguwar
GRA da ke cikin birnin Gusau.
Kamar yadda aka shaidawa kotu cewa Lalo sananne ne a danginsu
ministan, kuma yana daga cikin wadan da suka kai wannan ziyara ta Barka da
Sallah zuwa gidan, sai dai bayan fitarsu ne aka lura da cewar hular Safiyanu
wato dan ministan ta yi layar zana inda aka nemeta sama ko kasa. Dan haka ne
Iyalan ministan suka yi yunkurin bibiyar wadan da suka kawo ziyara a wannan
gida da nufin gano wanda ya dauki wannan hula. Daga baya bayanai suka nuna
cewar anga wannan hula a wurin lalo inda ya tabbatar da cewar ya dauki wannan
hula, kuma ya sayar da ita akan kudi Naira 15,000.
Da yake gabatar da hukunci mai shari’ah Alhaji Hadi Sani, ya ce
bisa la’akari da bayanan da wanda ake zargi ya gabatar dan haka kotu bata da
wani hukunci illa ta yanke masa daurin shekara daya a gidan kaso tare da biyan
tara ta Naira 20,000.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment