Hakika a wannan
karni na 21 Harshen Hausa ya samu ci-gaba sosai kuma me ma’ana. Tabbas duk
wanda ya kalli irin yadda al’amura ke gudana a duniyar Harshen Harshen Hausa dole
ya yi murna da cewar wannan Harshe yana kara samu ta gomashi sosai, misali ada
can jaridar da take fitowa da Hausa akusan kasarnan ko ma ka ce duniya gabaki
daya itace Gaskiya Tafi Kwabo wadda kamfanin buga Jaridu na Arewa ke bugawa na
NNN, amma kuma yanzu adadin jaridun da ake bugawa da Harshen Hausa ya karu
sosai da gaske, domin yanzu muna da jaridu da suke karade kasarnan baki daya
kamar Aminiya da Leadership Hausa da Rariya da suransu, haka kuma ta bangaren
mujalluma ansamu ci gaba sosai domin kamar yadda duk me bibiyar lamuran
mujallun Hausa ya sani ya san da cewa
Mujallar Fim kusan itace mujalla daya tilo da take fitowa da Harshen Hausa amma
yanzu adadi na mujallun Hausa na karuwa cikin sauri.
Hakika wannan
yake kara nuna bunkasa da buwayar Harshen Hausa a tsakanin Harsunan Najeriya. Domin
ko wane Harshe yana bunkasa ne ta hanyar rubuta shi da kuma karantashi, kuma
wani abun farinciki shi ne adadin masu karanta Hausa shi ma yana karuwa cikin
sauri, duk wanda ya ke bibiyar inda ake hada-hadar jaridun Hausa zaiga yadda
ake wawasonsu, domin irin yadda Harshen Hausa yake da sauki a wajen Bahaushe
akwai wadan da sun iya rubutawa tare da karanta Hausa ba tare da sunje wata
makaranta sun koya ba, sabanin sauran Harsuna wadda sai mutum ya yi da gaske
sanna ya kware wajen rubutu da kuma iya karantawa.
Wani bangare kuma
da yake kara nuna bunkasar Harshen Hausa shi ne irin yadda ake samun sabbin
kafafen watsa labarai masu watsa shirye-shiryensu da Hausa. Sanin kowa ne cewar
kusan sama da shekaru 50 ana watsa shiri da Hausa a gidan radiyoyin kasashen Turai
da Amerika kamar BBC HAUSA da DW HAUSA (docabele) da VOA Hausa (Muryar
Amerika), amma ya zuwa yanzu adadin gidajen radiyon da suke watsa shirinsu ga
duniya da Hausa shi ma ya karu domin yanzu akwai sabbin gidajen Radiyoyi kamar
RFI Hausa (faransa) da Radiyo Taiwan da Radiyo Sin da Muryar Afurka na kasar Masar
da sauransu. Duk wannan yana kara nuna mana cewa lallai Haurshen Hausa yana
samun bunkasa da ci-gaba.
Haka zalika inda
Harshen Hausa ya yiwa sauran Harsuna zarra shi ne, bayan karantar Harshen na
Hausa kuma ana iya Nazarin Al’adun Hausawa da kuma Adabi (Language, Literature
and culture) sabanin sauran Harsuna da dama, misali Harshen Turanci da ba’a iya
nazarin al’adun turawa da sauransu, wannan ya tabbatar da cewar Lallai Harshen
Hausa yana bunkasa sosai kuma ya tserewa sa’a.
Lallai kamar yadda
muka fada cewar Harshen Hausa yana bunkasa, a gefe guda kuma Hausawa na
ci-baya! Domin duk wanda ya kalli ko ya nazarci yanayin Hausawa yanzu zai ga
cewa suna komawa baya ta fuskar wannan Harshe. Misali wadan da ake kallo sune
‘yan Boko basu Baiwa Harshen Hausa wani muhimmanci ba, hasalima kalilanne daga
cikin ‘yan Boko wadan da zaka taras suna karanta rubuce-rubucen Hausa, ko yin
rubuce-rubuce da Hausa, wannan ya ke kara maida Hausawa baya domin sun nuna
fifiko akan wani Harshe sama da nasu wanda ya dara wanda suke kodawa.
Shakka babu
wannan maganar haka ta ke ya dan uwa mai karatu, domin idan ka shiga Jami’o’inmu
sai ka tarar cewar kusan daliban Hausa ne kawai ke mu’amala da takardun Hausa,
daliban da suke karanta sauran fannonin kimiyya da tattalin arziki da fasaha
duka da wahala kaga suna karanta wani abu na Hausa a jami’a sun gwammace su
karanta takardun turanci ko da kuwa rabin abinda suka karanta zasu fahimta.
Kuma bayanai suna
kara nuna cewar hattana daliban da suke karanta Harshen Hausa a jamio’I su
kansu da yawa ba suna karanta Hausar bane domin it ace zabinsu na hakika. Wasu
da dama suna karanta Hausa ne domin kodai basu ci kyakykyawan sakamakon
jarabawar NECO da WEAC ba da zai iya basu damar karanta wani fannin na daban ko
kuma abin nan ne da ake neman takardar shaidar kammala DIGIRI dan kare yawa,
cewar nima nayi digiri ba wai dan hakika tun farko sun zabi su karanta Hausa ba
domin bunkasar Harshen.
Wani abu da yake
kara nuna cewar Hausawa na mayar da kansu baya ta fannin Harshen Hausa shi ne
cewar, ko a jami’o’I da kwalejoji zaka samu Malaman Hausa suna yin amfani da
Harshen Ingilishi wajen karantar da Hausa, sai kayi mamaki malamin da yake
karantar da Hausa yana ta yiwa dalibai turanci, wasu malaman sukanyi haka ne
suma domin kare yawa dan kada dalibai su dauki cewar malamin da yake karantar
da Hausa bai iya turanci sosai ba, su kuma dan su kare kansu daga wannan
kaskanci na dalibai sai kaji malamin Hausa ya zage yana ta turanci da dalibansa
a cikin aji ko a wajensa, ko kuma suma Malaman neman burga ce da rashin kishin
ainihin Harshen Hausar.
Haka kuma, ga duk
mai bibiyar irin muhawarorin da ake tafkawa a shafukan sada zumunta na facebook
da Twitter da Googl Plus da sauransu zai ga cewa galibi ‘yan Boko basa karanta Hausa
ko yin rubutu da Hausa, mafiya yawan wadan da suke yin rubutu da hausa kodai
basu iya turanci ba wannan ta basu damar yin rubutu da Hausa, ko kuma sun iya
turanci amma basu kware ba, domin suma su kare yawar kada a yi musu dariya sai
suyi rubutunsu cikin Harshen Hausa, ko kuma ka samu wadan da suke rubutu da Hausar
irin wadan da suka koyi karatu da rubutu ne a sama.
Wata matsala kuma
it ace ta yadda Harshen Hausa yake gurbacewa. Shakka babu Harshen Hausa yana
gurbacewa sosai ta yadda zakaji Hausawa suna Magana da Hausa amma kuma a
zahirin gaskiya turanci suke yi, domin kalmomin turanci suke fassarawa kai
tsaye suke Magana da su, misali Bahaushe zai gaida kai sai ya ce maka ‘ya kake’
kaga a Hausa babu gaisuwa ya kake, kai turanci ne ko wani yaren aka fassara shi
kai tsaye, da sauran irin yadda ake yiwa Harshen Hausa dandantsa irin haka.
Dole ne duk mai
kishin Harshen Hausa ya ji kwarain gwiwa a duk lokacin da yaga mutane sun dauki
wannan Harshe na Hausa da muhimmanci. Akwai mutanen da ko wasika ka rubuta musu
da Hausa bazasu karanta ba, kuma Hausawa ne, amma duk irin maganar da ka rubuta
mara ma’ana da rashin tsari indai da turanci ne sai kaga ana bata lokaci ana
karantawa, Haka suma wadan da suke aiki da kafafen watsa labarai na Hausa da
muryoyinsu suka cika gidajen Radiyoyi suma sunfi gwammacewa su yi maka rubutu
ko karatu da turanci akan abinda ya shafe su.
Sannan yana daga
cikin ci-bayan Hausawa kuma ci-gaban Harshen Hausa shi ne irin yadda ahankali
wadan da ba Hausawa ba ke mamaye Radiyon Murayar Amerika. Ga duk wanda yake
bibiyar Muryar Amerika yasan da cewar da Sunday Dare ne kadai wanda ba Bahaushe
ba yake a wannan gidan radiyo harma ya zama shugaban sashen Hausa na VOA wanda
abin kunya ne a ce wanda ba Bahaushe bane yake shugabantar irin wannan gidan
radiyo na sashin Hausa, yanzu haka akwai akalla mutum biyu a wannan kafa ta
Murayar Amerika wadan da suke karanta labarai da Hausa kuma ba Hausawa bane, ko
shakka babu wannan ci-gaba ne ga Harshen Hausa kuma ci-baya ga Hausawa, domin
zakaji suna fassara turanci da Hausa gurbatacciya irin yadda suka ga dama, tun
Hausawa suna jin banbarakwai har ya zama jikinsu.
Sanin
kowa ne, Babban abin da fassara ke bukata shi ne lakanta sosai ta harsunan guda
biyu wanda za ka yi fassara daga gare shi da wanda za ka fassara zuwa gare
shi. sannan Yana kuma da kyau ka san wani abu na al’adun wadanda ke
magana da wannan harshe, domin wani lokaci sanin ma’anar kalmomin kawai ba zai
ba ka cikakkar fahimtar da kake bukata ba don yin fassara. A
fassara kuma, ma’ana ce ya kamata a fi baiwa muhimmanci ba kalmomin da aka yi
magana da su ba. Misali, Ingilishi da Hausa sun sha bamban da juna. Don haka,
ba kome ba ne mutum zai iya fassarawa kai tsaye. Mu dauki bankwanan bature a
lokacin tafiya barci, “Good night”; in aka fassara kai tsaye cewa za ka yi,
“Dare mai kyau” abin da zai iya sanya Bahaushe yin dariya idan ya ji. Amma in
ka fassara da “Sai da safe” ko kuma “Mu kwana lafiya”, to a sannan ne Bahaushe
zai fahimce ka. Kuma bature yakan amsa “Good night” ne, ko kuma “Night” kawai,
abin da zai kasance shirme a Hausa in ka fassara shi da “Dare” kawai. Shi ma
bature zai ji abu banbarakwai idan ka fassara masa “Ina kwana?” kai tsaye.
A ‘yan kwanakin
da suka gabata angudanar da gasar OLYMPIC a birnin landan kuma ‘yan najeruya
sun shiga wannan gasa. Wani abu da ya bani mamaki shi ne daga cikin wadan da
aka dauka domin nishadantar da ‘yan Najeriya da wakokinsu harda wani mai suna
EMMANUEL wanda yana daga cikin masu waka da Hausa, anyi hira da shi a filin
taba-kidi-taba-karatu na BBC Hausa, kuma ya yi waka da hausa, abin gwanin ban
dariya kuma abin haushi domin na farko Hausar yanayinta tsararo wato a gaggatse,
amma kuma bunkasa Hausar yake yi. Zaka samu yanzu Bahaushe dan Boko yafi jin
kunyar ya yi kuskuren turanci akan ya yi kuskuren hausa, idan mutum ya yi
kuskuren turanci aka yi masa gyara sai kaga duk ya damu, amma idan Hausa ce sai
kaga ya zama abin raha da dariya.
Kamar yadda sauran Harsuna suke da ka’idar rubuta su haka ita ma Hausa
ta ke da irin wadan nan ka’idoji wanda yanzu da yawan Hausawa babu ruwansu da
kiyaye wadannan ka’idoji, misali, ka’idojin rubutun Hausa suna taimakawa matuka wajen
saukaka karatu, da kuma saukakawa me rubutawa ko kuma me neman kwarewa, dan
gane abin da kai kanka kake cewa, da kuma fahimta daga shi wanda kake rubutawa
ko kuma karantawa idan misali Radiyo ne. Babbabn abu shi ne sanin yadda ake
harhada bakake a tada kalma.
Hakan ya hada da sanin cewa idan ka hade kalmar da ya
kamata ka raba za ta bayar da wata ma’ana daban da wadda kake so. Misali, idan
ka rubuta “koyaushe” a matsayin kalma guda, ma’anarta na nufin kowane lokaci,
amma in ka rubuta “ko yaushe...”, ka soma da yin tambaya ke nan, wanda
watakila, ke bukatar kammalawa ko amsawa. Misali, “Ko yaushe Musa zai zo?” kaga
wannan tambaya ce, amma Idan aka yi kuskuren rubuta wadda ba ita ba ce, to za a
faro karatun ba daidai ba, sai daga baya a gane ashe ba haka ya kamata a dauko
karatun ba.
Haka batun dangantaka ko mallaka. Idan ka ce “rigarta”
kana nufin wadda ta mallaki rigar kenan, amma idan ka ce “rigar ta...” to mai
karatu ko kuma mai sauraronka idan Radiyo ne zai jira ya ji abin da rigar ta
yi. Salon karanta su ma daban yake. Da yake ba kowa ne ya san ka’idar rubutun
Hausa ba sosai, shi ya sanya rubutun wani da Hausa, wanda aka yi ba kan ka’ida
ba, yakan yi ma wani wuyar karantawa.
Lallai ne mu
Hausawa mu sani duk wanda ya sha inuwar gemu bai kai ya makogaro ba. Domin duk
wani wanda ba Bahaushe ba ya kaiga son ya bunkasa Hausa bai kai Bahaushe ba,
domin akwai al’adu wandan da duk yadda mutum ya kai ga nakaltar Harshe ba zai
iya saninsu ba idan dai ba harshensa bane, kuma dole Hausawa su nuna martaba da
kimar Harshen Hausa wannan shi ne zai jawowa Hausawa martaba da kima a idan
duniya. Tabbas karatun turanci abu ne da Duniyar Hausawa ta ke bukatarsa sosai
da gaske, amma kuma wannan ba zai zama dalilin da zai zubar da ajin Harshen Hausa
ba. Bahaushe yana cewa kowa ya bargida .
. .!
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
Masha Allah. hakikanin gaskiya, nai matukar karuwa da wannan mukala taka. kuma insha Allahu za muyi kokarin yin gyara game da yanda muke mu'amalar mu da harshen hausa da hausancin. Allah Ya taimake mu baki daya.
ReplyDeleteBissalam
Naka Ahmad Aminu